Sashe 103
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin cuta?"
Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace "Amal ina zaki? Kina jin maganar da gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?"
Amal tace "tunda ki kaji ta faÉ—a a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan Allah ya kyauta"
Amal ta tafi É—akinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da zubar jinin sun isheta haka.
Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta yace "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari"
A Shagwaɓe Nurat tace "Brother ruwa zan sha"
Yace "ok bari in baki"
Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?"
Khalil yace "kwantar da hankalinki tana nan lafiya"
"A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?"
Khalil ya kalleta yace "kamar yaya ya kulle ki? Ya kulleki a ina?"
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun Nurat, cikin kuka tace "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah"
Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta farka zata zo ki ganta"
"to wai meyasa meta ne?"
"Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta temaka miki kiyi wanka"
Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan gaba ɗaya haushinsa suke ji.
Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene?"
Alhaji Musa yace "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin ba?"
Khalil ya kalle shi yace "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka"
Da sauri Alhaji Musa yace "tana ina? Nurat ɗin ta farkane?"
Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka kana ƙoƙarin tashi ina zaka?"
Yace "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?"
Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka garin yaya ka kulleta"
"wai Khalil yaushe ka koma haka? Yaushe ka koma mara kunyane?"
"ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba ƙaramin haushinka nakeji ba"
Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin, bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai"
"Da nayi maka me?"
"in mun haÉ—u a kotu kaji"
Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake nufine?
Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana tambayarta  "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?"
Ramlah tace "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda ubansa"
Hajiya Halima ta É—ora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah gaba É—aya kika biyewa namiji kika barbaÉ—ar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa kanki kenan?"
Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please "
Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa, ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali.
Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya É—ago kai yace "ke wai ina Mummy ne?"
Iman tace "tana sama É—akin Daddy"
Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu.
Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa ya kama shi.
Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan kenan? Yaushe rabonka da shigowa"
Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace "Mummy ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau, dama na shigo mu gaisa ne zan karya"
Tace "shi Daddyn naka bazaka gaishe shi ba?"
"Ai na gama gaidashi, ni da sake gaisheshi har abada"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?"
Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office "
Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? "
Yace " bakomai "
" Bakomai amma ka faÉ—a masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?"
Ya girgiza kai alamar a'a
"to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku Wulaƙanta mahaifinku?"
"Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faÉ—i wannan maganar ba, kawai dai Allah ya kyauta"
Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace "Mummy"
"Na'am"
"wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?"
"haba dai? Gidan nan tazo? Ai ban sani ba"
Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy"
"subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah"
. "Mummy ya akayi kika sani?"
"last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai ba, sema baƙar magana da tayi min"
Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye"
Hajiya Sarah tace "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka"
"Mummy kiyi haƙuri, wataran se labari ze dena insha Allah"
"Mhmm Iman kenan, yaushene watarn É—in? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah ya kyauta dai kawai".
Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama