Sashe 69
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Bukar yace "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan"
Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting É—in nan da kace"
Alhaji Bukar yace "to shikenan, se kazo"
Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?.
Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran wake zasuyi alala.
Hari tace "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya muyi ta juyi a gidan nan"
Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa.
Hindu tace "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya.
Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace "aifa dama ina zaki ƙoshi tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze rufa masa Asiri ".
Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga sabgar iyalan gidan ba.
Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne.
Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira shi namiji da take miki gori a kansa "?
Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba"
"wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki kiyayeni akan ɓata mata rai"
Hanne tace "idan anƙi fa?"
Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace "A'a Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai"
Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace "ba alfahari ba amma Wallahi da kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata aura, Jahila kawai"
Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi, amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci.
Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo, Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?"
Amal tace "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun kasa ganewa"
Mummy tace "madalla, shine nake ta magana kika ƙi buɗewa"
"Am sorry, bazan sake ba insha Allah"
"Hmm ai shikenan, ya hannun naki yanzu?"
Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun hanani wai ba network"
Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode"
Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji Haruna.
Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace "Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba"
Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace "nima naji saƙonki, ance bayan mota zakizo karɓar gids ma"
Tace "eh hakane, ko idan na dawo bazan samu ba"
. Yace "idan kika dawo ina?"
"zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama ya gama tunda fari"
Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina, tabbas naji daÉ—in kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi"
Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara, ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar.
Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake"
Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina É—an tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze bani ita idan mun koma gida"
Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya É—au 'ya ya bamu alhalin bamu da wata dangantaka a tsakaninmu"
Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa"
Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata ayi"
Tace "shikenan, Allah ya kawo shi"
Yace "Ameen"
A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki, suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini, sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa.
Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace "gaskiya ki ƙyalemin gashina mana, haba se izaya kikemin a kaina"
Ta ɗan tura baki tace "kitso fa zan koya"
"To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin taki ta ina za'a kitsa sumata?"
"Ni dai ka ƙyaleni"
Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi"
Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai"
Yai murmushi yace "kuma fa hakane, to na fasa askewar"
"A'a gara dai ka aske É—in"
Hindu Tayi sallama kawo musu Abincin Safe, akayi mata izinin shiga tana shiga ta tarar da Yusuf kwance akan cinyar Widad.
Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace "sarkin kunya, idan na aura miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?"
Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace "Yuzarsef, wallahi da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's very kind and innocent"
Yusuf yace "hakane tana da kirki kam, ga nutsuwa"
Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace "ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma"
"ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma"
Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace"
"A' a ban yadda ba, gaba É—aya nawane, bayan kace baka son Baby"
Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin iyayi da tsari"
"wai dan Allah dagaske bani da ciki?"
Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai madam"
Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi"
"Seki zauna kiyi ta imagination ai, miƙomin abincin nan inci"
Ta ɗakko kwananon Abinci ta miƙo masa, suka ci tare suna hira.
Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaÉ—on gurji da zogale zan mana, zaki ci?"
Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daÉ—i Sosai"
Yusuf murmushi yace "to kwaÉ—ayayyiya"
"Eh anji É—in"