← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 127

Sashe 44

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maimakon ya É—aga ta seya sake gyara kwanciya a jikinta, yana kuma nanata mata "ina sonki Matata, ina sonki Widad"

Gaba É—aya taji wata kasala na saukar mata, batayi magana ba sedai tasa hannu ta rungumeshi itama.

Hanne cw ta bankaÉ—o É—akin sannan zata yi sallama.....

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

84_85

Yusuf ya ɗago da sauri, yayin da jikin Hanne ya ɗau rawa, ba tare da tace uffan ba ta ajiye kwanukan da ta wanke, jikinta na rawa ta fice waje, yayin da wani abu kamar dutse yazo ya daskare mata a ƙirjinta, tana tafe amma kamar ta kifa, danko gabanta bata gani, maimakon taji haushin Yusuf, se wani tuƙuƙin tsanar Widad da taji a ranta, kamar ta janyo ta ta shaƙe haka take ji.

Widad kuwa tsaki tayi, ta haɗe rai tace  "kaga malam ɗagani mana"

Yusuf yace "to nikuma meye laifina da zaki wani haÉ—emin rai haka?"

Ta ƙara haɗe rai tace "kaika sani dan Allah nika ɗagani, ina da abunyi fa"

Yai ƙasa da murya yace  "My queen..

Ta katse shi ta hanyar cewa" dan Allah malam ka ɗagani nace, bana son jin komai daga bakinka, kuma karka ƙara bawa wata 'yar ƙauye kwanukana ta wanke min na gaya maka, in bahaka ba nika ajiyemin abuna zan wanke, idan kuwa ta sake wanken kwanuka na, wallahi sena zuba su gaba ɗaya a wannan rijiyar ta gidan nan, kuma idan na kuma ganinta a ɗakina duk abunda nayi mata ita ta janyowa kanta na gaya maka "

Yusuf ya ƙura mata ido, yana kallon yadda take masifa fuskarta na bayyanar da matsanancin kishin dake zuciyarta, amma yanzu daze ce tana sonshi seta fara masa iyayi, tana ita bata san so ba, kawai dai danya temake ta ne.

Ta ture shi daga jikinta, ta miƙe tana kumbure kumbure ta cire kayanta ta tafi wanka.

Bayan fitarta ya miƙe, ya gyara mata shimfiɗarta, Gwaggo ta aiko musu da Abun karin kumallo.

Koda Widad ta fita tsakar gida, tana kallon mugun Kallon da Hanne ke mata, banda Widad na ganin darajar Gwaggo, da ba abunda ze hana tayiwa Hanne rashin mutunci me wuyar mantawa, amma ta ƙyaleta taje tayi wankanta.

Data dawo ɗakima Yusuf yana ta ƙoƙarin rarrashinta, amma ta basar dashi taƙi kula shi, ta barshi yaita ɓaɓatunsa shikaɗai, ta ɗakko kaya zata saka yazo ya karɓi kayan daga hannunta, amma tasa hannu fizge abunta, sosai kishi me zafi ya bayyana a fuskarta, Yusuf yace bari yayi amfani da wannan damar gurin jarraba Widad, bari yaga idan dagaske kishinsa take ko kuwa?.

Ya koma gefe ya zuba mata ido, tasa kayanta, ta koma gefe tana shafa mai tai kicin kicin da fuskarta, kamar ba itace suke tare É—azu ba cikin farin ciki.

Yusuf yace "Allah sarki rayuwa, Ohh koya Amal ɗina tayi da taji an sace mata ni, Amal ta gama matowa a sona, she really loves me, ga Nurat ma light, ga fara'a ga kirki she also loves me, itama ban san ya zataji ba, ga Sakina abokiyar aikina, abunda ya hana in bawa Sakina fuska shine shigar matsatsun kaya, da yawan kule kulen maza, se gashi Allah yasa na Auri me sa matsatsun kayan, ga tsiwa gashi sam bata sona, taita bani wahala, gashi ina matuƙar sonta, kissing ɗinta in nayi ta dingamin faɗa kenan tanamin tsiwa, laifi koni nayi ko bani nayi ba taita fushi dani, bata tausayina sam, nikaɗai nake sonta, Nasan da Nurat na Aura dana huta, zan sha soyayya dan akwaita da tausayi da sanyin hali, sannan masha Allah, gata da lips masu kyau, nasan ita ba zata dinga ƙyamata ba, ko kissing ɗinta na....

Aibe ƙarasa ba yaji saukar ludayin roba a ƙeyarsa, seda ya razana ya kalli inda Widad take, kawai ta fashe da kuka harda hawaye.

Yusuf yace "Ke lafiya Mena yi miki kuma? Kinƙi kulani nazo ina hirata kuma seki jefe ni, sekin jimin rauni tukuna, mu koma gida 'yan matan nawa duk su gujeni?ko kuma su kasa ganeni?"

Aikuwa ta ƙara sautin kukan nata sosai, harda sheshsehseƙa, wani guntun murmushi yayi a ransa yace' yarinya kin faller '

Amma a zahiri seya miƙe, yazo inda take yace  " Widad, meyasa ki kuka ne? Kowani abun nayi miki ne?"

Cikin shagwaɓa Tace" Nima ban sani ba"

Yusuf yace "to meyasa kika jefeni da ludayi? Baki san naji zafi ba?"

"Ni bana son zancen da kake ne, raina ɓaci yake ni karka ƙaramin zancen wata a gabana, bana so am feeling bad, ni gaba ɗaya ma zuciyata haushi nake ji"

Yusuf ji yayi kamar ya ƙyalƙyale da dariya, amma yasan yana yin hakan, sabuwar rigima zata saka masa, dan haka yace

"Ohhh shikenan ya isa haka, am very sorry bazan sake ba, dena kukan kinji abar sona, na dena insha Allah dena kukan haka kinji gimbiyar"

Ya dinga share mata hawayen da yake ta binta fuskarta.

Widad ta ture hannusa cikin zumɓira baki tace "ni rabu dani, tunda ka sani kuka"

"Yi haƙuri I don't mean to hurt you Baby, ban zaci ranki ze ɓaci ba, kinga se binki nake ina magana amma kika shareni, se da ki kaji nafara lissafin 'yan matama sannan kika hau kuka"

Widad tace "to waima meyasa nayi kuka ne?"

Yusuf yace "Oho nima ban sani ba, aike zan tambaya" Yusuf ya bata amsa ɗan taɓa baki tayi ta ɗanyi tsaki sannan tace

"wai dagaske Nurat ma budurwarka ce?"

Yusuf yace "A' a naje gidansu dai, bayan mahaifinta yayi yunƙurin sawa a sace ki, ita na ritsa da bindiga ta gayamin inda kike, bayan nan na koma gidansu, dan inyi mata wasu tambayoyi, da farko ta tsorata daga baya kuma ta saki jiki, muka dinga hira a haka na samu abunda nake son ji daga gare ta, har mukayi exchange na lamba, akwai ranar da muka fita dake, nakw waya nace ina tare da matata ne, ai da ita muke waya, sedai daga baya na fuskanci Nurat ta kamu da sona ne "

Widad tace "kuma kaima kana son ta"?

"To waike meye naki na tambaya ne? Bayan kince bakya sona, ina ruwanki ki ƙyaleni in samo mesona, wanda bazata gujeni ba kota dinga min tsiwa ba"

Ɗan guntun tsaki tayi, tare da jin haushin kanta ko meye na damuwa ma oho, ta janyo kwanon Abinci ta buɗe, kofin an zuba kunun tsamiya, kwanon kuma wainar gero ce an barbaɗeta da ƙuli ƙuli, Widad tace "wannan wane irin Abinci ne kuma, shima wani baƙi dashi??"

Yusuf yace "wainar gero ce"

Tace "Meye kuma wainar gero, mutanen nan suna son yin Abinci baƙi" tai maganar Tare da saka hannu ta fara yashe ƙulin kai tana lashewa, Yusuf ya kalle ta yace  "bismillahi, kwaɗayayyiya zaki cinye ƙuli ƙulin ki barmin gaya ko? Dama kin saba"

Hararsa tayi ta cigaba da lasar ƙuli ƙulinta, Yusuf yace "baze fa yuwu ba, se saka yawu kike a jiki, idan muka koma gida sena gayawa Daddy yadda kike bani wahala, duk na rame kekuma ƙibarki kawai kikeyi"

Duk da a fusace take amma murmushi ya suɓucemata tace 'kamar kasan akanka Daddy ze iya zaneni ma inaga, dan yana matuƙar sonka sosai"

Yusuf yace "nima ina sonshi sosai"

Widad ta kalle shi da sauri tace "dagaske? Kana son Daddyna?"

Yusuf yace "sosai makuwa, ai bazan manta alkhairinsa a gareni ba, kuma koba komai ko bama tare, yana da matsayi a gurina saboda na taɓa Auren 'yarsa, dan haka inajinsa kamar mahaifina mussman yadda yake girmamani"

Widad ta jinjina kai, har cikin ranta taji daÉ—in yadda Yusuf yace yana son mahaifinta harya ya beshi haka.

wainar geron nan ba ƙaramin daɗi tayiwa Widad ba, ta saki jiki taci sosai, sed suka gama faɗansu da Yusuf sannan ya fita.

Widad ta fito tsakar gida, amma bata ga Hindu ba, ta kalli Hansai tace "wai ina Hinduna ne yau ban ganta ba fa"?

"Hindunki a ina?" Hari ta faÉ—a tana yatsune fuska.

Banza Widad tayi mata, ta kafe Hansai da ido tana jiran amsar tambayarta, Hansai tace "Zazzaɓi take yi, tana ɗakin Gwaggo a kwance"

Widad tace "subhanallah garin yaya?"

Hansai tace "larura daga Allah mana"

Widad ta tafi ɗakin Gwaggo, ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama, Aka amsa ta nemi izinin shiga, sannan ta shiga.

Jamila na zaune a gefe tana shayar da jaririyarta, yayin da Hanne keta ƙoƙarin gyara ɗakin Gwaggo, Gwaggo kuma tana ta rarrashin Hindu taci Abinci amma taƙi.

Gaba É—aya damuwa ta bayyana a fuskar Widad.

Jamila ta kalli Widad tace "ina kwana?"

Widad ta kalli Jamila ta É—auke kai, tazo ta nemi guri ta zauna a gaban Gwaggo tace "Mama, meyasa ba'a gayamin Hindu ba lafiya ba?"

Gwaggo tace "ahh haba, ya za'ai a takura miki, amma yanzu ai gashi da kika fito kinji"

Jamila taji haushin sharetan da Widad tayi a karo na biyu, kuma tana ji tana mata magana.

Cike da tausayawa Widad tace "sannu Hindu, Allah ya baki lafiya"

Hindu tayi murmushi tana gyÉ—a kai, yayin da Hanne se cika take tana batsewa, tana faman jan tsaki kamar wadda akayiwa wani abu, dan data tuna a yadda ta gansu itada Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka.

Widad ta kai Hannu ta taɓa Hindu, jikinta zafi sosai Widad tace "Gwaggo, baza'a kaita Asibiti ba? A kaita a duba ta mana"

Gwaggo tace "hmm Amarya kenan, da kinsan azabar tazarar dake tsakaninmu da Asibiti da baki ce a kaita ba, bamu da Asibiti a garin nan, ƙauye uku zuwa huɗune tsakaninmu da Asibitin shaka tafi, yanzu kafin a kaita ma wani wahalar ne, duk seta galabaita"
Chapter 44 · 0% Book details