Sashe 23
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh mana, sunce zasu bani, amma baffanta yace kuÉ—in Auren million huÉ—u, na rasa yadda zanyi ne, ga Yayana wai ze ciyo bashi akai kuÉ—in auren"
"bashi kuma? Kawai ka bari idan ya karɓo bashin, kazo muje 'yan mata se wadda kake so, mezesa ka wahalar da kanka akan wannan balarabiyar, hasken fatane fa kawai da gashin'
Nasir yace " A'a gaskiya ni Huda nake sl, kuma bazan ma bari ya karɓo bashin nan ba gaskiya"
Bulama yace "kai meyasa baka da wayo, wallahi garin nan akwa tsula tsulan 'yan mata, duk abunda kake so zasuyi maka indai da uwar kuɗin ka"
Tsaki Nasir yayi, ya tashi ya bar gurin saboda kunna shi da Bulama yayi.
Be zame ko ina ba se gidan Alhaji Abubakar, ya samu Ahmad É—an gidan Alhaji Abubakar, suka zauna suka gaisa Ahmad yace "Angon Huda ya akayine? Naga baka walwala sam"
"Ahmad ina zanyi wata walwala? An yanka min sadaki fiye da tunani, gashi gaba ɗaya jarin da ribar da nake juyawa basu fi million ɗaya ba, ga Yaya Yusuf duk ya damu, har yana batun ze karɓi loan, gaba ɗaya na damu nina ma haƙura gaba ɗaya, amma yaƙi saurarata"
Ahmad yace "Nasir, ita kanta Huda tana buƙatar taimako, idan ka aureta zata samu sassauci, Allah baze hanaka yadda zakayi ba, Insha Allah, in dai matarka ce seka Aureta"
Nasir yace "Ni dai na haƙura na fidda rai, nasan ina matuƙar son Huda, amma bani da halin Aurenta"
"Ka dena faÉ—ar haka, Insha Allah za'a samo kuÉ—in nan, kuma zaka auri Huda"
Nasir yace "to idan rabona ce Allah yasa in samu"
Yusuf ya dinga faɗuwa yana tashi, ya fasa karɓar bashin banki saboda haramcin hakan, Amma ya saida abubuwansa ya tattara kuɗin hannunsa da ƙyar sukayi million ɗaya da rabi, Ahmad ya bawa Nasir gudunmuwar dubu ɗari biyu, shima ya tattara ɗan abunda yake dashi, amma kuɗi ko million biyu basu yi ba, saura kwana uku kwanakin su cika, Alhaji Abubakar yazo ya samu Yayan Nasir yace "Malam Yusuf ya ake ciki ne? Kun haɗa kuɗin kuwa?"
Yusuf yace "wallahi kuɗin nan basu kai ba, muna ta faɗi tashine, dan Allah inda hali a basu haƙuri su ɗan ƙaramana lokaci, dan Allah karsu bawa wani, Insha Allah zamu cika a samu Nasir ya aureta"
Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar yayi yace "nikam wani irin so kakewa Nasir haka?"
Yusuf yayi murmushi yace "Nasir ne kaɗai ya ragemin, kuma kaga yarone ƙarami ba wani babba bane, kuma maraya ne, yana buƙatar a jashi a jiki, kuma iyayenmu sun mana wasiyya sosai akan muso juna, inyi haƙuri dashi in kula dashi, kaga dole in kula da marayana"
Alhaji Abubakar yace "Masha Allah, gaskiya na daɗe banga managarcin mutum kamarka ba Yusuf, Allah ya biyaka, kawo abunda ya samun, inje musu dashi inga ya zamuyi"
Yusuf ya dinga murna, kamar Alhaji Abubakar yace an bawa ƙaninsa Hudan, yaje ya kawo masa kuɗin, ya duba ya ƙirga su sannan yace "zanje can marocon, zanga yadda zamuyi, amma da ina da 'ya ko ƙanwa gaskiya dana baka, dan na yaba da amanarka da haƙuri da ɗan uwanka'
Yusuf yayi murmushi yace " rufamin Asiri kar Uwargida ta jimu, kasa ta haÉ—emin rai yau"
Sukayi dariya gaba É—aya, daga nan suka yi sallama.
Sam Nasir be san me ake ciki ba, Yusuf yana ta cigaba da fafutuka, yana haÉ—awa da Addu'a.
Tafiyar Alhaji Abubakar da kwana biyar, ya dawo yai sallama da Yusuf ya sanar masa da an basu Huda.
Yusuf ya gigice yace "ai bamu cika kuɗin ba"
"karka damu, na shawa kan wannan matsalar, nan da sati biyu za'a kawo masa ita"
Yusuf yai godiya kamar ze duƙawa Alhaji Abubakar, har seda yasa Alhaji Abubakar yaji kunya.
Shikam Nasir ya dawo daga kasuwa, yayi sallar isha'i yaje yayi kwanciyarsa, ko abinci be nema ba, babu abunda yake banda begen Huda.
Yusuf ne ya shigo ɗakin da Nasir yake yace "Ango kasha ƙamshi"
Nasir be gane me yayansa yake nufi ba, yayi zaton zolayarsa kawai yake.
Yusuf yace "gobe in Allah ya kaimu, masu aiki zasuzo suyi gyare gyare a gidan nan, ka tattare kayanka ka koma shagon gidana"
Cike da rashin fahimta Nasir yace "gyaran me kuma za'ayi?"
"Amarya za'a gyarawa gida"
"Aure zaka ƙara ne?"
Yusuf yace "Rufamin Asiri, inani ina ƙara Aure, Nadiyata ta isheni matar rufin Asiri, 'yar aljanna insha Allah, har ƙiyama muna tare da ita"
Nasir yace "to gyaran me za' ayi?"
"Huda za'a gyarawa gida"
Zare ido Nasir yayi yace "wace Hudan?"
"Hudanka mana"
'Yayana, yaushe ta zama tawa? "
" Sun baka, nan da sati biyu insha Allah za' a É—aura Aure"
Ai ba shiri Nasir ya rungume Yusuf ya fashe da kuka yace "Yayana, wallahi na rasa me zance ma gaba ɗaya, yadda kake ƙoƙarin farantamin rai, Allah ya sadaka da Annabin rahama, yasaka a aljanna ma ɗaukakiya"
Yusuf yace 'Ameen ya Allah, tare da kai ƙanina, farincikin ka shine nawa, nima nasan idan nine a halin da kake ciki, ba zaka zuba ido ba, ina me maka nasiha daka kula musu da' ya, ko bayan ba raina ka tuna gwagwarmayar da muka sha kafin ka sameta, ka nunawa duniya mazan hausawa Jarumai ne, kuma sun iya riƙe mace su bata kulawa "
Nasir yace " karka damu Yayana, Insha Allah zanyi iya ƙoƙarina inga na riƙe Huda da Amana"
Haka Yusuf ya ci gaba da yi masa nasiha, da jan kunne akan sha'anin Aure.
Nan da nan magana ta cika unguwa Nasir ze auri Huda, wani abun takaici dangin mahaifinsu sukace bada yawunsu ba, ba zasu yi jagora aje a Aurowa Nasir balarabiya ba, babu hannunsu a ciki, abun nan ya ƙara tsayawa Nasir a rai, ƙiri ƙiri se bare ne yayi jagorancin karɓa masa Auren wato Alhaji Abubakar.
Haka suka tafi maroco, da Alhaji Abubakar, da É—ansa Ahmad, da Yusuf da Nasir da wasu Abokan Alhaji Abubakar suka tafi maroco, Nasir yaso a tafi da Bulama, amma Yusuf ya hana yace ba zasu je da shi ba.
Huda ji take kamar ba itaba, lokacin da aka faɗa mata kuɗin da aka yankewa Nasir ta fidda rai da Aurensa, saboda tasan bashi da wannan kuɗin, ta fidda rai gaba ɗaya ta haƙura, se rashin lafiya take tana rama, babu zato babu tsammani yayarta Islam tazo mata da zancen ai megidanta ya zo da kuɗin Auren Nasir daga Nigeria, Alhaji Abubakar ne ya cika kuɗin, amma babu wanda ya gayawa hakan.
Baffansu Huda be taɓa tsammanin za'a iya biyan kuɗin nan ba, duba da yadda aka gaya masa Nasir marayane, kuma bashi da ƙarfi, ganin haka yasa yace tunda ta dage se bahaushe, bahaushen ma talaka ta dage ita da 'yar uwarta to suje, gasu nan ga bahaushe, kuma ya cire hannunsa daga kansu, kome ze faru ta nemi' yar uwatta da mijinta da suka dage akan se anyi wannan Auren, karsu ƙara nemansa.
Huda ta wani fannin tayi farinciki, yayinda gefe ɗaya kuma hankalinta a tashe, jin cewar jigon da suke tunƙaho da shi yace bashi basu.
Alhaji Abubakar kuma yace yaji ya gani, shi har Abada Aure albarkarsa ake nema ba wai tarin dukiya ba, idan da rabo a gaba Nasir zeyi Arziki, kuma in dai Huda ce kome ze faru ze riƙeta, balle babu abunda ze faru se alkhairi.
Shikuma Habib yace se an biya shi duk abunda ya kashewa Huda, alhalin duk abunda Ake bayarwar ba bata akeyi ba, wanima bata san an bayar É—inba.
Da kuÉ—in Auren gurin Nasir, aka tattara abunda ya samu aka biya Habib.
Kamar wasa ranar wata juma'a, bayan sallar juma'a, a masallacin Kairaouine, suka ɗanyi shagalinsu a can, da suka tashi dawowa Nigeria, Alhaji Abubakar ya kasa ya tsare ya karɓi sadakin Huda a hannun ƙanin mahaifinta, sauran 'yan uwa ma suka tattara mata sha tara ta arziki, wani aka bata wani kuma aka ƙwace, suka taho da Amarya Nigeria.
'yan unguwar su Nasir, suka haÉ—a kuÉ—i suka shirya musu walima, wani ya bada hall, wani ya bada buhun shinkafa, gaba É—aya kai baka ce Auren maraya ne ba, abokansu suka dinga basu gudunmuwar kuÉ—i wasu kaya, saboda duk wanda yasan Nasir da Yusuf yasan iyayensu, yasan mutane ne masu karamci da biyayya.
A lokacin maƙoci yana ganin ya isa da ɗan maƙocinsa, ana zaune lafiya kamar 'yan uwa dan haka Nasir yayi mamakin yadda bare sukayi musu wannan karar amma dangin mahaifinsu suja kasa yi musu.
Duk Wanda yaji yadda akayi auren yasan kawai rabone, dama Allah ya rubuta Huda rabon Nasir ce.
Huda ta tare a gidanta, musamman Yusuf yasa Nasir a gaba sukaje gaban Alhaji Abubakar sukayi masa godiya dashi da Islma amaryarsa.
Nasir baze taɓa manta alherin Ahmad da mahaifinsa ba, da sauran abokansa, amma Bulama babu abunda yayi masa, sema wadaƙa da sata daya dingayiwa Nasir a shago, ganin hankalinsa ya koma kan Auren da zeyi.
Sam Bulama beso Nasir ya auri zuƙeƙiyar balarabiyar yarinya ba, kullum suna tare, amma gaba ɗaya Nasir ya fishi sa'a a rayuwa.
Kuɗaɗen da Nasir ya samu na gudunmuwa, da wanda aka bawa Yusuf ya ɗau abunda ze ɗauka ya bawa Nasir sauran, ya sake zuba dukiyar a harkar kasuwancinsa, duk inda yaji wata harkar samu seya ɗebi kuɗi ya tafi ya jarabba, duk lokacin da yayiwa Yusuf zancen be bashi kuɗin daya ara masa, se yace ya ajiye masa ba yanzu ba, dan gani yake idan ya karɓa hakan ze iya shafar kasuwancin ƙanin nasa, yana nan zaune da matarsa lafiya, yana sonta tana son shi, Arziki se bunƙasa yake a hankali.
Ya É—aukewa Yusuf É—awainiyar siyan kayan Abincin gidansa, ya nuna masa baya so amma be bari ba.
Huda ta ɗau kuɗinta na sadaki da abubuwan data samo a can ƙasarsu, ta bawa Nasir tace ya haɗa, da tayi ta ajiyar kuɗin babu abunda zata yi dasu gara ya dinga juya su, ya karɓa ya haɗa yana juyawa, a hankali ya dinga janyo abokansa cikin harkar kasuwancin da yake yi, wasu suzo zuciyarsu ɗaya wasu kuma suzo da niyyar mugunta.