Sashe 11
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Widad ta kalli Hari tace "kekam abunda kika yi baki kyauta ba Hari, ke kanki aka bibiya sadakarki aka bawa megari ba dan kina da wani abu da namiji ze kalla ya aureki ba, dan ba kyau kika fi Hindu ba, yakamata ki dinga jan girmanki kema kin haifi mata"
Shiru Hari tayi da yake tasan bata da gaskiya.
Gaba ɗaya ƙarashen wunin nan haka Hindu tayi shi ba walwala, hakan ya shafi Walwalar Widad itama, seta kasa sakewa sukayi jugum jugum.
Nurat suka gama hirarsu da Anwar, tai masa rakiya har mota ya tafi, sannan ta dawo, tana shiga falo ta tarar da mahaifinta a tsaye yana huci, ya kalleta yace "dan ubanki meya haɗaki da wannan yaron?"
Cikin rashin fahimta Nurat tace "Daddy Anwar nefa"
"ina ruwana koma uban waye? Ke yanzu shikenan ban isa in gayamiki kiji ba? Meye haÉ—inki dashi nace?"
Mahaifiyar Nurat ce ta fito da sauri tace "dan Allah ka saurarawa yarinyar nan, wucewa yazo yi ya tsaya suka gaisa meye abun ɗaga hankali kuma? '
" ke dama ke kike goya mata baya take karyamin doka, ni anya ma kuwa wannan' yata ce"
Cikin mamaki tace "Meka ke nufi da anya kuwa 'yarka ce? Zargina kake kome? Kokuma dan kana abu zata kake kowama haka yake?"
A fusace yace "ni kike gayawa haka?"
"na gaya maka É—in, ashe ba daÉ—i nida ka gayamin"
"A gaban' yata kike cewa ina biye biye?"
"to kace ƙaryane mana? Ni zaka kalla kace anya 'yarka ce?"
Aikuwa cike da zuciya yayi kan mahaifiyar Nurat, sedai cikin gaggawa Nurat ta shiga tsakani tana kuka, aikuwa yasa hannu ya shaƙota yayi wurgi gefe ɗaya, bisa tsautsayi tai gware da center table, take ta zube a gurin jini ya shiga zuba a goshinta kamar an buɗe famfo, take suka yi kanta da gudu, sedai ko motsi ba tayi.
Mahaifiyarta ce ta ɗagota a gigice tana kiran sunanta, Alhaji Musa yasa hannu yana ƙoƙarin karɓar Nurat a hannunta amma ta riƙeta gama taƙi sakarmasa ita, cikin kuka tace "ka ƙyalemin 'yata, ai dama kace ba' yarka bace, tunda ka kashemin ita se hankalinka ya kwanta"
Be saurareta ba ya suri Nurat da sauri yayi waje da ita jini yana zuba a goshinta.
Amal kuwa bayan ta shiga gida, Hajiya Halima tace "ina Anwar É—in?"
"Ya ajiueni ya tafi, wai zashi wani guri ne"
"Nifa bana son yawan yawon nan da yake tafiya, se wani abun ya sameshi tukuna ko? Ze dawo ya sameni ne, ina jinki meyafaru da kukaje gurin Bulama"
Amal tace "ba wani abu bane, dama kawai tambayarsa yayi ya akayi yayi free? Se kuma jaje da yayi masa"
Hajiya Halima tayi tsaki tace "Aikin banza, dana san hakane wallahi ba zashi ba, mutumin banza kawai"
"Mummy kenan É—an uwankine dai"
"dalla rabu dani, É—an uwana mara amfani ba"
Amal tai murmushi tace "in an jima zamuga kun jone ai, ba'a shiga faÉ—anku"
Widad bata wani iya rarrashi ba, dan haka ta kasa saka Hindu farinciki, haka kurum idan ta tuna Gorin da'akayiwa Hindu se taji ta ƙara tsanar Hanne, sam Hanne bata ɗakko halin Gwaggo ba, Gwaggo mace ce me kirki da kawaici, ba zaka taɓa cewa ba ita ta haifi Hindu ba, saboda yadda take nunawa kamar tafi son Hindu ma aka Hanne kai kace gaba ɗaya ita ta haife su, bautar da Hindu take wa Gwaggo Hanne ba tayi, ga shegen som jikin tsiya, shiyasa basa shiri da Gwaggo.
Gwaggo se jan Hindu take da hira, amma taƙi sakin jiki, saboda gaba ɗaya ranta a ɓace yake, haka suka haƙura suka ƙyaleta, sedai hakan ba ƙaramin damun Widad yayi ba.
Yau shiru shiru Yusuf be dawo ba, gashi tun la'asar hadari yake haɗuwa a garin, se cida ake me ƙarfin gaske, kowa ya shige ɗaki ga iska da'ake yi, gaba ɗaya hankalin Widad yaƙi kwanciya, Yusuf be dawo ba ga hadari se cida yake, ga wani irin tsoro da ya baibayeta, lungun kan katifa ta koma tayi shiru tana ta addu'a a ranta.
Har magariba Yusuf be dawo ba, daga bakin ƙofar ɗakinsu tayi alwala, ta rufe ƙofar ta dawo tayi salla, se wata irin walƙiya ake.
Ana idar da la'asar aka kece da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, babu Yusuf babu labarinsa, hakan ba ƙaramin ɗagawa Widad hankali yayi ba, be taɓa yin haka ba se yau.
Tun Widad na tsumayin dawowar Yusuf harta fara cire rai, ga tsoro da ya bai baye ta, take ta fashe da kuka, ta dinga kuka kamar wata ƙaramar yarinya, ga tsoro ga gefe guda tana tunanin ko wani abu ya samu Yusuf ne.
Har wajen ƙarfe goma da rabi na dare, gashi babu alamar za'a tsagaita da ruwan nan, ta dunƙule guri ɗaya tana kuka, ji take tamkar ɗakin nan ze ruso a kanta, dan in akayi cida ji take tamkar ɗakin yana vibrating.
Babu zato ba tsammani taga An turo ƙofar ɗakin, Yusuf ne ya shigo ya jiƙe sharkaf da ruwa se ɗiga yake, jikinsa yana rawar sanyi.
Tana ganinsa maimakon ta tausayawa a halin daya dawo, kawai ta fashe da kuka ta haushi da faÉ—a
"Ina kaje ka tsaya, kalli agogo ƙarfe nawa? Kawai ka kama ka ɗagamin hankali ga tsoro inaji, ka fita kaje kayi zamanka baka damu da halin da zan shiga ba, wannan wane irin abu ne haka?"
Aikuwa Yusuf ya ƙule, akanta yaje yasha wannan uwar baƙar wahalar, ga ruwan sama yayi masa duka, bata tausaya masa ba se masifa da ta haushi da ita daga shigowarsa, aikuwa ya ajiye kayan hannunsa, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda ya jefo mata, ya juya ya shiga kokawar canza kayan jikinsa.
Ledar ta ɗauka, taji an nannaɗe leda cikin leda, ga ɗumi a jikin Ledar, se ƙarnin kifi da yake tashi a jiki.
Yadda ya haɗe rai ne yai mata banza yasa ta gane haushi yaji, ya canza kayan jikinsa ya ɗau abun shimfiɗarsa ya shimfiɗa a bakin ƙofa inda yake kwanciya, ga babu abun rufa ga iska da feshin ruwa a gurin.
Gaba ɗaya taji tausayinsa ya kamata, ta ƙarasa kan bargon da yake kwana ta zauna tace
"ka taso mu kwanta akan shimfiɗata, kaga nan ruwa yana jiƙaka"
Banza yayi mata, yaƙi ko motsawa daga inda yake, balle tasa ran ze kulata.
"Yoseef magana fa nake maka" still dai bece komai ba yayi mata banza.
Ta Kai hannunta ta shiga É—an girgiza shi tana faÉ—in "dan Allah ka tashi, muje mu kwanta nan akwai sanyi"
A ɗan kausashe yace "malama ki ƙyaleni, tunda bakya tausayina komai nayi abun faɗa ne a gurinki, bana taɓa yi miki abu ki yaba, sedai ki ɓata mini rai, maimakon ki tambayi ya akayi na daɗe haka meya sameni kawai kin hauni da masifa, ni matsa ki ban guri ki dena taɓani"
Se kuma taga tabbas abunda tayi bata kyauta ba.
"Am sorry, ka tashi daga nan karka yi zazzabi"
"ina ruwanki idan nayi, ai ba damuwa kika yi dani ba, ki rabu dani kawai"
Taga dai alamar Yusuf bashi da niyyar tashi, dan haka kawai tayi kwanciyarta a bayansa, sosai ruwa yake feshi yana jiƙasu.
Yusuf yace "ke ki tashi daga gurin nan, wannan ruwan da yake taɓaki ze iya saki mura ko zazzaɓi"
"gara ya samu tare, tunda bazaka tashi ba" tai maganar tana sake maƙalƙaleshi ta baya, Yusuf jiya yi yana nema ya dena fushin da yake, ya maze ya kunna fitilar torchlight ya haskata yace "malama ki cikani kije ki kwanta"
Noƙe masa kafaɗa tayi, Yusuf yace "Shikenan naji, tashi muje mu kwanta a taki shimfiɗar"
Tana jin haka ta miƙe suka nufi katifar, ta gyara musu ita Yusuf ya zauna yace "miƙomin ledar nan" ta juya zata ɗakko akayi wata walƙiya data haske ɗakin gaba ɗaya.
Gaba ɗaya ta afko kan Yusuf, ta riƙe shi gam jikinta yana tsuma, ta runtse ido sosai tana ajiyar zuciya.
Aikuwa akayi wata tsawa me ƙarfin gaske, ruwa ya sake ɓallewa, haska fuskarta yayi yaga yadda jikinta yake tsuma tayi wiƙi wiƙi da ido kamar Agola a rabon gado, yai dariya yace "wai baki iya addu'a bane, se tsoro da kuka?"
Tashi tayi daga jikinsa tana cuna baki gaba, ta miƙo masa ledar kifine a ciki, ya kalle ta yace "wani guri aka kwatantamin, nace bari inje in siyo miki kifi, gurin da nisa ga babu abun hawa a kusa, nayi tafiyar ƙafa sosai, shiyasa kiga na daɗe fa"
Shiru tayi tana kallonsa kamar taga wani sabon abu, ya buÉ—e ledar kifin, manya manyan gashashiyar tarwaÉ—a ce da karfashe.
Ya zauna ya dinga cire ƙayar ya ɗakko ya kai bakinta, tasa hannu zata karɓa ya girgiza mata kai yace "karki ɓata hannunki da ƙarni"
Haka ya dinga bata tana ci, can kawai yaga tana hawaye, ya kalleta yace "meyafaru kuma? Yanzu kuma me nayi miki"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.
"kifin ne ba daÉ—i" ya kuma tambayarta, nan ma ta girgiza masa kai
"to faÉ—an da nayi mikine ya saki kuka?"
Nan ma ta girgiza kai, ƙarshe tace "Nagode"
Yusuf yace "da akayi me?"
"Ka siyomin kifi"
"Haba Queen, meye abun kukan kuma? Kukan ki yana É—agamin hankali sosai, dan Allah kidena kinji, bakomai is my responsibility to make you happy Baby"
Yai maganar yana ɗago haɓarta da hannu ɗaya.
Shiru tayi tana ci gaba da share hawaye, seda ta ƙoshi sannan Yusuf yaje ya wanke hannunsa, ya dawo ya tarar da ita a zaune.
Yazo ya zauna a kusa da ita yace "oya kwanta"
A hankali ta zame jikinta ta kwanta tayi shiru, kamar wadda ruwa ya cinye, shima ya kwanta sedai ko mintuna biyar ba'ayi ba aka sake ƙyallo walƙiya, aikuwa ta kuma cakumo Yusuf kamar jikinsa ya tsage ta shige.
Yusuf yace "Gimbiya addu'a zaki dingayi, kidena tsoro haka"
Ba tace masa komai ba se sake lafewa da tayi a jikinsa, taƙi ko motsawa.
Haka aka cigaba da tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Shima Yusuf ya rungumeta gam a jikinsa, yana wasa da saman gashinta data É—aure da ribbon.
A hankali ya kai hannunsa kan ribbon ɗin, saitin kunneta yace "in cire?"
"inka cire min seka gyaramin"
Murmushi yayi, ya zare ribbon É—in dogon Gashin kanta ya baje akan katifar.