← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 127

Sashe 92

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Haruna kwana biyu ya samu sauƙi, Amal ta dena bibiyar sa, sedai ba ƙaramar kassarawa tayi masa ba, kwashe masa kuɗin Account da tayi, gashi ba damar kai rahoto yaje ya ɗaure kansa da kansa, gashi gaba ɗaya yanzu wanda zs nemi shawarar tasu hankinsu na kan wannan shari'a da'ake fafatawa.
Bulama gaba ɗaya yakasa nutsuwa, dukda wannan shirin da wannan shirin da yake yi, slide mistake Asirinsa ze iya tonuwa, kuma yasan koda tsiya, koda Arziki Yusuf baze bada abun nan ba, yayi signing ma a tabattar wannan signing ɗin nasane, me shige dana Daula amma yaƙi, babu irin dukan da baa'yi masa a gidan yarin nan ba amma fafur Yusuf yaƙi sakawa, wane ma tabbaci yake dashi akan cewar Recording ɗin yana gurin Yusuf, dan rainin hankali ba wani abun wahala bane a gurin Widad, zata iya raina masa hankali tace yana gurin Yusuf amma baya gurin nasa, nan ya dinga takura Ƙwaƙwalwarsa, akan lallai seya gano mafita.

Umma kuwa tun daga ranar da Widad ta bada wannan shedar taji ta tsane ta, bata sonta duk wannan halin wahalar sanadiyyarta ya shiga amma taje ta bada shedar zirr, gashi a maganar da Yusuf yai mata ranar da sukaje ganinsa a prison ya gayamata wai Widad É—in matarsa ce, ko ta yaya oho? Umma gaba É—aya tunaninta ya tsaya, bata da yadda zata yi wanda zata temaki Yusuf dashi.
Ta kira Suleman tace "dan Allah idan baya komai yaje tana son ganinsa"

Bayan awa ɗaya da rabi, sega Suleiman yazo suka gaisa sannan tace  "Suleiman, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi da ƙoƙarin da kake ta min, amma ina neman wata alfarma ne a gurinka"

Suleiman yace "To Umma ina jinki"

Tace "dama cewa nayi, ko zaka samo me siyan gidan nan, ai masa kuÉ—i a siyar, a saida Babur É—in Yusuf, da gurin furnitures É—insa, a É—auki lawyer me zaman kansa yaje kotu ya tsayawa Yusuf , ko Allah zesa a dace"

Suleiman yace "Umma da hakan ze yuwu, da tuni nayi wallahi base an siyar da gidan nan ba, har Office akamin aike daga sama, akace muddin nace zan saka kaina a cikin case ɗin nan, to tabbas zan rasa aikina, kuma nima za'ace dani aka haɗa baki, sannan a hanya aka kuma tsareni, akace idan nai involving kaina a case ɗin nan, to za'a kasheni da iyalina, kuma irin wannan barazana akewa duk wanda yai yunƙurin taimakon Yusuf, shiyasa kikaga an kasa komai a kai, bakiga inaji ina gani akace wai ba hukumar 'yan sanda ce ta bashi aiki ba, bayan kuma nasan ƙaryane ba, da hannuna na bawa Yusuf aikin nan, amma ina yunƙurin yin wani abu, komai ze kwaɓe "

Umma tai ajiyar zuciya tace" babu wanda ya bani mamaki irin Abbas, har gida yake zuwa ya É—aukeshi su tafi gidansu yarinyar nan, amma saboda rashin imani, yace wai be san zancen ba"

Suleiman yace "kiyi haƙuri, ki dena kuka haka, dama ai si mutane kullum ƙara koya maka hankali suke, amma ina tabattar miki Yusuf baze zauna a gidan yari ba, gaskiya zata yi halin ta"

Umma tace "Allah yasa, ina fatan haka nima"

Nurat kam kamar ta ɗora hannu aka tai ihu, ta rasa abunda yake mata daɗi, wai ace Widad ya bada wannan shedar aka Yusuf, dukda irin yaddar da tayi dashi, tabbas da Yusuf yana neman wani abu a gurin Widad dabe dinga bata kariya ba, yanzu shikenan saboda shedar Widad, ta tabatta Yusuf yayi abunda ake zarginsa dashi, kamar wadda mintsina, ta tashi da sauri don taje ta sato wayar Mummy tai waya, sedai tana fitowa falo ta tarar daddynta yana kallon labarai, 'yan jarida na bayyana abunda ya faru a kotu, Alhaji Musa yace  "Maman Nurat, kinga shari'ar yaron nan ko? Dama na faɗa miki, irinsa ba abun tausayi bane, gashi nan ita kanta yarinyar ta tabattar da abunda ake zarginsa dashi, bari in kira Bulama"

Ya ɗakko wayarsa ya kira Bulama, "Allah ya baka yawan rai, ai yau naga yadda shari'ar nan ta kasance, komai ya tafi daidai, kayi ƙoƙari gaskiya, haka ake son Amini, gashi baya nan amma ka tsaya tsayin daka akan sha'anin iyalinsa, gaskiya kayi namijin ƙoƙari, Allah dai yasaka da alkhairi"

Nurat bata iya jin abunda ake cewa daga ɗaya ɓangaren, amma tana ganin yadda Daddynta ke ƙyaƙyata dariyar mugunta a waya.

A hankali ta juya ta koma ɗakinta, tana hawaye tace "Allah sarki Yusuf, ya za'ayi in fita in gayawa duniya cewar ba kai kayi garkuwa da Widad ba, da saka hannun mahaifina a sace su Yusuf? Ta yaya? Tabbas idan aka rufe Yusuf ba'a masa adalci ba, definitely tasan akwai yadda akayi har suka kuɓuta aka kamasu a ƙauye, amma Yusuf baze garkuwa da Widad ba, ta zauna tai shiru tana tunani, bata san ta ina zata fara temakawa Yusuf ba, amma tabbas ƙarshen zalunci an masa.

Ramlah ce tsaye akan Fahad tana zazzaga masa masifa, "Wallahi Amal baka isa ba, tun wuri ka maida hankalinka, nafi ƙarfin ka wulaƙantani, wato ka gama dani ka kama wasu, to baka isa ba tun wuri kaje ka turo azo ayi maganar Auren nan"

Fahad yai wata irin dariya sannan yace "Ramlah kenan, waye yake yaudarar wani tsakanin nida ke, dama a rashin wannan yarinyar ne, tuntuni tun ina ƙasar waje kin san ita zan aura, kuma gata ta dawo, dan haka me kike so inyi miki kuma? Kawai ki rungumi sorry, in kin samu wani wanda zaku daidaita se ku haɗe, dukda dai bance ke mummuna bacd but gaskiya ga balarabiya ina kallo bazan aureki ba, sorry kawai "

" Ni kake kallo kake gayawa haka? Lallai baka san Ramlah ba, kai ƙaramin ɗan isaka ne, wallahi baka isa ba, zaka ga abunda zan maka "

Fahad ya busa hayaƙin shisha sama sannan yai murmushi yace " Hmm keme baki san waye Fahad ba, karki bari ki gane waye Fahad tabbas "

" Ni kake gayawa haka ko? "

"Na gayamiki ɗin, dama haka bariki ta gada, kuma ki shiga hankalinki tunda wuri, tun ban saɓa miki ba"

Ramlah ta kalleshi tai ƙwafa, tai waje a matuƙar fusace, tana fitowa tai karo da Hajiya Sarah ta fito zata fita, mamaki yakamata ganin Ramlah daga part ɗin Fahad, ta tsaya Ramlah ta ƙaraso, tana ƙoƙarin buɗe motarta, Hajiya Sarah tace "Ramlah, lafiya kuwa? Me kika je yi ɗakin Fahad? Ina fatan lafiya?"

Ramlah ta kalleta tace "ba lafiya ba, kuma wallahi ki gayawa É—anki ya saurari abunda ze biyo baya"

Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa? Meya haÉ—aki da Fahad É—inne? Me yayi miki ne?"

"Ki tambaye shi, shi yasan me yayi, kuma ya jira sakamakon abunda yayi min"

Ta bankaɗa ƙofar motarta ta shige ta jata a guje, mamakine ya cika Hajiya Sarah, ta shiga part ɗin Fahad, tana zuwa ta tarar yana shan shisha ta kalle shi tace "Fahad, wato har yanzu baka dena shaye shayen banzan nan bako, kana kawo mana matan banza har cikin gidan nan, kasa ubanka yazo ya kamani da faɗa da masifa, wallahi kaji tsoron Allah, ita kuma Ramlah meye ya haɗaka da ita?"

"wani abun tace miki na mata?"

"Ban sani ba, me take a part É—inka? Ko itama shashancin kuke yi?"

"Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kawai wasu suratanta ne na banza, marasa tushe balle makama, tazo ta nawa mutane Hayaniya a ka"

"wane irin Hayaniya ce? Gayamin kasan halin uwatta sarai, daga ita har yaranta ba mutunci suka cika ba, har gara Anwar ma, amma wannan me soyayyen idon, idan ka sake wani abu mara daɗi ya haɗaku dasu, wallahi duk abunda suka maka kai ka janyowa kanka, kaje ka ƙarata kai da uwarsu, idan yaso ubanka yasan yadda zeyi dasu, tunda 'yan uwansa ne, na gaya maka, tunda wannan rayuwar ka zaɓawa kanka Fahad, gaka nam ga duniyar kaje kayi Allah ya temaka "

Ba ce mata komai ba, ta fito ta baro É—akin nasa, zuciyarta sam babu daÉ—i, ace yaronta na farine ke irin wannan mummunar rayuwa haka, ranat baya mata daÉ—i Sam.

Amal ta rasa yadda zata yi da uban kuÉ—in data damfari Alhaji Haruna, gashi sam Mummy bata san abunda ya faru da ita ba, balle tasan da wannan uban kuÉ—in data damfari Alhaji Haruna, sedai Amal ta kasa gane abunda yake damunta, gaba É—aya yanzu kullum cikin ciwo take, nan ciwo can ciwo, abun ya fara damunta, ta yanke shawarar zata je ganin likita zata je taji meye yake damunta haka.

Ramlah kuwa data bar gidan Bulama kamfaninsa ta tafi, yana tsaka da aiki yana shirin shiga meeting se gata, babu sallama babu komai ta tsaya ta tstsareshi da ido.

"Ke lafiya kuwa? Ni na rasa waye yafi hanki tsakanin ke da babarki, ya zaki zo ki tsaya a kaina haka kina ƙaremin kallo babu ko sallama"
"kaga suararamin kawai, tsason shekaru kana juya mahaifiyarmu, muna abunda kake so, wancan satin har kotu kasa naje na bada sheda akan wannan sharia'r, to nazo da buƙatata guda ɗaya tam, da nake so kamin"
"wace irin buƙatace haka? Bayan seda aka baki wani percentage kema, kuma idan kuɗin nan suka samu hadda ke za'a ci"
"Niba kuɗi zaka bani ba, shekaruna sun na ina zaune a gida na gama karatu bana aimin fari, balle na baƙi, kuma ɗanka Fahad ya taɓa min Alƙawarin Aure, dan haka tunda wuri azo ayi maganar da za'ayi a wuce gurin"
"Nifa ban gane maganar da kike ba"
"Kamar yaya baka gane me nake nufi ba? Wane yaren nakeyi maka? ÆŠanka Fahad ya Aureni"

"Haba Ramlah, wacs irin kwaÉ—on magana ce wannan haka mara daÉ—in ji? Baki san Widad ze aura ba?"

"ban saniba, kuma matsalar kuce ba ta Ramlah ba, kawai ayi maganar da za'ayi"

Bulama yace "ni kike wa magana a haka? Ƙwarai kuwa waye kai a gudina da bazan maka magana a haka ba, ina ƙarewa 'yar gidan Daula shekaru ta kwashe tana maka wulaƙancin data ga dama, balle kuma ni da kake wa kallon biri ina maka ta ayaba, kawai kayi abunda ya dace, ko kuma komai ya faru "

Bulama yace " Ramlah, ban san meyasa kike haka ba? Kema kin san aurenki da Fahad ba abune me yuwuwa ba ko? "
Chapter 92 · 0% Book details