Sashe 102
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
   Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji
 Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606
144_145
Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me yayi masa haka?"
Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai, kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat, amma gaba É—aya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na kwashi kuÉ—ina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani bayani "
Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar É—a yake a gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa "
Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren.
Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya taƙi shiga sam.
Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa tana bala'i "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?"
Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?"
"ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?"
Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance É—an uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa"
Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato ba tsammani ya É—aga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa.
Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso kawai ki hauromin É—aki haka?"
"Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba"
Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana"
"Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi? Wani munafukin ne ke neman haÉ—ani da 'yar uwata?"
" Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba, macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it, wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan iya aikatawa "
Gaba É—aya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa wani beji abunda ta faÉ—a ba.
Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa.
Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja yaga likita.
Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki, tabbas yasan da tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali, "Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa.
Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon da take masa idan ya tsokane ta.
A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daÉ—i a nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure.
Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta.
Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace
"wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?"
Amal tace "lafiyata ƙalau, period kawai nake shiyasa"
Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?"
"A'a sekin faÉ—a"
"wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri"
Da sauri Amal ta kalleta tace "A kasheshi kuma? Me me kikace masa?"
"Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa"
Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan ɗaya.
Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon tace "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa.. W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane" kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam.