Sashe 96
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Seda Ramlah tai dariya me isarta, yayimda Fahad ya bita da kallon mamaki irin dariyar da take ƙyaƙyatawa, tace "Fahad ai duk yadda kake tunanina na wuce nan in gaya maka, shiyasa nake ta binka Allah ma'aiki ka aureni, ban nuna maka nasan kana ɗauke da cutar HiV ba harka samin ba, nake ta lallaɓaka amma baka gane ba, to na ɗau matakin daya dace, dan haka zan maka Albishir, Danni agurin Albishir ne, ina me farincikin sanar da kai cewa Ubanka Bulama ma yana ɗauke da wannan ƙwayar cuta "
Ai a razane besan ya miƙe tsaye ba akan ƙafafunsa, ya dinga binta da wani ƙasƙantaccen kallo, yace " mekike nufi? "
" Kurma ne kai? Ko yaren da nayi magana dashi ne baka ji, nace ubanka mahaifi wato Bulama, shima yana da cutar, na saka masa dan haka seka hanzarta kaje kasa shi ya fara shan magani akan lokaci, tun kan ciwon ya huda shi sosai, sannan yama da kyau ka binciki babarkama, ko itama ta rabauat seku duƙufa shan magani, kaga rabajau daku idan wannan ya manta lokacin sham magani yayi, se wannan ya tuna muku "
Kamar Fahad ze fashe da kuka yace" kina nufin, Dad É—ina yana É—auke da wannan cutar ne? "
" babu ko shakka " ta bashi amsa
" Amma wace irin tinkiyace ke Ramlah, yanzu sekiyi mu'amala dani ki koma kiyi da mahaifina saboda mugun abu? "
Ramlah tace " duk cikin iya takune, da farko shiya fara ɓatamin rayuwa, na rufa masa Asiri, har na fara sonka, tun a wancan lokacin ya fara take taken baya goyon bayan soyayyar, kaima kazo ka nemeni na bada ksi bori ya hau ina zaton zaka Aureni, amma kaƙi kuma na kasa rabuwa da kai, duk da yadda Anwar ya dinga nusar dani, kawai naga magani a jakarka, na tambayeka na mene kace min na gyaran jiki ne, nai nai ka bani ka hanani, shine nai snapping nace a samomin maganin, aka gayamin na meye, nayi kuka na shiga damuwa amma nakasa gayawa mowa damuwata, na cigaba da shaye2 daka koyamin dan ragewa kaina tension, naga babu hanyar da zanbi in huce takaicin nan daka ƙunsami , seta hanyar sanyawa Ubanka wannan ciwon, se duk muyi jinyar tare, nake ta binka ka aureni kana rainamin hankali kana ganin ka cuceni, kuma ina me tabattar maka da cewa dukda kamilewa irin ta ƙaninka Ramadan, shima zan iya bashi nasa rabon, dan haka seka san abunyi tun dare be maka ba ".
Ta ƙarasa maganar tana hararasa, ta bar ɗakin.
Ya dafe kai ya zauna yana faɗin" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ya isa tsakanina dake, kin cuceni, ba kowa aka cuta ba se Mother, tana gefe ta kawamme kanta ta riƙe Aurenta an kwasa mata masifa, Daddy why? "
(dama ita zina haka take, idan ka yi da É—an wani za'ai da naka, idan ba ayi da naka ba in one way or another, dole se wannan illar zinar ya shafi wani naka, zina bata da wata riba sam, ga zunubi, ga cuta ga É—aukar alhakin wanda basuji ba basu gani ba, Allah ya shirya al'ummar musulmi baki É—aya)
Fahad ya cigaba da kuka yana tunanin, ta yaya ze fara gayawa Mummy abunda ya faru, wama ze tunkara da wannan Mummunan labari haka?
Babu wanda aka cuta sama da Mummyn mu, dama har yanzu Daddy yana biye biyen mata? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un.
"Ramlah kin cuceni, tsakanina dake Allah ya isa kawai ban yafe ba Wallahi, wayyo Allah na, ban taɓa dana sanin irin rayuwar da nayi ba se yau, ubangiji Allah yasa Mummy bata ɗauka ba, saboda abun kunya da Allah wadai, ace inbi yarinya mahaifina ma yayi, wace irin rayuwa ce haka? Ta yaya zan tun kari Mummy in sanar da ita ta binciki lafiyarta?
Fahad ya zauna zaman dirshan a ƙasa yana kuka, sekace ɗan yaye kuka harda majina, ya rasa inda ze saka kansa dan baƙin ciki da takaici, yau a dalilinsa za'a sakawa mahaifiyarsa wannan larura, koma an riga an saka mata, yanzu ta yaya ze tun kare ta da wannan maganar?
Seda aka watse daga kotu sannan Bulama yabi Justice A duste chamber, A dutse yai murmushi yace "ya kaga shari'ar tamu? Naga tunda muka fa fara shari'ar baka zuwa"
Bulama yace "ya za'ayi inzo, sannan shari'a tayi dan yi, shekaru talatin ai kan nan komai yayi dai dai , amma abunda ya bani mamaki shine meyasa zaka ce wai yana da damar daze ɗaukaka ƙara, ɗaukaka ƙarar na mene kuma? Tunda ka yanke hukunci, meye kuma na wani ze iya ɗaukaka ƙara kuma? "
" Bulama kenan, har yanzu baka san meye shari'a ba, babu yadda za'ayi aiwa mutum hukunci a irin kotunanmu sannan ka hanashi ɗaukaka ƙara idan hukuncin be masa ba, ba'ai haka ba haka ƙa'idar aikin take ba, nan da kwanaki talatin yana da damar daze je ya ɗaukaka ƙara "
Bulama ya ɗanyi ƙaramin tsaki yace " to yanzu meye abunyi? "
" Eh to, iyakaci kuyi ƙoƙarin toshe duk wata dama da zata saka ya ɗaukaka ƙararar, idan kuma ya ɗaukaka ƙararar, to se ka faɗi ka tashi suma ka siye su "
Bulama yai tsaki yace " Aini daya ɗaukaka ƙarar da kar ya ɗaukaka idan na samu abunda nakeso, can ta matse musu, ni yanzu zanje in maida hankali in samu abunda nake so "
A dutse yace "Shikenan, as you wish"
Bulama yace "Nagode sosai da gudunmuwar ka"
Suka musabaha, ya bar chamber.
Bulama kai tsaye gidan da Widad take ya nufa, yana zuwa ya tarar da ita a zaune cikin zumbulelen hijjabinta, ta ƙara zabgewa, duk babu ƙibar nan, Widad lazumi kawai take a zuciyarta, dan tasan yaune ranar daza'a yankewa Yusuf hukunci a kotu, sedai zuwa yanzu bata san wani hukuncin za'a yanke masa ba.
Bulama yazo ya sakata a gaba yana ƙare mata kallo, shikansa yaga yadda duk ta rame ta fita hayyacinta, mutum baya ce ita ce Widad Nasir Daula ba.
Tunda ya shigo bata motsa ba, balle ta É—aga kai ta kalle shi, ta zuba guri É—aya ido ko motsi ba tayi.
"Ina fatan kinji hukuncin da aka yankewa wannan sakaran xa kike iƙrarin mijinki ne? Koda yake ba lallai ki sani ba, amma shekarun babu yawa, shekaru talatin da ɗaya ne, se tarar miliyan biyar, sakamakon kama shi da laifin garkuwa da mutum, laifin fyaɗe da kuma sata, ina fatan yanzu kin san me Bulama ze iya aikatawa? Koda yake tun ba yau ba kin san irin abunda nake iya aikatawa idan ina buƙatar abu"
Widad bata motsa ba bata kalle shi ba, tai shiru abunta tana cigabs da ƙurawa guri ɗaya ido.
"Yanzu kin shirya gayamin inda abubuwan nan suke ko sena je nasa an kashe Uwar Yusuf"?
A hankali ta É—aga kai ta dube shi, tace "kai a tunanin ka zan bar mijina ya shekara talatin da É—aya a gidan yarine? Lallai baka da hankali, kuma ga dukkanin alamu ka manta wacece Widad ko? Zan baka mamaki kuwa, Yoseef baze zaman gidan yari ba, kuma bazaka samu abunda kake so ba"
"Kin zaɓi mahaifiyarsa ta mutu kenan?"
"Ba zata mutu ba se lokacinta yayi"
"Shikenan, tunda haka kika zaɓa, zaki gani kuwa"
Widad tace "meye ban gani ba Bukar, zalunci da mugunta wanne ne bakamana ba? Kasa aka kashe mahaifiyata, kasa aka haukatani, kai kutungwila ka aurawa mahaifina matar da ta dinga azabtar da shi tsawon lokaci, yana bauta ita da 'ya' yanta amma suna azabtar dashi, hakan be isheka ba kasa aka dinga kaimin farmaki dan a kasheni akan dukiyar nan, banda message na razanarwa da tashin hankali da kake turomana, ƙiri ƙiri ka rabani da ƙasata ta haihuwa saboda mugun zaluncinka, kasa nayi rayuwa kamar matacciya, babu me raɓata ka jefa tsoron mutane a zuciyata, kasa aka dinga farautata kamar dabbar daji, Allah ya kawo Yoseef na fara samun sassauci, nan ma akasa akayi garkuwa damu, muka kuɓuta ya dinga wahala dani, amma a ƙarshe kalli sanadin zaluncinka abunda aka masa, nida abun a kaina ya ƙare da sauƙi, shi meye nasa a cikin lamarin nan? Wallahi wata shari'ar se a lahira shi kaɗai ze sakamin wannan zalunci da kamin "
Bulama ya ƙyaƙyace da dariya yace " ke yanzu da duk kin san ni nake shirya wannan abubuwan amma kika ƙyaleni nake cin karena ba babbaka? Lallai kin iya wauta, meyasa kika ƙyaleni kikemin kallon uba bayan kin san ni maƙiyinki ne "
Widad tace " talala na maka, tun ranar da aka kashe mahaifiyata aka ambaci sunanka, bazan taɓa manatawa ba, sedai na ƙyaleka ne saboda muddin nai wani yunƙuri zaka kashe min mahaifi, shiyasa na ƙyeleka, amma a yanzu inaji a jikina kana daf da yin faɗuwar baƙar tasa"
"Hmm, lallai yarinya dole a sarawa ƙoƙarinki, da iya takunki tun kina ƙarama kanki yake kawo wuta sosai, kin iya lissafi sosai, Amma ki sani ni tsohon hannune a duniyanci, tunda hukuncin da akayiwa mijinki be zama izina a gareki ba, zan sa a kamo min uwarsa, inzo in yankata a gabanki tunda ke taurin kai baze barki ki ƙwaci kanki ba"
Wani mugun kallo tayi masa, ya tashi ya fita daga É—akin nata, bayan tafiyarsa Sabuwa ta shigo É—akin Widad tana dube dube tace "dan Allah ban yarda memory É—ina a É—akin nan ba, tun jiya nake nemansa ban ganshi ba sam"
Widad tace "nima ban ganshi ba gaskiya, dan Allah Al'ada ne yazomin, tunda aka ciremin cikin nan ban ƙarayi ba se yanzu, dan Allah ki aramin dubu ɗaya, in rubuta miki irin wadda nakeso ki kai kowane shago a baki, idan Allah ya fitar dani zan bi yaki"
Sabuwa tace "to shikenan" taje ta samo biro da takadda ta bawa Widad ta raba takaddar biyu, Widad tai rubutu akan kowacce takaddar, da yake Sabuwa bata iya karatu ba, Widad ta rubuta ta bata ta É—akko wata leda tace "dan Allah karki gayawa kowa na aike ki, ki kai shago kice a bani abunda na rubuta a jiki, ki haÉ—a musu da wannan ledar ki basu"
Sabuwa ta karɓa tace "shikenan, zan sawo maki insha Allah"
Widad tace "nagode sosai"