Sashe 53
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta, shiru ta ɗanyi tana ƙara so ta tabbatarwa da zuciyarta kalaman Yoseef ɗin, na mafarkine kawai baze zama gaskiya ba, amma dagaske kenan Ta kamu da soyayya?
Tana cikin tunanin taji Yusuf yace "Wife, ina kika samu wannan turaren ne, tun rana yake tashi a jikinki, ina ta ƙoƙarin riƙe kaina, tauraren nan yayi daɗi a jikinki sosai"
Cikin cuna baki irin na wanda ya gama kuka tace "Jamila ce tabani"
"Wow, kince mata kin gode dai ko?"
Ta gyɗa masa kai, yace "good, ki tambayeta kuɗin turaren nan, zan bayar a ƙara mana"
"Dayawa fa ta bani, wai itama maƙociyarta ce a barrack ɗim da take ta bata dayawa da ta haihu, shine nima ta zubamin kuma da yawa fa ta bani"
Cikin nishaɗi yace "dukda haka i suppose to pay for it, naji daɗi Sosai, bazan manta kyautar turaren da kika bani ba, kyauta ta farko da kika bani, kyauta daga hannun masoyiyya, amma sedai naji kamar wari nake shiyasa kika bani turare"
Duk da a damuwa take, amma seda tayi dariya tace "taɓ duk wannan gayun naka, dukda basajar da kake yi amma abunda ya fara birgeni da kai ashine tsaftarka, dan wasu dan suna irin wannan aikin se suyita ƙazanta, su a dole se sun nuna talaucinsu, abun da yasa na baka turaren nan, duk lokacin da naji turare na tashi a jikinka, se naji wata kasala ta kamani, ko laifi kayi min seka rage ƙarfin fushin da nake ɗauke dashi, shiyasa nace bari in canza maka turare ko zan dena jin hakan, wataƙila daga turaren naka ne "
Yusuf yayi murmushi yace 'to daga baya mekika fuskanta?"
"Nagane cewar kwarjini kakemin, kuma abun ba daga turarenka bane daga kai É—inne"
Yusuf yace "Ahse dai an daÉ—e ana so"
Tace "Ana son me?"
Yace "bakomai, just forget, ni dai ki bari kawai in shaƙi wannan ƙamshin me daɗin gaske"
Shiru tayi tana saurarensa ba tare da ta sake cewa uffan ba, aikuwa Yusuf ya wuce makaÉ—i da rawa, yau dai be sha cizo baðŸ¤ðŸ¤, sema wani farinciki mara misaltuwa da suka tsinci kansu a ciki.
A hankali a kunnenta yace "God bless you my Wife, thank you very much"
Ƙin magana tayi, sema lafewa data sake yi a jikinsa, yace "tashi in ɗora mana ruwa, naga akwai sauran kalanzir ko?"
Widad tace "eh akwai, amma shekaranjiya Hindu tayi girki a kai, idan babu se muyi dana sanyi"
"No akanme? Haka kurum in baki ruwan sanyi kiyi wanka inje ki shiÉ—emin, abunda baki saba ba, bakomai zan dafa mana, inma babu naje in tada murhu yanzun nan"
Widad tace "Murhu kuma a daren nan?"
"Eh mana, meye a ciki, muna cikin baccin mu kin tasheni kin janyo mana aiki"
"Au hakama zakace ko?"
"A'a tuba nake, wane ni" yai maganar cikin murmushi.
Akayi sa'a da kalanzir ɗin, ya fito da rishon tsakar gida ya ɗora musu ruwa, saboda yanayi na zafi kae ɗakin ya ƙara ɗaukar zafi, kafin ruwan yayi zafi, Yusuf ya ɗakko musu gashashiyar gujjiya suka zauna suka kama cin abarsu suna hira a wannan daren, se kace aljanu.
Jin ana ɓuruntu, yasa Hanne ta miƙe cikin tsoro ta leƙa taga dan ganin meke faruwa, ta hangesu zaune a cikin farin wata, suna ciue ciyensu suna hira.
Ta jinjina kai tace "lallai wannan kinyi dacen miji, yana sakar mata fuska sosai saɓanin mazan garin nan, wanima murmushi baze iyayiwa mace na wai karta raina shi.
Ƙarshe ma tare sukayi wankansu, Yusuf jinsa yake kamar wani sabon mutum, wani irin farinciki ya mamaye zuciyarsa, sedai duk da ɓangaren Widad ma hakan take, amma ta kasa manta mafarkin da tayi akan Yusuf, haka kurum abun ya tsaye mata a rai.
Anwar gaba ɗaya abunda ya faru yau a gidansu ya tsaye masa a rai, muraran mahaifiyarsu ta tabattar maaa da tafi ƙaunar Ramlah akansa, kuma bata son ace ga laifin da tayi, balle a saka rana zata mata hukunci, ransa ya ɓaci sosai dan haka ya fara tunanin, wane mataki yakamata ya ɗauka, dan janye jikinsa daga harkokin gidanma gaba ɗaya?.
Yana kwance yana tunanin meye mafita, yaji wayarsa tana ringing, da kamar baze É—aga ba amma ya janyo wayar ya É—aga.
Jin muryar Nurat ce tayi masa sallama yasa ya ɗan saki ransa ya amsa, Nurat tace "Yaya Anwar, ɗazu kazo baka samu ganina ba"
Anwar yace 'eh, nazo mu gaisa amma megadi yacemin zan ja miki matsala, wancan zuwan da nayi ma na jamiki matsala amma baki gayamin ba"
Ajiyar zuciya Nurat tayi tace "hmm kai dai bari kawai Yaya Anwar, abunne duk se a hankali, na kasa gane kan mahaifina gaba ɗaya, ya hanani fita zuwa ko ina, sannan ya hana kowa yazo inda nake, na kasa gane manufarsa, sam ban gane inda ya dosa ba"
Anwar yace "Amma kuma lokacin da yazo ya samemu tare be nunamin komai ba"
"Ai haka yake yi, baya taɓa nunawa a gaban mutane, amma bayan tafiyar ka har dukana yayi"
"Subhanallah, kiyi haƙuri wallahi ban zan zuwana ze kawo miki matsala a gurin mahaifinki ba"
Nurat tace "bakomai karka damu Yaya Anwar, ba laifinka bane, sannan kayi haƙuri rashin haɗuwar da mukayi"
"A'a bakomai Nurat, ina fatan ubangiji Allah ya daidaita tsakanin ku, dama biyowa nayi mu gaisa, wallahi nima kusan a cikin damuwa nake Nurat"
"Subhanallah, meyafaru?"
"Wallahi Nurat abubuwan nan da suke faruwa gaba ɗaya na rasa abunyi ma, jiya Ramlah a buge ta dawo tayi mankas da ƙwaya, amma ƙiri ƙiri dan na hukuntata Mummy ta fituttuke tace ƙaryane, taita faman Yimin faɗa, ban san meyasa take haka ba, abu in dak Ramlah ce bazata taɓa ganin laifinta ba, ƙarara take nuna banbanci a tsakaninmu"
Nurat tace "se haƙuri ai, lamarin iyayen nan namu sedai addu'a, ni gashi nikaɗaice a gurin iyayena, amma wasu lokutan idan Daddy yayi min wani abun, se inga kamsr bashi ya haifeni ba, yaita treating ɗina a hagunce, abun yana damuna sosai"
Anwar yace "kin san kowane bawa da irin tasa jarabbawar, kowa akwai ta ɓangaren da Allah yake jarabtarsa, sedai fatan Allah ya bamu ikon cin jarrabawa"
"Ameen Yaya Anwar"
"to akwai wani news ne daga gareki?"
Ajiyar zuciya tayi tace "News kam baza'a rasa ba, amma kasan wai Yusuf ɗan sanda ne ashe?"
'Eh nasani, amma da farko nima ban saniba, se daga bayan nan, da aka fitar da wannan Sanarwar"
Nurat tace "Amma Anwar meka fuskanta game da wannan Sanarwar"
"To ni dai abunda nake gani, wata maƙarƙashiyar ce aka shirya domin ɓatawa Yusuf suna, turoshi akayi domin bincike akan maƙiyan Daula, amma kuma daga baya ake nema a ɗora masa sharri, ni yadda naji ma sunce wai babu wanda ya turoshi aiki gidan"
Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Yaya Anwar, wannan abubuwan duk shirine akayi shi domin a ci mutuncin Yusuf, kuma shiryayiya ce aka shirya wannan lamarin, ni ban san yadda za'ayi Yusuf ya ƙuɓuta ba, yana cikin matsala"
Anwar yace "hakane, nima naje na samu Alhaji Bulama, tunda yana da alfarma a ƙasar nan, ayi bincike yadda yakamata"
Nurat tace "Yaya Anwar, tayasu da Addu'a shine abunda yakamata, amma harkar ƙasar nan se godiyar Allah, gashi haryanzu babu labarin Mahaifin Widad"
Anwar yace "wallahi kuwa, to Allah ya wuce mana gaba, Allah ya kawo mafita gaba É—aya"
"Ameen ya Allah, nagode sosai Yaya Anwar"
"Bakomai, nima nagode"
Washegari da safe, Widad ta riga Yusuf tashi, yau da kanta ta dafa ruwa tayi wanka, ta gyara tsakar gidan nan fes tayi wanke wanke, ta zuba shinkafa ta fara tsincewa, ta tsince shinkafar nan iya yadda zata iya, amma Yusuf be tashi daga bacci ba,
Taje inda yake kwance ta zauna ya gama ƙare masa kallo, sannan ta shiga tashinsa kamar zata tashi jariri.
A hankali ya buɗe ido, yanayi yana lumshewa alamar bacci be isheshi ba tace "wai yau da Yunwa zaka barni?"
Murmushi yayi ya sake lumshe idonsa, cikin Shagwaɓa tace "tashi Yunwa nakeji fa"
'Nikuma bacci nakeji "
"to bari inje in dafa da kaina, tunda ba zaka tashi ba"
"No sorry, bari in tashi in dafa miki'
"kaga harna dafa ruwa nayi wanka, na tsince shinkafan ma"
"Haba dai?"
'dagaske nake fa"
Ya miƙe ya duba ta share ko ina, tayi wanka har shinkafa ta gyara ta wanke, murmushi yayi yace  "Alhamdilillah, mutuniyar ta fara zama mace"
"Dama ni namijice?"
"A:a ni bance ba, amma mace ai seda aikin gida, kice zamuyi surprising Daddy '
" Sosai makuwa "
Ya ƙarasa musu girkin, suka zauna sukaci Abincin su.
lokaci lokaci Widad se taji gabanta ya faɗi, amma ta dake da dinga ɓoyewa, dan karya gane tana cikin damuwa.
Widad tace "Yoseef ina kewar su Mama sosai da Hindu, mutum rahama ne"
'Ni Aljani ne kenan? "
" A' a ni ba haka nace ba, na saba ganinsu ne, ina ganin mostinsu da giftawarsu, amma kwana biyun nan shiru bana ganinsu"
Yusuf yace "yanzu kin gane amfanin mutum a rayuwar É—an adam kenan? Babu yadda za'ayi mutum yayi rayuwa shi kaÉ—ai babu mutane kuma yace hakan yafi daÉ—i"
'hakane, dan ina gudun a cutar dani ne, shiyasa nake gudun mutane, amma yanzu nasan wannan mutanen da muke tare dasu bazasu cutar dani ba, shiyasa nake kewarsu"
"hakane, naga taku tazo É—aya dasu sosai, Amma naji anjima zasu dawo ai ko?"
"Eh anjima zasu dawo insha Allah"
"to Allah ya dawo dasu lafiya"
Ta amsa da Ameen.
Anwar sosai yake tunanin samawa kansa mafita, akan lamarin gidansu dan duk se yaji zaman gidan baya kansa ya fita a ransa.
Shiga yayi gidan da nufin gaida mahaifiyar su da safe kamar yadda ya saba, sedai ta window ɗin ɗakinta yaji suna magana ita da Ramlah, seya tsaya be ƙarasa ba.
"Ramlah wannan rayuwar da kika É—auka ba inda zata kai miki, ki kiyayi kanki da shaye shaye nan, kinga na gwale 'yan uwanki jiya amma tabbas maye kikeyi, dan dai inajin daÉ—in shawara dake ne da fushi zanyi dake"
'Mummy na dena fa"
"Shikenan, ai dama nasan zaki dena, nace ya kukayi da Fahad É—inne, ina fatan dai baze tona mana asiri ko gurin babansa ba"?
' Haba Mummy, shiya fara ma tunda abun nan harda shi ake ƙaruwa "