Sashe 27
Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata gidan Talabijin yayi hira da Daula, akan yadda akayi ya fara kasuwanci, nasarorin daya samu da kuma ƙalubale, duk ya dinga bada amsa, gashi duk hirar da za'ayi dashi se yayi zancen Yayansa Yusuf, se yayi musu addu'a, duk inda me Suna Yusuf yake Nasir kamar ze duƙa masa saboda girmamawa, komai ƙanƙantar Yaro indai yana da wannan sunan, to tabbas yana da ƙima a idon Nasir.
Babban abunda ya daɗa ja masa baƙin jini shine, yadda yakewa al'umma hidima, yake facaka da dukiyarsa gurin hidimtawa al'umma da addini, wanda sauran abikan kasuwancinsa basa yi, hakan yasa ya ƙara samun masoya ta kowane fanni.
A cikin hirar da'ake dashine ya bayyanawa 'yan jarida cewar, shifa ainihin kuɗin daya fara kasuwanci dasu bashi aka bashi, kuma be biya bashin ba, ya sanar dasu cewa wanda ya bashi bashin ya gaya masa me kuɗin yana nam zuwa ya karɓi wannan kuɗi, dan haka gundarin dukiyar da yake juyawa yana samun riba akwai me ita, kuma duk sanda lokaci yayi indai me dukiyar ya bayyana to tabbas shi keda kaso bakwai cikin goma na dukiyar daya mallaka, ya ƙara da cewa a hirar nan da suke, tuni ya ware wannan dukiyar guri guda, ko bayan ransa duk wanda yasa hannu akan wasiyyar daya bari da takaddun dukiyar daya ware, to tabbas wannan dukiya tasace, ko waye yasa hannu akai tasa ce "
Wannan hira da Daula yayi ba ƙaramin cecekuce ta janyo ba a cikin al'umma, wasu suna jinjinawa amanarsa, wasu suna ganin wautarsa suna inama zasuga inda tajaddun suke su saka hannu su karɓe kuɗaɗen, wanda suke da hannun jari a kamfanunnukansa suka shiga zullumi, akwai dukiyarsu a cikin kuɗaɗen Daula, kuma muddin ya janye daga kasuwancin to tabbas zasu talauce, dan haka suka shiga tunanin nemawa kansu mafita.
Katsam akayiwa Huda scanning, aka tabattaf da cewa tana ɗauke da ɗa namijine a cikin ta, ana gayawa Daula ya zube yayi sujjadar godiya ga Allah, bakinsa yaƙi rufuwa, farincikinsa yakasa ɓuya.
Sunyi murna sosai da wannan kyauta da Allah yayi musu, Kasancewar Daula ya daɗe yana kuma neman haihuwa yasa shi, ya shiga gayawa abokansa ai Madam ta samu rabo, kuma anyi scanning ance zata haifi namiji, zatonsa duk masuyi masa dariyar nan masoyansa ne, zasu taya shi farinciki, ashe abunda be sani ba ta ciki na cikine kawai, dan gaba ɗaya ba ƙaunarsa suke ba, dukda da yawa su, Daula shine silar Arziƙinsu.
Watarana suna zaune suna hira da abokansa, suke bugun cikinsa Haruna yace "Yanzu kai Daula, gashi ga abunda kace akan cewa akwai me kaso bakwai na dukiyarka, yanzu idan ba'a samu wanda yasa hannun bafa? Sannan meyasa me dukiyar baze zo ya karɓa ba"
Daula yace "me kuɗin, yayana ne da matarsa da Allah yayi musu rasuwa, kuma shi ya gayamin akwai wanda ze karɓi wannan kuɗin, dan haka nayi a rubuce ko bayan raina idan mesu bezoba, a rabawa al'umma su, ko kuma a gina abunda al'umma zasu amfana"
Haruna yace "duk wannan uwar dukiyar, kace a rabar?"
Nasir yace "eh mana, haka shine yakamata ai, har wasiyya nayi yadda na kasafta dukiyar"
"to yanzu a ina suke, balle mesu ɗin yasa hannu ya karɓa?"
Daula yace "idan har me dukiyar nan yazo, no matter how hard seya karɓi abarsa, babu wanda yasan inda suke, se Allah seni, nayi bayanin komai a video wasiyyar dana bari, na danƙashi a hannun 'yata Widad"
Munir yace "Widad kuma? Wannan jaririyar yarinyar?"
Daula yai murmushi yace "wannan Yarinyar, yadda kanta yake lissafi naka bayayi, a hakan tayi min alƙawarin zata adana wasiyyata kamar yadda zata adana Ranta daza ta ganshi"
Haka sukayi ta bugun cikin Daula, wani abun ya gaya musu, wani abun ya waske shi duk a ganinsa an zama É—aya, har yake labarta musu ai matarsa namiji zata haifa.
Cikin Huda yana da watanni bakwai, ta dage tace ita seta koma Nigeria a can take son ta haihu, Daula ya kaÉ—a ya raya tace ita Nigeria takeson ta koma, yanzu zaman nan ya isheta.
Haka Daula ya tattara ya dawo Nigeria, dama akwai katafaren gidansa me girman gaske, inda suke sauka idan sunzo, akwai ma'aikata a gidan saboda girmansa, dukda babu kowa a gidan akwai megadin gidan Bala, Sojane shiyake kula da shuke shuke da sauran al'amauran gidan idan basa nan, gidane har gida katafaren gaske me matuƙar girma da yalwa.
Suka koma Nigeria suka sauka a wannan gidan, lokacin da cikin Huda ya shiga watanni takwas tafiya ta kama Nasir ta gaggawa, Huda haka nan taji bata son ya tafi, ta dinga masa Shagwaɓa harda kuka ita karya tafi.
Widad ganin Mamanta na kuka, hadda shagwaɓa yasa tace "da nice da yanzu Ammi kin koreni kince na fiye takura, shine kikewa Daddy kuka ko? Daddy ka ƙyale Ammi shagwaɓabiya"
Nasir yayi murmushi yace "my princess gayamata dai, kalli tana kuka kaman baby"
Widad suka haɗu ita da Babanta suka dinga tsokanar Huda suna dariya, akwai kyakkyawar fahimta da ƙaunar juna a tsakaninsu, haka yaita rarrashin Huda, harta haƙura ta ƙyaleshi ya tafi, ita dama tsoromta bata son ya tafi daga ita se Widad a gida ga tsohon ciki.
Kwana biyu da tafiyar Daula, cikin dare sun tsaka da bacci, Widad ta tashi ta shiga kiran "Ammi, Ammi ki tashi"
Cikin bacci Ammin Widad ta farka tace "lovely lafiya kuwa?"
"Ammi yunwa nakeji"
"Widad yunwa cikin daren nan kuma?"
Widad ta jinjina mata kai, Huda tace "Widad kin fiye rigima, ko tausayin halin da nake ciki bakya yi, tashi muje in haɗa miki"
Haka ta kama hannun Widad zuwa kitchen, ta haÉ—a mata Frisco ta samata madara ta bata, Widad ta zauna tana sha, yayin da Huda keta hamma saboda bacci.
Widad ta kalli Amminta tace "Ammina kije ki kwanta, idan na gama nima zanzo in kwanta"
Huda tace "kin tabatta bazaki min fitina ba?"
Widad tace "yes Ammi, i promise you i won't do anything bad"
Huda tace "Yawwa my lovely friend, barakallahu fik"
. Ta sunkuyo ta sumbaci goshin Widad, itama ta sumbaci goshin Amminta, har taje bakin ƙofar kitchen ɗin, Huda ta juyo ta kalli Widad ta ɗaga mata hannu, itama ta ɗaga mata, Huda tace "Babyna, ki zama me riƙon Alƙawari, sannan karki zama me manta alkhairi"
Widad tayi murmushi, ta jinjinawa Amminta kai.
Tafiyar Ammin ɗaki ba daɗewa, Widad taji kamar ana taɓa gate ɗin gidansu, ga Ƙaton karensu yanata zabga haushi, a zatonta ko Daddynta ne ya dawo a daren nan, dan haka ta taka kujera, ta hau kan drower ɗin kitchen, ta leƙa Window, da yake gurin a saman bene ne, hakan ya bata damar ganin abunda ke faruwa a ƙasa harabar gidan.
Ƙaton police dog ɗin nasu yake ta haushi yana zagaye, a harabar gidan, Bala soja ya kama karen ya maida shi ɗakinsa ya rufe, sannan yaje ya zare sakatar dake gate ɗin.
Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan, sun kai su biyar fuskarsu ɗauke da mask baƙi, baka gane fuskokin su, ga manyan bindugu a hannunsu.
Tunani Widad tayi, a irin fina finan da take kallo, idan akaga mutane da irin wannan shigar musamman cikin dare, to they are dangerous, tana nan akan drower taga Bala yayi musu jagora har ƙofar da zata sadaka da cikin gidan.
Ya buɗe musu ƙofar suka shiga, Widad ta sakko daga kan drower a hankali, ta leƙa ta ɗaya window, tana gani suka shigo babban falon ƙasan benen, suka shiga haurowa saman benen, komawa tayi ta ɓuya suka buɗe ƙofar ɗakin da Huda take ciki suka shiga.
Suna shiga Widad ta fito daga kitchen ɗin, tana tafiya a hankali tazo ta window dake corridor ta tsaya ta Leƙa window a hankali, cikin sanɗa take komai.
Tana gani ɗaya ya kunna fitila, haske ya gauraye ɗakin, Huda ta buɗe ido tana salati, nan da nan ɗayan ya janyo pillow ya danneta, ta dinga mutsu mutsu tana fizge fizge, Kasancewar ƙaramar rigar bacci ce a jikinta, kana iya ganin yadda cikin dake jikinta ya dunƙule guri ɗaya.
Widad tana tsaye tana kallonsu, ta toshe bakinta da hannunta, tana ta gumi jikinta yana tsuma, ƙafafunta se rawa suke, tun Huda na iya mutsu mutsu da ƙoƙarin ƙwacewa, ɗaya ya zaga ya hau kan gadon ya riƙe hannayenta, tun tana motsa ƙafafunta, har rai yayi halinsa ta dena motsi.
Widad na zuwa nan kawai ta rirriƙe Yusuf ta fashe da wani irin kuka me matuƙar ban tausayi, ba Widad ba shi kansa Yusuf seda jikinsa yai sanyi, labarin ya ratsashi sosai, tun daga rayuwar iyayenta zuwa kanta a cikin ƙaddara take, rungumeta Yusuf yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma ya kasa magana sam se Ajiyar zuciya.
Ganin Widad bata da niyyar sassauta kukan da take yasa Yusuf ya fara magana, cike da rauni da tausayawa yace "Am very sorry dear, ubangiji Allah jiƙansu gaba ɗaya, take heart Widad, Allah ya jiƙan Ammi"
"Yoseef, my Mum was killed before my eyes, a gaban idona aka kashemin ita, bayan an san bani da gata se Allah se ita da Daddy na, amma without fear, she was killed mercilessly, ga tsohon ciki, how can I forget this in my life, how?"
Jikinta har tsuma yake saboda kukan da take, ga wani irin numfashi da take jerawa, Yusuf yace " tabbas an cutar da ahlinku, cutarwa mafi muni Widad, amma kiyi haƙuri ki miƙa lamarinki ga Allah, dama Allah yayi a lokacin mahaifiyarki zata rasu, bawa baya wuce lokacinsa"
Widad tace "na sani, da Ammi mutuwar Allah tayi, bazan cigaba da damuwa tsawon wannan lokacin ba, nasan lokacinta ne yayi, amma aka kasheta da tsohon ciki laifin meta yi? Me tayi musu zasu kashemin ita Yoseef?" ta maganar muryarta na sarƙewa.
Seda Yusuf ya zubda hawayen tausayin Widad, ya shiga share mata hawayenta yana,  " kiyi haƙuri, mucigaba da yi musu Addu'a, kidena wannan kukan, Allah yayi mata rahama, take heart "
Shaƙuwa Widad ta dingayi, numfashinta yana sama yana ƙasa, gigicewa Yusuf yayi ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma bata iya magana hannunsa ya ɗora akan ƙirjinta ya shiga karanta mata duk abunda yazo bakinsa, na ayoyin alƙur'ani.
A hankali ta dinga sauke ajiyar zuciya, ta dena shaƙuwar, Yusuf yace mata sannu, jinjina masa kai kawai tayi.