← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 127

Sashe 85

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Musa yace "Haruna ina ka shiga ne? An kira layin ka ba adadi amma taƙi shiga, gashi baka bawa Bukar takaddar nan ba gashi za'a shiga kotu, kasan fa idan wani ya ɗau takaddar nan tsaf zamu shiga matsala, har saƙo aka turo maka na zamuyi taro amma baka ɗaga ba"

Alhaji Haruna yace  "bani da lafiya ne, banga saƙon ba"

Alhaji Musa yace "ban yadda ba, akwai wani abu a ƙasa, ka gayamin ko menene mana? Kasan halin Bukar wallahi ze iyayi maka Akuya kasani sarai"

Alhaji Haruna yace "a bar zancen kawai, zanzo in same ka zamuyi magana"

"Shikenan, seka zo amma kasan yarinyar nan ta gano Bukar kuwa"

"Ahh haba dai garin yaya kuma?"

"oho masa dai, wallahi tayi masa sheda da wuƙa, ta yanke shiba fuskarsa da cinyarsa, kai baka ga yadda ya sha ɗinki ba, gaba ɗaya halittun fuskarsa sun sauya"

Alhaji Haruna yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Taɓɗijan dara taci gida kenan, to wani mataki ya ɗauka"

Alhaji Musa yace  "eh to, yace tunda ga riga ta gano shi yasan yadda ze da ita, sedai kawai idan mun haɗu da kai tukuna, mayi magana mu tattauna maganar bazata yi ta waya ba, zan shiga meeting ne yanzu"

"Shikenan, sena zo tukuna"

Ramadan ne yai sallama ya shiga falon mahaifinsa, yana zaune yana kallon labarai, Ramadan yace "Daddy barka da hutawa"

Bulama yace "Yawwa barka, sannunka wai ni ina É—an uwanka Fahad ne, yaushe rabon da in sashi a idona"

Ramadan yace "Daddy kasan halinsa fa, wallahi yau kwanansa huÉ—u baya gidan nan, nima ban san inda yake ba, babu wanda yayiwa sallama, dama hana yin haka fa, yakan kwana biyu ma baya gidan nan"

Bulama yace "da kyau, ze gauraya dani kuwa, dan ubansa"

Ramadan yace "Yawwa Daddy, nace a wane Asibitin Widad take ne, Nurat ta aiko a gayamata imsa take, tana son ganin tane kasan ƙawarta ce"

Bulama yai shiru yana nazarim Ramadan sannan yace  "wata aiko?"

"Wani ne, nima ban sanshi ba, wai ko Khalil ne kowaye, ya cemin É—an uwanta ne shi, yana so zeyi magana da Widad ne, Nurat na son sanin halin da take ciki"

Bulama ya jinjina kai yace  "rabu dasu kawai"

"Daddy saboda me? Aikowa yasan tana hannunka, yakamata ka faɗi Asibitin da take, saboda masu dubiya sannan wataƙila 'yan sanda zasu samu wani rahoton daga gareta"

"Kai Ramadan ka kiyaayeni, ka fiye shisshigin tsiya wallahi, to ban saniba tunda nace maka tana Asibiti amma kama cigaba damin tambaya"

"Allah ya baka haƙuri, amma Daddy wannan yakan fa dake fuskarka da ƙafarka? Tun shekaranjiya nake son in tambayeka amma se inga kana bacci, na tambayi Mummy tace itama bata sani ba"

Bulama yace "Accident ne na samu, tashi ka bani guri tafi maza ka bani guri in huta"

Haka ya fatattaki Ramadan, ya kulle ƙofarsa ya ɗakko wayarsa ya kira Alhaji Musa, ya ɗaga yace  "Allah ya temaki Bukar Bulama"

Alhaji Bulama yace "Musa kasan da ana shirin samun ɓaraka daga gidanka kuwa?"

"kamar yaya kenan?"

Bulama yace  "Waye Khalil a family ɗinka kona matarka?"

Alhaji Musa yace  "ɗan yayar Babar Nurat ne, cousins ne shida ita"

"Shine ta turoshi gidana wai azo agane mata ya Widad take? Wai aga halin da take ciki, da sanin ka akayi haka?"

Alhaji Musa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wallahi ban sani ba saboda haka fa na kirsheta a gida, ko nan da cam bata zuwa, na hanata zuwa ko ina Sam, ban san yadda akayi tayi hakan ba, amma ka ƙyaleta zanyi maganin ta, zan ƙwace wayoyinta sannan in turata ƙasar waje, bakomai zan ɗau mataki a kai, hakan bazata sake faruwa ba"

"gara dai kayiwa tufkar hanci tun kafin inyi abunda yakamata da kaina, karka ƙara turomin wani yazo yana neman Widad, ka jawa 'yarka kunne"

"Insha Allah, hakan bazata sake faruwa ba, zanyi abunda ya dace base ka É—au mataki da kanka ba"

Bulama yace "da dai yafi"

Litinin, tushen aiki kotu ta cika maƙil, domin ji da ganin yadda shari'a zata kaya, musamman shari'ar da mutane suke cike da sonji da ganin yadda zata kaya, wato shari'ar Yusuf Bashir Maitama, ɗaga jajirtaccen ɗansanda wato Bashir Maitama.

Umma ya halarci zaman kotun nan, dan shine kaÉ—ai hanyar da zata ga ÆŠanta Yusuf, 'ya' yan Bulama su Alhaji Munir, da Hajiya Halima da 'ya' yanta duk sun halarra a kotun.

Umma tana nan zune tana waige waige aka shigo da Yusuf, hannunsa ɗauke da sarƙa, 'yan sanda sun taso shi a gaba, yadda yake jan ƙafa da ƙyara da yadda jaabiyarsa tai baƙiƙirin saboda datti, ga fuskarsa duk a kumbure, kai da gani base an faɗa ba kasan Yusuf a wahala yake, Umma ta ƙunshe fuskarta a mayafinta ta fashe da kuka.

Haka akaje aka tsayar da Yusuf, 'yan sanda suka kewaye inda yake, Yusuf ya ɗaga kai yaga yadda kotu ta cika maƙil, masu masa kallon banza nayu, masu na tausayi suna yi, idonsa ya sauka akan ummansa wadda idonta yayi fururu saboda kuka, ya sunkuyar da kansa yana danne hawayen dake shirin zubo masa Allah kaɗai yasan me Umma takeji a rantava yanzu haka.

Aka karantowa Yusuf ƙunshin tuhumar da ake masa, amma Yusuf ya musanta yace "shi bashi ya sace Widad ba"

Barrister Saminu ya miƙe, ya gabatar da kansa a matsayin lawyoyin gwamnati masu gabatar da ƙara sannan yace "duba da yadda wanda ake zargi ya musanta abunda ake tubumarsa dashi, muna neman wannan kotu me Alfarma data bamu dama muje mu tattara hujjojinmu da zamu gabatar a gabanta, wanda zs tabattar da abunda ake zargin wanda ake ƙara ya aikata"

Me shari'a Justice Abdallah A dutse yace "duba da yadda lawayan gwamnati ya nemi a basu dama domin kawo shedunsu, wannan kotu ta ɗage sauraran wannan ƙara zuwa goma ga wata me kamawa, sannan wannan kotu tayi umarni da akai wanda ake zargi gidan gyaran hali zuwa lokacin da za'a sake wannan zama"

Haka aka tashi a shria'r yau, aka taho da Yusuf za'a sashi a motar 'yan sanda,' yan jarida sukayi dandazo amma aka hansu magana da shi, Umma ta taho da gudu Suleiman ma cikin hanzari ya nufi inda su Yusuf suke, Umma tana kuka tana "dan Allah ku barni in ganshi ko sau É—ayane, É—ana ne watana kusan biyar rabona dashi, ganinsa kawai zanyi Suleiman dan Allah kace su bari in ganshi"

Suleiman yace "Dan girman Allah ku bar baiwar Allah nan taga É—anta, ko sau É—ayane uwace kunsan ba zata iya jurewa ba, dan Allah ku bari ta ganshi"

"Ba a bamu wannan damar ba, seta bari idan mun kaishi prison taje can idan sun batta seta ganshi"

Ayshercool
07063065680
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

130_131

Haka aka ja mota aka tafi da Yusuf, umma tana ta zabga kuka, Yusuf ma ya sunkuyar da kansa yana kuka a cikin motar nan, shiba kaishi gidan yarin bane damuwarsa, kukan da Ummansa take shine ya tsaya masa a ransa.

Dan abun takaici, 'yan jarida sukazo suka kangawa Umman Abubuwan magana sun antaya mata tambayoyi, Suleiman ya janyeta suka hau mota suka tafi, ba tare da tace uffan ba, amma a haka suka naÉ—i muryarta tana kuka tana ambaton Allah dan suji daÉ—in yayatawa a duniya.

Haka aka watse a zaman kotu, kowa da abunda yake faÉ—a, wasu su faÉ—i alkhairi wasu kuma su faÉ—i som zuciyarsu.

Aka wuce da Yusuf gidan gyaran hali, aka bashi kayan fursunoni, aka shigar da bayanan sa, sannan aka kaishi É—akin daze zauna, mutane masu laifi sunyi su sittin a É—aki É—aya, ga rashin isashshen vantilation, ga cunkoso ga tsamin dauÉ—a da wasu suke yi, gaba É—aya abun se godiyar Allah haka akaje aka gwamutsa Yusuf a cikinsu.

Bayan an tashi daga zaman kotune, Bulama yabi Justice Abdullah gidansa, aka masa iso ya shiga, yana ganinsa A dutse ya faɗaɗa murmushinsa yace  "kaine da kanka haka baa aike ba?"

Bulama yace  "Ai saƙonne, yafi da cewa in isar dashi da kaine ba aike ba"

"to barka sa zuwa, ya kaga zaman shari'ar tamu na yau?"

"To Aini dutse banyi zaton haka ba, muda muke da shedu tuni mun tanada, na gaskiya dana boge amma kace wai ka ɗage sauraren ƙarara, ina laifin a fara gabatar da shedun, nifa da wuri nake son ayita ta ƙare fa, ayi a yanke masa hukunci in rufe babainsa, saboda in dai yana nan ze hanani rawar gaban hantsi, dan gaba ɗayansa matsalane a gare ni wallahi "

A dutse yayi murmushi sannan yace " hmmm Bukar Bulama, ai ita shari'a saɓanin hankkalice, bar ganin ka saye ni ka saye lawyoyi da hukunar 'yan sanda, karka manta akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu, na kare haƙƙin ɗan Adam, akwai lawyoyi masu zaman kansu, dukda wasu abubuwa da akayi da suke fito da laifin shi yaron ƙarara, amma duk da haka zasu saka ido akan shari'ar, za' a samu wanda zasu bibiyi shari'ar, dan haka muje a sannu, ina sane nayi hakan komai a sannu akeyinsa cikin hikima da ƙwarewa irin ta aiki "

Bulama yace " Aini gaba ɗaya hankalina baze kwanta ba muddin ba a gama shari'ar nan ba, yaron nan fa ba ƙaramin bincike yayi akaina ba, kuma bana son Daula ya bayyana ba'a gama shari'ar nan ba"

"Calm down mana, waini haryanzu babu labarinsa, babu wanda yasan inda yake ne? Abunfa da mamaki"

"to waye ya sani, anneme shi am rasa kamar wani kuɗi, duk iya bincike na saka anyi amma babu labarinsa, ni dai kayi kayi ayi gaggawa a ƙarƙarw shari'ar nan da wuri, ka yanke masa hukunci, kuma hukunima me tsanani wanda ze ƙare a prison"
Chapter 85 · 0% Book details