← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 127

Sashe 38

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daula yace "ni lafiyar 'yata ƙalau, babu abunda ya samu Ƙwaƙwalwarta a wancan lokacin, Allah dai ya bata kaifin basira fiye da shekarunta" yana gama maganar ya miƙe, ya saɓa Widad a kafaɗarsa ya tafi ɗakinsa da ita, yaje ya kwantar da ita, ya koma gefenta ya kwanta ya ƙura mata ido yana jin tausayinta na ratsashi, Widad ta rasa mahaifiya da ƙananan shekaru, yasan rayuwar maraici, yasan yadda take, musamman ga 'ya mace tafi shan wahala, take hawaye suka shiga zarya a fuskarsa yace  "insha Allah zanyi iyayina, ba zakiyi kukan maraici ba Widad"

Wasa wasa tunda aka yiwa Widad Allurar nan bata sake farkawa ba, haka ta dinga wannan baccin kamar wata matacciya, abun ya É—agawa Daula hankali sosai, Amma likita yace masa bakomai samun relief É—inta kenan.

Seda Widad tayi kwana biyu cir tana wannan baccin, ko motsi ba tayi rana ta biyu da yamma sannan ta farka, tunda ta fara baccin nan Daula baya matsawa ko nan da can, yana kusa da ita, har Allah yasa ta farka.

Koda ta farka ta farka da wata irin matsananciyar yunwa, amma ta kasa cewa tana jin yunwa, maganar duniya Daula yayi amma taƙi bashi amsa, sedai ta bishi da ido.

Ya haɗo Abinci yazo ya zauna yana bata, tana ci tana kallonsa kamar taga sabon abu a tare da shi, yana cikin cin aka zo aka sanar dashi yayi baƙi yace ayi musu iso nan inda yake baze iya tashi ya bar Widad ba.

Aka musu iso suka shiga har inda Daula yake, sedai Widad na ganinsu se taga kamar wannan mutanen da suka kashe Amminta, seta dinga ganinsu da wannan mask ɗin a fuskarsu, abunda ya faru da Amminta ya shiga dawo mata fes a idonta, taga kamar a lokacin abun ke shirin faruwa, aikuwa ta kurma ihu me razanarwa, haka yasa mutanen suka tsaya suna zuba mata ido, ta riƙe Daula gam tana ihu, ta rintse idanunta alamar bata son ganin kowa gaba ɗaya.

Ƙarshe mutanen nan se barin ɗakin nan sukayi gaba ɗaya, suka koma babban falo suka jira shi, abu kamar wasa sosai Widad take gudun mutane bata son kowa a inda take inba Daddynta ko Bulama ba.

Watarana tana zaune a É—akin Daddynta, tana wasa da magen Amminta data bari, Alhaji Daula yana son ya É—an fita, amma yana tunanin yadda zeyi da Widad.

Widad da a rana bata fi tayi magana sau a ƙirga ba amma tace  "Daddy kaje inda kake son zuwa, ba inda zani"

"A'a lovely, ina tsoron barinki anan ke kaɗai, abubuwa sun fara bani tsoro, ina zaton zan sa a ƙara security"

Widad tace  "Daddy har yanzu Bala be magana ba?"

"Eh lovely, Amma a binciken 'yan sanda, security na kan babban titi sunga wucewar mota tsakar darw ta shigo hanyarmu, sedai wai sunyi zaton gurina ko wani suka zo, saboda kin san mukanyi meeting cikin dare, amma har yanzu anata bincike"

Widad ta jinjina kai tace  "Daddy kaje kawai, ina nan ba inda zani"

"Babyna ina tsoron barinki, kinga baki da lafiya"

"Lafiyata ƙalau fa"

"ko kuma mu tafi tare da ke?"

"A'a Bazani ba, ka tafi kawai"

Daula yace  "nayi murna daughter, yau kina magana sosai da kanki".
Tayi murmushi, Daula ya shirya ya fita.

Bayan fitarsa Widad ta fito ta dinga zagaye gidan, kamar bata saba ganin gidan ba.

Kamar gaske ta fara dawowa daidai, amma dukda haka bata son mutane sam, daga Daddynta bata son kowa ya raɓeta, balle a yimata wani abun, haka Daula yake yawo da ita gurin taro ko harkokin kasuwanci, kamar yadda uwa ke yawo da ɗanta, sam ko makaranta bata zuwa saboda rashin son mutane, indai ba'a gida ba ko tana tare da Daddynta bata zama a ko ina.

Daula Shine wankanta, Abincinta, da dukkan buƙatunta, sam baya gazawa.

Wataran zeje taron kasuwanci Africa ta kudu, nanma ya ɗauki Widad ya tafi da ita, ranar da suka dawo kusan ƙarfe ɗaya na dare, direbansa yaje ya ɗakkosu daga airport suna tafe suna hira, kawai aka tare motar tasu.

Widad na ganin mutanen da suka taresu ta gigice, yanayin jikinsu sak wanda suka kashe Ammi, gasu da mask a fuskarsu.

"Kai buÉ—e motar nan"! ÆŠayan yayiwa direban Daddy tsawo

Widad ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba, tabbas sune wanda sukaje har gida suka danne Umminta da pillow, nan da nan jikin Widad ya ɗau rawa, amma ta dake taƙi nuna alamar Hakan.

Suka bubbuɗe murfin motar, Daula ya rungume Widad a jikinsa yana ta nanata Hasbunalahi wani'imal wakil, suka fizgo direban Daula ƙasa suka saita masa bindiga.

Ɗaya daga cikinsu Wanda Widad bazata manta dashi ba, shine wanda taji yana wayar nan ranar da suka kasje mahaifiyarta, har ya ambaci sunan wani mutum, ya kalli Daula yace  "Nasiru Daula, haƙiƙa ina me tabattar maka da zaka bi matarka inda ta tafi idan har ka mana gardama, tambaya ɗaya zan maka kuma amsa nake so ta kai tsaye, ina wannan takaddun da wasiyyar da kayi na cewar akwai wanda yake da kashi bakwai bisa goma na dukiyarka suna ina?"

Daula ya kalleshi cikin mamaki yace
" dama dalilin da yasa kuka taremu kenan? toni babu wannan kayan a hannuna, kamar yadda nayi bayani lokacin da nayi hira da 'yan jarida"

Cikin tsawa yace " kai, karka min wata taƙama da jin kai, babu wani amfani da taurin kai ko tsaurinka ze maka a nan, zan iya fasa maka kaibda harsashen nan"

ÆŠauke Daula yayi, yai musu shiru.

"Ina takaddun nan suke?!" sukai masa magana cikin tsawa.

Ko gezau beba balle susa ran ze basu amsa, yunƙurwa sukayi zasu danƙo Daula daga cikin motar, Amma Widad ta buɗe hannayenta ta tare mahaifinta.

Daula yace "lovely, ki bari kar suyi miki wani abun kinji, karsu illatamin ke"

"Am not afraid of anyone, abunda suke nema yana gurina, karsu ƙara yi maka tsawa"

Kallonta suka shigayi, dudu ba zata fi shekaru takwas ba, amma kalli yadda take magana kamar ba yarinya ba.

Hannu babban cikinsu ya saka ze fizgo Widad, amma Daula ya riƙita gam suna janta, shi kuma ya riƙeta gam.

"Idan baka saketa ba zamu fasa kanta da harsashi!"

Daula yace  "idan kuka kasheta kun kasheni, kuma kun rasa abunda kuke nema, kuma koda kun barmu a raye shima duk ɗaya zaku rasa abunda kuke nema, dan wallahi kome zakuyi da kaina bazan baku amana ba, bazan baku kayan da ba nawa ba, sedai idan Widad ɗince ta yarda ta baku bani da matsala da duk wanda ta ɗauka ta bawa"

Zuro hannu ya kuma yi ze danƙo Widad, sedai a wannan karon bisa sa'a, Widad ta nuna musu ita mahaukaciya ce, dan kukan kura tayi ta datse yatsan mutumin nan a bakinta, ta kafa masa haƙora kamar yadda ta yiwa Fahad.

Abun mamaki sega Ƙaton da yake ɗauke da bindiga yana kurma ihu, yasa kan bindiga ya daki kan Widad, wanda hakan yasa ta ƙwala ihu ta sake shi, sega jini na zuba ta hancinta ta sume a gurin, ganin Asirinsu na ƙoƙarin tonuwa yasa suka cika wandunansu da iska suka ɓace daga gurin.

Daula gaba ɗaya ya rikice, ƙarshe direban ne yayi dabarar wucewa dasu Asibiti, aka kai Widad emergency gaba ɗaya Daula ya rasa abunda yake masa daɗi, matsala daga wannan se wancan be maganin wannan ba waccan ta kunno kai.

Yai shiru ya dafe kansa ya zubawa Widad ido, wadda ke kwance ruwa na shiga jikinta, ya kifa kai akan gadon da take yai kuka yai kuka, harya gaji yayi shiru, cikin dare Widad ta farka tayi juyi taji kanta yayi mata nauyi, ta juya taga mahaifinta ya kifa kansa a kan gadonta, ya riƙe hannayenta, da alamu yana cikin matsananciyar damuwa, a hankali tayi juyi ta rungumo kan Daddynta ta kwantar da kanta a kan nasa, a haka bacci ya ɗauketa.

Wayewar gari labari ya cika gari, ga abunda ya sami Daula da 'yarsa nanma akayi ta tururwar zuwa Asibiti dubata.

Daula ya tafi masallaci salla sega wasu mutane sun shigo ɗakin nata, wai sunzo dubata, ta dinga binsu da kallo, suka zazzauna, kallo ɗaya ta gane wanda ya buga mata bindiga jiya, wanda suka kashe Amminta ne, bata taɓa ganin fuskarsa ba se yau, bata ƙara tabattarwa ba seda ta kalli inda ta gasa masa cizo jiya, a hankali yace

  "ina baban naki?"

Shiru tayi ba tace masa komai ba, yazo gaban gadonta ya durƙusa sannan kalleta yace  "Baby girl, tambayarki zanyi kinji ko? Ina abubuwan da Dad ɗinki ya baki ajiya, su nake son ki gayamin inda suke kinji, nima bazan gayawa kowa ba"

Widad ta tsare shi da manya manyan idanunta tana masa wani irin kallo, daya kasa gane na menene?

"Baby ki gayamin kinji"

Still ba amsa, ya ɗakko wata ƙaramar wuƙa yace "idan baki gayamin ba, zan gutsutsura naman jikinki da wuƙar nan, in dafa in cinye, gayamin nace"

Yai maganar yana zare mata ido.

Ya ɗauka Widad irin yaran dazewa barazana ne, amsar data bashi shine  "idan ka kasheni bakomai, nasan dai Daddy zeyi kuka, amma nasan wanda ya kashemin Ammina" tai maganar tana kallonsa

A fusace yace "ina ruwana da wanda ya kashe ta? Kema kashe ki zanyi in kashe babanki idan baki faÉ—an ba"

Maimakon ta bashi amsa, se tace "Na rubutawa DSP wasiƙa, zan gayamasa wanda ya kashe Ammina, yayimin Alƙawarin ze gano suwaye"

"Ke dan ubanki ba wannan muke tambayarki ba, ina kayan nan suke?"

Widad bata nuna ta ganesu ba, ta sake kallon hannunsa tabbas shine babu ko tantama, ga inda ta cijeshi jiya a tsintsiyar hannu, abun da ya faru ranar da aka yi kisan ya sake dawo mata ranta, gani tayi ya miƙe ya ɗakko handkerchief a aljihunsa ze saka mata a hanci, nan experience ɗinta na kallace kallacen films ya dawo mata, bata san ya akayi ba ta fasa ihu, ta ɗakko kwalbar malt zata buga masa, ai kafin tayi wani yunƙuri, sun bar ɗakin nata da sauri, nan ta cigaba da kurma ihu tana jifa da kwalabe a ɗakin.

Da gudu Daula dasu Bulama, da ɗan sandan Da Widad ta saka ya kama Bala, suka ƙaraso ɗakin, dama suna kan hanyar zuwa ɗakinne, Daula yayiwa ɗansandan waya, yayi masa bayani, shine ya taho Asibitin.
Chapter 38 · 0% Book details