← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 127

Sashe 118

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗanyi shiru sannan ta kalli Yusuf, daya zuba mata ido tace "inda Bulama ya kaini ya ɓoye, akwai wata mata da take kula dani a gidan, wayarta nake karɓa inyi browsing inga yadda shari'arka ke gudana, katsam ta bar wayar a hannuna, ta tafi aikace aikacenta, ni kuma nayi recording a wayar, na cire memory card ɗin bata sani ba, na bata wayarta, na rubuta takadda na bata na nannaɗe memory card ɗin a leda, a cikin takadda, nace ta aramin dubu ɗaya taje ta samu shagon masu saida abubuwa ta basu, na bata ina addu'a Allah yasa saƙona yaje inda na tura shi.
Nayi rubutu ne, nace 'zuwa ga wannan takaddar taje gareshi, dan Allah ina neman Alfarma, ina son duk yadda za' ayi ledar dana aiko da ita, da abunda ke cikin ledar, a kaiwa Barrister Hafiz Mubi, ace masa inji Widad, sannan a karɓi dubu ɗayan hannun matar a bawa wanda ze kai yayi kuɗin mota, itakuma ace maya babu abunda na aikota ta saimin.
Shine aka karɓi saƙon, akace mata babu aiken da na mata, ta dawo ba tare da tasan mena aiketa ba.
Barrister Hafiz, ɗahane daga cikin lawyoyin Daddy, saƙon ya isheshi ya duba, shima na rubuta masa wasiƙa, nace ya duba cikin memory card ɗin, akwai saƙo ya duba.
A cikin audio na gaya masa yadda ze saida wasu daga kadarorina, ya ɗaukar maka lawyer, Kasancewarsa abokin Khalil ɗan uwan Nurat, a nan ya samu dama shima suka haɗu da wasu lawyoyin aka tsaya maka a shari'ar, badan kuɗin da na saki ba, da har yanzu ba'a ƙare shari'ar a haka ba, da kotu bazata wanke ka ba, harse an kammala shari'a dasu Bulama, sedai a bada belinka, amma daka motsa sekace Nurat ta maka halacci, kaje ka ƙarat kai da ita, kaje ka Auri Nurat"
Ta ƙarasa maganar tana kuka, ta tashi zata tafi, Yusuf ya riƙeta gam ya zuba mata idanunsa, taƙi kallonsa ta cigaba da kukanta, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa.

"Kinji nace miki zan auri Nurat ne?"

"Idan ma baka faÉ—a ba alamu sun nuna ai"

"kina so in saɓawa Umma, dukda tarin alkhairinta a gareni saboda ke? Idan nayi haka na kyauta? Kina ganin raguwar auren namu zata yi albarka ne?"

Widad ta girgiza kai alamar a'a.

Yusuf yace  "ki bani lokaci, ina son in daidiata komai ne, amma sekin dena wannan koke koken, da tayarmin da hankalin sonake mubi komai a sannu, kinga ni duk ban san wannan ba se yanzu da kika gayamin, kiyi haƙuri kinji"

Ta zumɓura baki taƙi magana, hawaye na cigaba da fita daga idonta.

"bazaki dena kukan bane?"

"Nika ƙyaleni inyi dan haushinka nake ji" tai maganar tana basarwa

Yusuf yace "to shikenan, bari in tashi in tafi"

Sauri tayi ta riƙe shi tace  "wallahi ka tafi sena bika"

"to goge hawayen nan maza"

Bata goge hawayen ba, ta kwanta a jikinsa tana sake tura baki gaba, kamar yarinya ƙarama.

Ya shafa gashin kanta yace  "dama haka kike sona? Bani da bakin yi miki godiya, nagode sosai Babyna, Allah ya bani abunda zan mayar miki da kadarorinki bazan so ace kin rasa wani abu da kika mallaka saboda ni ba"

Widad tace "Dukiya É—azu ce, ni kai ne a gabana Yoseef, bana kallon dukiya ni kai nake kallo kawai, zuciyata kai kawai take kallo, ni kai nake so fa, ni banyi dan ka biyani ba, ni tukucin zuciyarka nakeso kawai"

Tai maganar tana sake kwanciya a jikinsa tana kuka.

Ya rungumeta sosai a jikinsa yace "is ok my love, ki dena kuka na fahimce ki, in dai zuciyata ce kin samu I love you my wife"

Tace "I love you too Yoseef"

Ta maƙalƙaleshi tana lumshe ido, tana shaƙar ƙamshin turarensa daya kashe mata jiki sosai.

Yusuf ya shafa gashin kanta yace "kinyi kyau sosai masoyiyata, kamar in sace ki in gudu haka nakeji"

Widad tace "dan Allah mijina ka fahimtar da Umma, mu samu ta yadda mu rayu tare, Yoseef na yadda in rasa komai nawa in kasance da kai har abada, you are my world and happiness Yoseef"

Yusuf kasa magana yayi, se ajiyar zuciya da yake tayi, saboda yadda jikinsa ya mutu gaba É—aya, ya dinga sauke ajiyar zuciya, can yace "My love ya babyna yake? Fatan baya wahalar min dake dai?"

Ta tura baki tace "gaskiya yana bani wahala, yaita kicking cikina, ko ya hanani cin Abinci"

"ki kwantar da hankalinki, lokacine ze dena insha Allah, zan masa faÉ—a ya dena wahalar min da babyna, ke dashi duk ina sonku sosai"

Widad ta tashi daga jikin Yusuf, ta kalli cikinta tana murmushi tace "kaji dai Abunda Dad É—inka yace ko? Ka dena takuramin"

Yusuf ya ƙura mata ido sosai, ta ɗago ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Wannan kallon fa? Ga fruit can a dining tashi muje ka bani abaki, nima in baka"

Yusuf ya girgiza mata kai alamar a'a, tace masa "why?"

Yace "that's not what I want"

'So what do you want? " tai maganar tana kallonsa.

" I want to kiss you, lips É—inki sunyi kyau sosai da kika sa jambaki "

Murmushi kawai tayi ta ɗauke kai daga kallonsa, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa dai dai tata yana mata wani irin kallo me wuyar fassara, a hankali yake mata numfashi a fuska, Widad kamar an sassaƙata ta kasa ko motsi daga inda take zaune, tana jin saukar numfashinsa a fuskar ta.

Rungumeta yayi yana kissing ɗinta, to show her how he misses her, and she responds to his message to show him that she also miss him, wayar Yusuf data fara ringing ce ta dakatar dashi daga abunda yake yunƙurin yi.

Sunan Umma ya gani akan screen É—insa, yaiwa Widad alama da tayi shiru, ya daidaita nutsuwar sa ya É—aga wayar yace "hello Umman Yusuf"

Umma tace "kuna inane?"

"muna gidansu Nurat ne"

"bata wayar mu gaisa"

"Umma ai ta koma cikin gida, kin ganni a harabar gidansu, yanzu zamu taho da Yallaɓai"

Umma tace "to shikenan, ka hanzarta ka dawo, bana son ka dinga nisa sosai"

Yusuf yace "to Umma, Insha Allah gani nan dawowa"

Ya kashe wayar yasa a aljihunsa, ya kalli Widad dake kwance, ta ɗauke daga kallonsa yace "sweetheart am sorry, kiyi haƙuri zan tafi kar Umma ta gane nazo gurinki kinji"

Bata ce masa komai ba se binsa da kallo da tayi, ya saita nutsuwarsa ya miƙe ze fita, ya waigo ya kalleta yaga tana hawaye, ya dawo ya durƙusa ya riƙe hannayenta yace "kiyi haƙuri matata, Insha Allah na kusa dawowa gareki kinji, karki damu dan Allah kidena kukan nan haka, nafi ki buƙatar ganinki a kusa dani"

Ya share mata hawayen fuskarta, ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan ya bar falon cikin hanzari.

Suleiman na ganinsa yace "kai haka mukayi da kai, daga zuwa ka ganta seka shige kayi zamanka kana soyayya ka shanyani, har Umma ta kirani a waya, na mata ƙarya ai muna tare a gidansu Nurat"

Yusuf yace "muje kawai, nima ta kirani karta gane naje gurin Widad"

Sulaiman yace "shikenan muje"

Tunda suka tafi Yusuf hankalinsa baya jikinsa, ya baro shi can a tare da matarsa, gashi yayi mamakin jin itace tayi me yuwuwa, da dukiyarta dan ganin shiya kuɓuta daga halin daya shiga.

Tunani kawai yake yi, Suleiman ya fuskanci hakan, dan haka yaita masa nasiha yana kwantar masa da hankali, amma sam Yusuf baya gane me Suleiman ke cewa.

A waje Suleiman ya ajiye Yusuf, shi kuma ya tafi, Yusuf ya shiga cikin gidan.

Ya shiga tare da sallama, Umma ta amsa masa tace "Yusuf kun daÉ—e fa, ya jikin Nuratun"?

Yusuf yace "da sauƙi, suna gaisheki?"

Umma tace "to Allah ya ƙara afuwa, amma ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?"

"A'a Umma, bakomai fa"

Umma tace "shikenan, ana daf da shiga sallar magariba, kai alwala ka tafi masallaci"

Yusuf yace "to Umma"

Ya shiga É—akinsa, cike da tunani fal a zuciyarsa.

Dan kar Umma ta gane yana cikin damuwa, yasa yaje ya É—auki Abincin dare yaci, Umma nata masa hira amma baya ganewa, se amsa mata yake da ummmm.

Ya tashi ya tafi ɗakinsa, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗakko waya ya kira Widad, sedai muryarta ƙasa ƙasa kamar bata da lafiya.

Yusuf yace "lafiya kuwa wife?"

"bakomai" ta bashi amsa

"Kiranki nayi muyi hira, kuma naji kamar ba lafiya"

"hirar da zata fi kowacce a gurina, itace ganinka a kusa dani, amma kamin nisa, ina ji ina gani ba yadda na iya, dukda son da nake maka"

Nan Yusuf ya kwantar da murya ya shiga aikin rarrashi, harta saki jikinta dashi, ta dena fushin suka koma soyayya, yauma seda suka sha soyayyar su, seda dare yayi sosai sannan suka kwanta bacci cike da begen junansu.

Umma tana monitoring ɗin Yusuf, ya dena zaman tsakar gida ko kuma hira da ita, kullum yana ɗaki riƙe da waya, da tayi zancen Nurat seya dinga basarwa, saboda haka ta zuba masa ido, sedai ta toshe duk wata hanya daze fita yaje yaga Widad, dan bata son ya kuma raɓar Widad yaja musu matsala.

Sosai fa Suke kewar juna shida matarsa, gashi baze iya bijirewa Umma ba, yana matuƙar tausayin Widad sosai, dan yadda suka yi waya yau ya gane bata da lafiya tana jin jiki sosai, ga babu hanyar fita, dan idan harze fita se Umma ta tambayi ina zashi.

Da Yamma Umma ta hanshi zaune yayi jugum, yayi shiru kamar wanda akayiwa mutuwa.

Ta kalle shi tace "Yusuf zo kaje ka siyo kayan miya, zanyi girki naga yamma tayi"

Yace "to"

Ta bashi kuɗi ta lissafa masa abunda ze siyo mata, sannan ta bashi dubu biyu tace "ga wannan ka riƙe a hannunka, kafin ka koma gurin aikin"

Yusuf ya karɓa yace ya gode, ya fita yin cefanen.

Umma tana ta aikinta a tsakar gida, taji anyi sallama, ta amsa tare da waigowa wanda ta gani ne yasata sakin tsintsiyar hannuta ta saki baki, tana kallonsa..

AMANA! AMANA!! AMANACE!!!

IDAN KIKA FITAR BADA IZININA BA, ALLAH YANA KALLONKI, KUMA KINCI AMANA
Chapter 118 · 0% Book details