← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 127

Sashe 63

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Iyeee, kai kodai baka da lafiya ne? Idan bahaka ba, amma kace baka so in ƙyaleka, idan baka da lafiya ne ka gayamin in san abunyi, amma ta yaya za ka ce baka son Aure?"

Ya gane inda Umman ta dosa amma yace  "Umma wane irin rashin lafiya, niba zazzaɓi ba ba wani ciwo ba, kina ganina rasam danu, kawai ni matan ne se a hankali, bana son wadda zata zo ta damemu"

"Ai ina maka addu'a, kuma nasan Allah ya amsa, Insha Allah mace tagari zaka samo mana, amma dai gaskiya anemomin sirika, ko kuma ni in nemo"

Yusuf ya miƙe tsam yace   "Hajiya Umma kenan, me abun mamaki Allah ya ƙaro mana Arziki in biyamiki Makka, ni nayi nan seda safe"

"Au zancen ne baka so shine ka gudu ko? Zakazo ka sameni kuwa dan ƙaniyar ka, jikoki nake son gani, na ƙagu ka ƙara gaba yara nake son gani "

Yusuf yayi waje yana dariya yace "Hajiya Umma, tawa ta kaina.

Yusuf ya cigaba da aikin sa, da neman kuÉ—insa.

Wataran ya dawo a babur É—insa, ze wuce gida yaji ance " Sannu da zuwa "

Ya waiga yaga wata matashiyar budurwa ce, shi dai yasan yana ganinta a nan unguwarsu, amma besan daga inda take ba, kuma ba abunda yake haÉ—ashi da ita, dan haka be kawo dashi take ba yai gaba abunsa.

Aikuwa yaji haushin ƙin kulatan da yayi, haka ta wuce ta tafi nata Aiken.

Da safe ya fito ze sai bredi, suka kuma haÉ—uwa da ita, tace masa ina kwana, ya waiga ya kuma kallonta tace "nace ina kwana"

Yusuf yace "lafiya ƙalau" daga nan yai gaba.

Ya zamana kusan kullum in dai ze fita kokuma ya dawo seya ganta, kuma seta kula shi, shi harta fara bashi haushi ma.

Wataran Asmar Umma ta tashi ga zazzafan zazzabi, Yusuf ya kaita Asibiti aka rubuto mata ruwa da allurai, aka sama ta wasu a can ya taho da sauran gida.

Da daddare za'ayi mata allura, yaje chemist É—in bakin titi, yaje ya gayawa me chemist É—in ko zezo yayi mata allurar a gida seya biya shi

Me chemist yace "karka damu, kaje zan turo ƙanwata tayi mata"

Yusuf yace "tasan gidan ne?"

Yace "eh ta sani, zata zo insha Allah"

Yusuf ya koma gida yana jira, yai girki ya tattara kwanukan yana wankewa, tayi sallama, ya miƙe kalleta aikuwa ya haɗe rai yace "ke lafiya?"

Taya fari da ido tace "ba gurinka nazo ba kake wani haÉ—emin rai, ina mara lafiyar tamu?"

Yusuf ya harareta yace "wace mara lafiyar? Malama ƙara gaba ba nan bane"

"Kamar yaya, Yaya Sani ya cemin inzo zan mata allura fa"

"Wai dama kece?"

"Eh nice, ina Umman tawa take?"

Yusuf a ransa yace "ji wani iyayi, wai Ummanta ummana dai ni kaÉ—ai"

Yai mata jagora gurin Ummansa, Yadda ta dinga lallaɓa Umman ne, yaji daɗi Sosai, bayan ta gama yace 'nawa ne? "

Ta Harare shi tace "in mutum yayiwa mamansa abu seya biya? Ummana Allah ya ƙara sauƙi"

Umma tayi murmushi tace "nagode sosai' yata, Allah yasaka da alkhairi"

Yusuf ya tsaya sororo yana kallonta tace "kaje ka cigaba da wanke wankenka mana, Umma seda Safe Allah ya ƙara sauƙi, likita ya rubuta a samiki ruwa, safe da yamma na kwana biyu, zanzo in samiki insha Allah"

Umma tace "to shikenan nagode Allah yayi albarka, amma baki gayamasa nawane kuÉ—in ba ya biya"

Yarinyar tace "Abunda ze biya shine, yaje ya ƙarasa wanke wankensa, yai miki shara ya siyo miki duk abunda kike so kici, kiji ƙwarin jikin ki"

Umma tace "to shikenan kana dai ji ko?"

Yusuf kawai ya sosa kai, Yarinyar tace "dan Allah ka fitar dani bakin hanyar nan taku, lungunku da duhu ina jin tsoro"

Umma tace "Yusuf raka ta mana"

Ya kalli Umma ya kalli yarinyar, ta kashe masa ido É—aya tayi gaba.....

LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUÆŠI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ÆŠAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel É—ina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

104_105

Yusuf ya bita da kallo yana hararta, Umma tace  "eh yakamata, Yusuf rakata hanya kaga dare ya fara yi, ni baki gayamin sunanki bama gashi zaki tafi"

Tai murmushi tace "Sunana Salma"

Umma tace "to Salma nagode, ki gaida mutan gidan"

Salma tace "zasuji insha Allah"

Badan Yusuf yaso ba ya biyota suka fito, Salma tace  "wai kai baka amsa gaisuwa ne?"

"Eh bana amsawa"

Salma tace "A'a kace dai nice baka amsa gaisuwa ta, da safe idan na ganka koda yamma idan na gaisheka seka wani basar kamar baka ji ba, kuma fa kana jina"

Banza yai mata suka cigaba da tafiya,  "au kana ji ina maka magana shine kamin shiru, ga mara hankali ko?"

Ko kallonta beba ya cigaba da takunsa majestically.

"Shikenan kar Allah yasa ka kulani É—in, kuma ma bana son rakiyar"

Yusuf yace "to ki gaida gida"

Ya juya ya koma gidansu, Salma tace "lallai ka cika É—an rainin hankali, dani kake zancen"

Washegari da Safe yakasance weekends ne ba aiki, dan haka bayan ya dawo daga salla, ya duba Umma yaga jikin nata da sauƙi, yakoma ɗaki  ya baje ya dinga bacci, saboda baya samun hutu sosai, yana tara gajiya matuƙa.

Se kusan ƙarfe goma na safe ya tashi da sauri, dan ya manta shaf zeyi girki, ya tafi ɗakin Umma da sauri ya shiga da sallama ya tarar da Umma a zaune da ruwa a hannuta, Yusuf yace "Ummana dan Allah kiyi haƙuri, bacci ne ya ɗaukeni me nauyi, ashe har an samiki ruwan ban sani ba ne, bari inje in ɗora ko tea ne inje in siyo bredi"

Umma tace "A'a baseka ɗora ba, ni a ƙoshe nake"

"me kika ci haka, har kika ƙoshi?"

Salma ce tayi sallama É—akin, hannunta É—auke da plate da kofi, Yusuf yana zaune a falon Umma, daga shi se gajeren wando da vest, dan haka kyakkyawar surar jikinsa ta bayyana, namijin gaske me tsabar kwarjini da kamala.

Yana ganin Salama ya miƙe yace " ke meye haka zaki shigowa mutane babu sallama, baki tsaya an baki iziniba kika shigo?"

Umma tace  "A'a ai tun ɗazu tana gidan nan, ita taimin shara da aikace aikace ma"

Ya kalli Salma da ta tsatstsareshi da ido yace  "to waye ya sata, Da kin bari Umma idan na tashi ai zanyi, ke Malama ajiye kwanukan nan ki tafi angode, zan kaiwa yayanki kuɗinki ya ajiye miki"

Hararrasa Salma tayi harda murguɗa baki, Umma tace  "jimin yaro da faɗan ba gaira ba dalili, daga taimako ita meta yi maka?"

"To Umma data gama aida seta tafi, amma kalli yadda ta ganni a haka ba kaya, kuma ta wani tsareni da ido"

Umma tace "to ubanwaye yace ka fito a hakan, ƙyaleshi kinji yau ban san dame ya tashi ba, naga yau rigima yake ji"

Yusuf ya fice daga É—akin yana mita.

Haka aka ƙarashe kwanakin nan a haka, kullum tazo se sunyi faɗa da Yusuf, in dai tazo seta yiwa Umma 'yan aikace aikace kafin ta tafi, ko su zauna su sha hira ita da Umma, Salma tana da kyau dai dai gwargwado, gata' yar kwalliya da iya ƙwalisa, tana da hasken fata da matskaicin tsawo, sannan tana da ƙirar jiki me kyau, ta yadda ko tafiya take tana ɗaukar hankali.

Mazan unguwar nan dana wajen umguwar da yawa suna rushing a kanta, amma bata da lokacin su, ba matasan samari ba har manyan masu kuÉ—i suna nuna tayinsu amma basu isheta kallo ba, Saboda mace ce me class, a mazan ma ba kowa ke iya tunkarar ta ba, saboda duk girmanka idan kamata abunda beyi mata ba, zata keta kane yadda take so kuma ko a gaban waye, Tayi school of Nursing, tayi midwife tana ji da kanta sosai.

A bakin yayyyanta taji suna hirar Yusuf wataran da daddare, ɗayan yace  "Habu gaskiya gayen nan da yaja salla da Asuba dama ya zasu bashi limanci, jar uba kaji ƙira'a kamar a Misra"

Habu yace "bari Usman, ni kaina da yaja sallar nan kamar kar ya dena karatun nan, ai rashin zuwan liman da wuri yau munga 'yan Islamiyya, anya wannan a ƙasar nan yai ilimin Addini?"

Usman yace "waya san masa, gaskiya ya iya karatu inaga zanje muyi bonding kona samu hasken makaranta"

"A gidan uwarwa zaka samu hasken makarantar? Bayan ko sauka Al'qur'ani ba muyi da kaiba ka fece neman kuÉ—i"

Habu yace "eh naji, aiba sharaÉ—ine se mutum yayi sauka za'ayi abota dashi ba"

"To bari in gayamaka, kaga duk wannan ilimin nasa shegen girman kaine dashi, baha kula kowa, iyakaci in ze wuce yai muku sallama, ban da haka ko aboki bashi da shi a unguwar nan, inda gayen ya ban haushi kenan, dan kana da ilimi ubanwa zakayiwa girman kai, kai ba wani shahararraen attajiri ba, ba basarake ba amma kace bazaka kula mutane ba"

Habu yace "Aikuwa ilimin baze masa amfani ba, dan girman kai rawanin tsiyane, ni harnaji ya bani haushi wallahi '

Salma tace   " Kukam Allah ya shirye ku, kawai kun zauna kuna tayi da bawan Allah kamar kun rasa abunyi "
Chapter 63 · 0% Book details