← Book details Akidata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 127

Sashe 45

Akidata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Widad ta girgiza kai tace "ni wallahi ina mamakin yadda za'ace mutane suna rayuwa babu Asibiti a guri, ai wannan se mutum ya rasa ransa ma ba'a bashi wani agaji ba, haba dan Allah to yanzu ba abunda za'a bata"?

"A'a na ɗan jiƙa kayan magungunanmu na gargajiya, na ɗan bata shima kuma tayi amansa"

Widad tace "Mama nifa bana son wannan kayan jiƙe jiƙen, su ba ƙa'ida ne dashi ba kawai sha akeyi, kuma kayan ciki basa san wannan jiƙe jiƙen, yanzu se wani abun ya taɓu, bari Yoseef ya dawo, in da sauran nasa magungunan se a bata"

Hindu tace "Nagode Amarya"

"Ba godiya tsakaninmu Hindu"

Jamila abun ya bata mamaki taji Widad na hira haka, kuma ta iya hausa amma tayi mata magana taƙi kulata.

Bayan Widad ta gama duba Hindu, ta tashi ta fita, Gwaggo ma ta fito tsakar gida, Jamila tace "wai nikam wacece wannan? Tana ji ana mata magana amma tana wani jin kanta tana share mutane"

Hanne tayi tsaki tace "bar shegiya, haka take wannan wulaƙancin dan tama ganinta a koɗe kamar an wanke karas, taita wa mutane wani iskancin banza da taƙama, se tsabar rashin kunya da rashin tarbiyya, ko magana bata iyaba ga ƙaryar masifa, komai seta dinga nuna bata sanshi ba, saboda gogewa mutane hadda "

Hindu dukda jin jikin da take, ba zata iya jure jin ana cin zarafin Widad ba, Hindu taja tsaki tace " Wallahi Jamila ba bata da mutunci bane, ni baki ga yadda tamin ba, bata da wata matsala, sedai bata sakin jiki da mutane, seta daÉ—e tukuna, bata fiye son mutane bane, amma Hanne san zuciya ne yasa kike cewa bata da mutunci"

A fusace Hanne tace "dalla malama yiwa mutane shiru, aikin banza uwar shisshigi se wani naniƙe mata kike kina cusa kai ba kwarjini, aikin banza dana wofi kawai"

Jamila tace "ya isa haka, ke Hanne abun faÉ—a baya miki wuya yaseen, har yanzu kina nan da tijararki baki dena ba"

Hanne ta riƙe ƙugu tana harare harae tace "ƙwarai kuwa, wallahi anamin nake ramawa ehee, babu 'yar masu baƙin jinin da zan saurarawa"

Shiru Hindu tayi, jin Hanne na ƙoƙarin fara ci mata fuska, Jamila tace "Hanne meye hakane? Nace ya isafa"

Hanne ta zumɓura baki tai waje, yinin yau Widad kanta bata da sakewa, ji take kamar itama bata da lafiya, Hindu tana matuƙar birgeta saboda biyayyarta da haƙurinta, shiyasa idan bata nan ko bata walwala Widad ma take shiga damuwa.

Saleh kam kwana biyu yayi ya koma kano, yaje ya tarar abubuwa nata sake rikicewa, dan ya fara karaya ya zubawa sarautar Allah ido, saboda tarakun da'aka kafawa Yusuf, ubangiji Allah ne kaÉ—ai ze iya fidda shi, dan babu imani babu tsoron Allah ko tausayi a tare da su Alhaji Musa.

Saleh yana gidan da yake zaune, yaji ana buga ƙofa yana zuwa ya buɗe yaga Abbas, Saleh yayi murmushi yace "Ahh saukar yaushe haka? Shigo daga ciki mana"

Abbas yabi bayan Saleh suka shiga, har falon Saleh, Abbas yace "ai yau sati na guda a garin nan, nazo in É—an huta ba inda nake zuwa shiyasa baka ganni ba se yau"

Saleh yace "Allah sarki, to ya Hanya?"

"Hanya Alhamdilillah, dan mun shata kam"

"to masha Allah"

Saleh yace "wai ni kuwa nace ya ake ciki ne? Har yanzu babu wani labari ne? Tun tafiyata banji wani motsi ba har yanzu ba'a samu komai bane?"

Saleh yace "haryanzu ba wani abu fa, ana ta fama ne abun duk se a hankali, shi can ya gudu ba'a san inda suke ba, shima kuma an sace shi, shi Daula babu wanda yasan inda yake haryanzu, anata fama ne"

Abbas yace "Ai naga sanarwar da aka yi akan Yusuf ne ya sace Ita 'yar Daula, hakan yayi ai hakan shine zesa hankalin mutane ya É—auke daga yin zargi, se a koma sauraren ta inda za' a gano su, ni babban abunda yake damuna ma kar muje ta bashi takaddun mu muna nan, dan wallahi ba kaga alherin da take masa ba"

Saleh kallon Abbas kawai yake harya kai aya, sannan ya numfasa yace "insha Allah, babu abunda ze faru, kota bashi takaddun babu yadda zeyi dasu, su Munir su suka san kan dukiyar, su suka san yadda za'ayi lamarin ya wakana, karka damu komai ze tafi daidai, sedai kamar yadda na gaya maka kansu suma a rarrabe yake yanzu haka, karka yadda wani ɓangare yazo ya nemi wani abu a gurinka, ka yadda ka bayar, karmu ɗau side mu zama a tsakiya, tunda bamu san ɓangaren da zasu yi nasara ba"

Abbas yace "dan wannan, ai karka damu tuntuni kamin wannan kashedin, kuma naji na É—auka, dan haka ka kwantar da hankalinka, sedai muna biue dasu, zuwa lokacin daza'a samu É—in"

Saleh yace "hakanma dai dai ne"

Daga nan suka cigaba da hirarrakinsu.

Daga baya kuma suka yi Sallama, Abbas ya shig motarsa sega kiran Suleiman, ya É—aga yana faÉ—in "Allah ya temaki Oga, barka da yamma"

Suleiman yace "Yawwa barka Abbas, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah Oga"

"Good, naji ance ka shigo garin nan, inba damuwa ina son mu haÉ—u gobe in Allah ya kaimu"

Abbas ya ɗanyi Jim sannan yace "shikenan Oga, yadda kace kaman da ƙarfe nawa?"

"Kamar goma na safe, muhaÉ—u a office"

"Shikenan, Insha Allah zan shigo"

Yana kashe wayar, Saleh yaja tsaki yace "Aikin banza munafukan banza, da kai aka haɗa baki aka canzamin gurin aiki, aka maida Yusuf kan kujerata, aiga abunda ya sameshi nan, Allah ya ƙara masa saura kaima"

Ya ajiye wayar yana ƙwafa, ya kunna motarsa sannan ya tafi.

Nurat ta rame tayi duhu, gaba ɗaya bata jin daɗin komai, tun mahaifiyarta tana rarrashinta harta haƙura, ita zatonta halayen mahaifinta ne suka sa tashi ga wani hali, bata san me yake damunta ba, ko Abincin kirki bata iyaci, ga wunin ɗaki data tsira, seta wuni cur bata fito ko falo ba tana ɗaki, Abinci in an kaimata ba zata ciba, sedai idan Mahaifiyar tace ta shiga ta sata a gaba shine zata ɗanci kaɗan, fuskar nan tayi fayau bakoma se dogon hancinta da idanuwa saboda damuwa.
Shikuwa mahaifinta sabgar gabansa kawai yake, yana ta faɗi tashi yana kashe kuɗi gurin malamai da 'yan tsibbu, da gurin manyan' yan siyasa domin ya samu ya koma takarar ɗan majalissa da Daula ya tsaya masa yayi, gefe guda kuma sunata cigaba da ƙulle ƙullen yadda ko sun rasa wanccan kuɗin, su samu wani kason ta ɓarauniyar hanya.

Yanzumu shiryawa yayi tsaf, ya tafi gidan Barrister Hafiz da kansa, domin jin inda maganarsu ta kwana akan batun ayi takaddar boge, ayi gwanjon wasu daga kadarorin Daula.

Barrister Hafiz ya karɓi Alhaj Musa hannu biyu, ya masa iso har falo aka gabatar masa da Kayan ciye2, Alhaj Musa ya ture farantin fruit ɗin yace "kafin wannan, dama zuwa nayi inji inda maganar da mukayi ta kwana? Yau kimanin wata guda kenan da yin maganarmu, amma shiru ba amo ba labari bakace mana komai ba, bamu san a ina aka kwana ba"

Barrister Hafiz ya ɗanyi shiru sannan yace "Yallaɓai kamar yadda a wancan lokacin muka rabu akan cewar, zan tattauna da sauran abokan aikin da muka kasance lawyoyin Alhaji Nasir Daula, na bisu ɗaya bayan ɗaya kowa naji ra'ayinsa, na zaɓe wanda nake ganin zasu iya yadda ayi harkar nan dasu, sedai me nazarin da mukayi, da binciken da muka sake yi shine, duk wata kadara da Daula ze siya muna sani, ko ince wasu daga kadarorin daze siya, a gabanmu akeyi da komai da komai, sedai fa takaddun Kadarorinsa babu ɗaya daga cikinmu daya san inda yake ajiye takaddunsa, dukda kasancewar mu lawyoyinsa, 'yar nan tasa dai ita kaɗai ce tasan inda kayansa suke, bakomai muka saniba, munyi tunanin yin takaddar boge kamar yadda kuka ce sedai babu wanda ze iya kwafar sa hannun sa, wataƙila se wannan yarinyar tasa"

Alhaji Musa yai shiru sannan yace, "shikenan ba damuwa, zamuje a bincika dole za'a samu wanda ze iya kwafa, nagode sosai idan akwai buƙatar sake nemanka, zaka jimu nan gaba nagode"

Ya miƙa masa hannu suka gaisa, ya tashi fita.

Nurat ce zaune a bakin gadonta tana ta sharɓe hawaye, wanda ya zamar mata jiki a 'yan kwanakin nan, tayi zurfi sosai a tunani, taji sallama a hankali ta ɗaga kai domin ganin me sallamar barrister Khalil ne, bayansa kuma mahaifiyarta ce, Amsa masa tayi cikin sanyin jiki.

A É—an razane ya kalleta yace "Subhanallah Anty Sauda dama haka Nurat ta koma?"

"to gata nan dai, shiyasa na kiraka ai, ban sani ba kokai idan kayi mata faÉ—a taji"

Khalil yace "sistona, meke damunki haka kinga yadda kika rame kuwa?"

Shiru Nurat tayi ba tace komai ba, Khalil yace "gayamin meke faruwa ne?"

ÆŠaga kai tayi ta kalli mahaifiyarta ta sunkuyar da kai, Khalil yace "Anty Sauda bamu guri muyi magana"

Ba musu ta juya ta fice ta basu guri, Khalil ya rufe ƙofae, sannan ya ɗakko kujerar gaban dressing mirror ɗinta ya ajiye ya zauna, ya kalleta yace "Nurat, tsakanina dake kin san babu ɓoye ɓoye ko? Bama ɓoyewa juna komai ki gayamin meke faruwa, kin san bazan fallasa sirrinki ba, sirrinki nawane ki gayamin koda taimakon da zan iyayi miki"

Aikuwa ta sake fashewa da kuka, seda tayi me isarta sannan tace "Brother meyasa wayarka bata shiga, na kira layinka babu adadi amma taƙi shiga?"

Khalil yace "wayar aka sa emin a gurin É—aurin Aure, se yau naje nayi swapping É—in layin, amma meyasa baki kira ko Mama ba muyi magana?"

Nurat ta goge hawayenta tace "bana son kowa yasan meke faruwa ne, bana son wani yaji shiyasa ban kira kowa ba".

"Shikenan naji, gayamin meke faruwa na ƙagu inji meyasameki haka?"

ɗakko wayarta tayi, ta buɗe labaran da ake yaɗawa akan ɓatan Widad, labarin me ɗauke da hoton Yusuf.

Ta miƙa masa wayar tace "Brother kaga wannan labarin?"

Khalil ya kalli wayar yace "eh naga labarin yana ta zaga gari"
Chapter 45 · 0% Book details