← Book details Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 119

Sashe 95

Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

an jim RK yay daga can, sai kuma ya nisa ya ce,
Ina asibiti. Miya faru?

Ambulance! Ka turo Ambulance yanzu ta
auki Mamy.
Murmushi RK yay mai sanyi, a ransa yay hamdala dan dama abinda yake jira kenan tun
azun, daurewa kawai yake yi amma hankalinsa gaba
aya nakan halin da Mamy
in ke ciki. Sai dai yasan bazai samu abinda yake fata ba sai AA yaje yaga halin da take a ciki saboda wasu dalilansa. Cikin abinda baifi mintinan ashirin ba Ambulance
in ta iso, zuwa lokacin harsu Oum na'a sashen dan abun kamar wani magic jikin Mamy
in ya rikice alamar jininta ya haura sama ko gani idannunta basa yi. Su Abah sun fita tun
azun, hakama Babban Yaya bai dawo ba. AA da Yaya Fawzan da kansu suka sakko da Mamy
asa, sannan aka sakata a abin
aukar mara lafiya aka fita da ita. ALLAH sarki Oum baiwar ALLAH, itace ta shiga kusa da Mamy
in. Su kuma su AA suka shiga motar Fawzan. Saheeba ma ta
auka su Mamansu suka bisu....
_________
Su Maanal basu san mike faruwa ba. Tana can da
an uwanta dan ba
aramin farin ciki tayi da ganin yayun nata ba, duk da yanda suke tsokanarta musamman Amaal ita dai tanata
oye fuska, har suka gaji suka barta, sun baje mata kayan da
in da suka kawo mata kowa na wani tattalinta. Sai Ammie da suka kira ta video call suka sha hira. Maanal na kuka Ammie nayi saboda farin cikin yanda abubuwa suka canja, baiwar ALLAH ji take kamar tai tsuntsuwa tazo Abujan ma. Albarka da addu'a babu irin wadda bata jerama AA ba yau harma da Maanal. Sunyi hirarsu cike da farin ciki da sha
uwa. Maanal nata zubama Ammie shagwa
a wai tana son ta tazo Kaduna idan ta warke sai ta dawo.
Ammie dake murmushi ta ce,
A'a Auta kiyi zamanki a
akinki kinji, ko sashen Aunty ban yarda ki koma ba balle Kaduna. Kefa yanzu kin girma, kiyi zamanki gidan aurenki kima mijinki hidima. ALLAH yay muku albarka ya baku zuri'a mai albarka kinji. In sha ALLAHU zanzo bikin Fawzan ai nan da sati uku
Murmushi Manaal tai mai sanyi, cike da shagwa
a ta ce,
Amma Ammie a wajena zaki kwana ko?
Dan kawai Ammie ta kwantar mata da hankali sai tace eh. Aiko hakan yama Maanal
in da
i sosai. Bayan sunyi sallama da Ammie suka koma hira a tsakaninsu, hirar da gaba
aya ta ta'alla
a ne akan batun fya
en nan, Amaal ta sanya Maanal gaba da sabuwar tsokana. Tun tana
yaleta harta fara ramawa, suka fara tsiyar tasu ta sako-da-sako.
Daga
arshe suka yanke shawarar zuwa Giro da babbar salla. Dan Maanal ta rantse sai taje ta maidama Gwaggo da kaf mutanen gidansu murtani babu fashi. Yanda tayi
in ya tabbatar ma su Amaal
anwarsu ta dawo ainahin Maanal ta shekarun baya data mutu. Aiko
ari bisa
ari suka bata goyon baya akan wannan
udirin nata, sun kuma ro
i Aunty Sakina kada ta gayama Ammie dan sai sun dawo zasu sanar mata karma ta hana su. Ta tabbatar musu bazata fa
a ba, kuma tana goyon bayan zuwan nasu itama....
Sai da sukai Magrib sukai
arin tafiya, a lokacin ne Hajiya Shuwa ta shigo yima Maanal gashi take sanar musu ai an tafi da Mamy asibiti jikinta ya rikice. Mamaki ya kama Maanal dan sai lokacin ma ita take sanin Mamyn bata da lafiya gaba
aya...

Matu
ar sanyi jikin Auntyn su Mamy yayi da ganin yanda RK ke tsaye akan al'amarin Mamyn tunda suka iso asibitin, dan cikin
anin lokaci likitocin da zasu dubata sun rufu a kanta. Sai taita kallon Maman Saheeba da tace bata yarda a kira Rafeeq ya duba Nuratu ba tun a jiyan. Itama kuma Mamyn da akace a kira Rafeeq ya dubata da safe catai bata yarda ba. Ta maida kallonta kan Oum datai shiru damuwa kwance a fuskarta, AA da Fawzan sun sakata a tsakkiya suna lallashi. Sai Auntyn taji kamar ta fara jin kunyar kanta. Anya kuwa babu gyara akan al'amarin su na
in baiwar ALLAHn nan Hajiya Fateema. Koba komai fa itace sanadin shigiwar
ar uwar tasu a wannan daular. To wai miyema aibunta da suke zaginta?
ar uwarsu fa ce da kanta ta
auka yaran ta bata..... Wannan tunani shine dan
are a zuciyarta har RK ya fito yana sanar musu karaya ce fa a
afar Mamy, sannan akwai
onewa a jikinta...
A tare Oum da Ya Fawzan sukace,
Karaya da
onewa kuma?
. Sai suka juya suna kallon su Maman Saheeba alamar tambaya. AA kam yama gagara cewa komai. Cikin
arfin hali Oum ta ce,
Aunty amma bakuce mana da
uma ba ai, batun karaya nasan maybe wancan likitan ne bai san aikinsa ba
Cikin
arfin hali Aunty ta ce,
Wlhy bamu san da
unar ba muma Oum Fawzan (da haka take kiran Oum kafin Mamy ta nuna bata so). Amma tabbas tea ya zuba mata a jiki babu kuma wanda yay tunanin zai
onata, ita kuma batayi magana ba
RK ne ya ce,
Ai shi ruwan zafi ba'a rainashi gaskiya. Yanzu dai an kira wanda zai yi
orin karayar kun san mu anan asibitin muna aiki da
orin karayar gargajiya ne saboda mai yi mana aiki na wannan fanin yasan aikinsa. Zamu jirashi dan yana a suleja ne. Amma gaskiya likitan can da kuka kira ya dubata bai san komai ba, kuma da
afar nan takai wasu kwanaki a haka komai zai iya faruwa. Dan haka ina baku shawara ku kiyaye, kusan da wa
anne irin likitoci zakuyi mu'amula musaman wanda kuke iya kira gida su muku aiki.
Daga haka ya juya ya fita ransa a
ace. Ita kanta Oum ranta ya
aci, dan tun
azu dama yanda sukai
oye-
oyen halin da Mamyn ke a ciki yanata mata kai-kawo a zuciya. A ganinta mizaisa suyi hakan? In dama
aramin ciwo ne sai ace. Shi kansa Abah ta fahimci ransa a
ace yake. Ture tunanin tayi daga ranta gaba
aya ta
yautata musu zato kawai da yardar ma zuciyarta abinda suka fa
a a
azun. (Wannan shine babbar halayyar Oum dake saka mata kwanciyar hankali akan zamanta da kowa, take kuma iya hakuri da dukkan jarabawarta. Tana da
arin
yautatama mutum zato. Ko abu akai mata a gabanta mara
yau kai tsaye bazata saka jin zafin mutum a ranta ba, sai taita kawo uzirin maybe kaza ne, ko kaza yasa yay haka. Sai kaga zuciyarta ta samu salama da kwanciyar hankali. Mu gwada kasancewa haka zamu sha mamaki wlhy koda akan mazajen aurenmu ne ma
Waya ta ciro ta kira Abah ta sanar masa komai. Yace mata suna masallaci idan sun idar da salla zasu zo. Daga haka ya yanke kiran. Mamaki ya kamata jin babu wata damuwa a cikin muryarsa. Amma sai ta ture tunanin kawai. Ta kalla su Fawzan tace suje suyi salla suma....
Sai bayan sallar isha'i mai
ori yazo, lokacin suma su Abah na asibitin harma da Babban Yaya. Su Hajiya Majdiya da su Umma ma sun iso asibitin jin shiru su Oum basu dawo ba.
Chapter 95 · 0% Book details