← Book details Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 119

Sashe 9

Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

______________
.......A
angaren Mamy kam ranta fes akan hakan. Burinta
aya yanzu shine Maanal ta dawo sashenta da zama kamar yanda ta zunguri Abah da zancen. Sai dai kamar ya yarda da farko sai kuma taji bai sake maganar ba. Ta
an bashi kwana biyu ne ta sake zuwa masa da zancen, dan idan ta cika matsawa zai harbo jirgin ta ne kasancewarsa mutum mai tsarta. Ajwaad kuwa data fahimci kauce-kaucen sa zata tattarashi ne ta watsar, akwai ga
ar data tanada masa ne. Sun gama tsara Nuratu zatazo nan gidan tai azumi. Acewarsu mamanta zata shirya ta tafi umrah sai ace Nuratun tazo nan ta zauna kafin ta dawo. Gefe kuma cike suke da alwashin bayan salla da sati biyu koda tsiya-tsiya sai an
aura auren Nuratu da Ajwaad idan ba haka ba kuma suyi maganin Oum...
Oho ita bama tasan sunai ba. Duk da bata son ha
in auren Nuratu da Autan nata bata ta
a ji a ranta zatai wani yun
urin hanawa ba. Fatanta ma ALLAH ya daidaita komai ya canja rayuwar Nuratu
in su zauna lafiya da Maanal da shi kansa Ajwaad data san baya son ha
in auren nan. Kai ko Mamy gani take bata so dan haka take nuna mata a zahiri. Da yake zuciyar Oum
in a tsarkake take kuma sai bata ta
a bin
wafin Mamy akan komai ba sam...
Yau ta kasance lahadi, dan haka Oum ta samu Abah da batun komawar Maanal aiki gobe idan ALLAH ya kaimu. A cewarta da zaman nan gara ta koma aikin sai ta samu nutsuwa sosai. Da farko Abah shiru yayi, dan sai ya dinga hango ai zuwa office
in zai saka Ajwaad yaga ya samu wata dama akan Maanal
in ne. Shiru ya
anyi na wasu sakanni, sai kuma cikin jinjina kai ya ce,
Okay zan yi tunani akan hakan
ewa Oum tayi tana masa sallama, dan har yanzu basu koma dai-dai da Abah
in ba. Ta dai daina fushin da take yi da shi. Da kallo kawai ya bita yana murmushi da girgiza kansa. A ransa yace (Fatete na rigima kenan) da murmushin Oum
in Mamy dake da shi yau ta shigo ta samesa. Koda yake tun ma bikin su AA
in Oum tace ta bar mata Abah
in har sai Maanal ta tare. Hakan ba sabon abu bane ga Oum. Dan haka kawai idan ta bushi iska sai tace ta barma Mamy Abahn na sati biyu koma na sama da hakan. Wani lokacin Abahn ne ma ke gajiya ya balbaleta da masifa yace shi bai yarda ba kamar dai yanda ya sakata kwana a gunsa dole randa yayar Mamy ta kwana a gidan.
Sosai ran Mamy ya sosu da murmushin nasa, wanda tasan akan Oum
in ne tunda sun ha
u a waje. Tarasa ya zata raba wannan sha
uwa da soyayyar, duk da haihuwar da tayi, da kwantar da kai tana musu bauta su duka biyun har yanzu Oum ta fita matsayi da girman iko a wajen Aliyu. Sam baya iya
oye
aunar da yake mata koda a gabanta ne ita Kamila. Baya shakkar yabon Oum ko sanya mata albarka ko yin kwatance da ayyukan alkairinta. Hira goma zaka zauna da shi zai ambata maka sunan Fateema so takwas ne kansa tsaye. Cikin takaici ta ha
iye
acin ranta ganin ya juyo gareta, a hankali ta maye fuskarta da sassanyan murmushi cike da makirci take tambayar fitar Oum
in wai taga ranta a
ace. Ikon ALLAH sai Abah
in yay nauyin baki yau, dan murmushi kawai ya mata baice komai ba. A
asan ransa kuwa hankalinsa na'a kan Oum
in ne, bu
atarta yake a jikinsa
warai da gaske, yana kewar sassanyan
amshinta da kulawarta a garesa. Badan wai Mamyn bata masa ba ita, kawai dai yana jin na Fateema a garesa special ne. ALLAH shine ka
ai yasan irin son da yake ma Fateema da
auna a rayuwarsa, shiyyasa yake kallon al'amarin Ajwaad da Maanal tamkar nashi da Fateema ne. Dan soyayyar yaran gaba
ayanta tamkar gado ne daga tasu soyayyar, abinda kawai ya banbanta shine shi da Fateema jini
aya ne...
Haushin ganin ya tafi zurfin tunanin nasa wanda Mamy tai imanin akan Oum ne yasa ta mi
e ta wuce bedroom
insa. Dan tana fara ganin irin wannan signing
in a garesa a duk lokacin da Oum ta bar mata shi take fahimtar ya gundura da ita hankalinsa nakan matarsa. Tasha zargin kodai Oum tana musu hakan ne dama dan wani tarko nata ko shiri, amma idan ta nutsa a bincike sai ta gano sam ba hakan bane ba..
Abah ya jima kafin ya dawo daga duniyar tunanin nashi, sai sannan kuma ya farga babu Mamy. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya
auka wayarsa ya tashi ya fita domin kiran
an uwansa suyi shawara akan batun Oum
in na komawar Maanal aiki. Wato Uncle Mahmud.....
____________
Kuka bana wasa ba Nurry tasha da jin batun
aga bikinta dana AA har sai zuwa bayan salla. Wani irin tsanar Oum da Maanal ta
ara fa
i da kauri a zuciyarta. Nanfa ta shiga
aukarma kanta alwashi kala-kala na gasama Oum da Maanal aya a tafin hannunsu. Dan ta tabbatar kamar yanda taji iyayenta na fa
a makircin Oum ne kawai. Bata sami nutsuwa ba har sai da sukai waya da Mamy da Saheeba da suka kwantar mata da hankali da tabbatar mata aure na nan babu fashi. ALLAH dai ya kaimu bayan sallar da sati guda za'ai ma ba biyu ba.. Sannan a gidan zatai azumi kuma...
Hakan ya
an sakata jin sanyi da sassauci a cikin ranta. Harta
an saki jiki ta cigaba da harkokinta musamman a media. Harda su tsara write-up ta turama
awayenta da abokan arzi
inta cewar biki sai bayan sallah saboda har yanzu ango babu lafiya.....
___________
WASHE GARI.
Safiyar yau Litinin har Oum ta fidda ran Abah zai bar Maanal
in ganin tun jiyan baice mata komai ba. Haka shima AA
in baima saka ran komawar Maanal
in yau ba. Kawai dai ya tashi da nasa shirin ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a
akin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a
ofar bedroom
in sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga
akin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na ha
uri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba.
an nesa da shi ta zauna, sai kuma ta
an zamo a kujerar ka
an cike da neman magana ta ce,
Yaya Aliy ina kwana
(haka take kiransa lokacin
uruciya). Hararta yay da fa
in,
A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran
anki zaki ce dani wani yayan gulma
aramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce,
Kun tashi lafiya?
Alhamdullahi
Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da fa
in,
Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da shara
in driver zai dinga kaita ba
anki ba. Dan bana son wata ala
a ta ha
asu. Ki kuma garga
esa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan
ara yawan kwanakin suspension
Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs
in yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips
insa a hankali ya furta,
Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal
. Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office
in....
Oum ma bayan tafiyar Abah
aki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje
ayan dama ya isheta sai taji gabanta ya fa
i. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla
an company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita
in matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?.....
Ko baki son komawa ne Baby?
Oum ya katse mata tunani.
asa tai da kan nata tana
aro murmushi. Sai kuma
asa-
asa ta ce,
A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin
an kamfani ne
Dariya sosai Oum ta sanya da fa
in,
Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki ri
e girmanki, ki
ara
wazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka
Cikin jinjina kai Maanal ta ce,
Amin
Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen ha
a musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal
in ta koyi yanayin fitar tashi tunda na
an lokaci ne zasu koma fita a taren..
Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matu
yau da haska chocolate color skin
inta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan
amshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da
an lips-gloss ka
an. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye
aramar handbag
inta saman table
in dining
in itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen
amshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matu
yau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta
an motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara
arin zuba abincin a ranta tana
unin (wayace ya sake airin kayanta)
Auta har an fito?
Oum ta fa
a dai-dai isowar AA dining
in. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai
an bata side hug. Sai kuma a
asa-
asa ya furta,
Barka da safiya my everything
Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da,
Ka tashi lafiya ya
arfin jikin?
Alhamdullahi Oumna, ai
anki ya warke sarai in sha ALLAHU
Masha ALLAH haka muke fata ai Auta
A hankali Maanal data
i sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumu
i da maradin hakan ta ce,
Ina kwana
Batare daya kalleta ba shima ya ce,
Lafiya
. Daga haka ya kalla Oum a
an shagwa
e ya ce,
Oum yunwa zata cinye hanji na
aramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal
in dai-dai ta
ago ta hararesa. Dan itace ke fa
ar haka idan tana jin yunwa. Gira
aya ya
age mata irin (Ni
in kike harara?) sai ta sake murgu
a masa baki sannan ta
auke kanta. Ita dai Oum wurin tai
arin bar musu tana fa
in,
Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne
Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta
auke idanun nata. Tsohon minti
aya kafin tace,
Me zaka ci?
Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta
ago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya
ago lumsassun nasa
ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips
inta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce,
Nace mi kake so?
Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips
in nasa
asa-
asa ya furta,
...........
_Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba
, shine nace bara na tambayeku
*_AJIYA A DUHU na ku
i ne, 500 ne kacal,
ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu.
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
*_Typing
*_
AJIYA A DUHU....
*_Bilyn Abdull ce
_Da s
nan Allah, Mai rahama, Mai jin
ai._
*_My TikTok account
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing
ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama
*_BOOK 2_*
Chapter 9 · 0% Book details