← Book details Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 119

Sashe 46

Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

______________
.......Da farko AA baya kulashi kamar yanda baya kula kowa a makarantar. Yakan dai shiga aji da an gama lecture zai fito yazo wajen ya zauna har sai lokacin wata kuma. Sai yazo yini guda ya fita baiyi magana da kowa ba a school
in. Wani lokacin Babban Yaya da RK ke zuwa
aukarsa, wani lokcin kuma Abah da kansa kuma su suke kawosa. Kamanin da suke da juna yasa Zhang fahimtar suna da ala
a ne, ya kuma ji sunan Maanal ne a bakin AA, dan in yana zaune shi ka
in nan yakan rufe idanunsa yay shiru a kujerar wajen kamar mai barci amma zakaji sunan Maanal na fita masa a baki ko yace Besty. Tun Zhang na
aukar AA nada matsala ta brain shiyyasa yake sambatun kiran abinda bai san miye ma'anarsa ba har daga baya ya gane AA yana cikin depression ne. Dan yayi course na karantar halayyar
an adam. AA ya bashi tausayi, dan haka ya fara zama kusa da shi koda bazai kulashi ba, dan wani lokacin ma tashi yake ya bar masa wajen. Shi kuma bai ta
a ce masa komai ba tsawon lokaci har AA
in ya daina tashi a waje idan yaga Zhang yazo ya zauna. Yau da gobe sai yake zama suyi gaisuwa kawai har dai shakara taja. Bayan sanin sunan AA abu na biyu da Zhang yaso sani shine miye ma'anar Maanal, sannan waye Besty da yake jin AA yana yawan ambanta.
Maanal suna ne, kuma itace Besty
. Ya bashi amsa a ta
aice. Ya ce,
Mace ne ko namiji?
. Anan ma AA bai kawai komai ba ya ce,
Mace
. Tun
daga nan Zhang ya fahimci matsalar AA. Bai sake masa tambaya akan hakan ba kuma har AA
in ya fahimci abinda Zhang ya karanta, sai kawai Maanal tazo masa a rai da zane-zanenta.
Wannan shine tushe kuma asalin kafa ala
arsu, kuma shine ya taimaka masa wajen kafa Maawad Company dan da taimakon Professor Zhang. Ya ta
a zuwa Nigeria lokacin bu
e MAWAAD COMPANY. Hakama zanen dake a companyn yasan na Maanal ne dan anan Chaina AA yasa aka zana shi yana siffanta musu ita. Har zuwa yanzu AA bai ta
a bashi any labari akan Maanal ba, iya abinda ya sani kenan, amma da kansa ya fahimci ita budurwarsa ce, amma basa tare. Sanin AA baya kula mata sam ganinsa da mace a yanzu da kuma kamanin da Maanal tai masa da wani hoto daya ta
a gani a wallet
in AA passport ne ma yasa shi saurin ganewa duk da bai tabbatar ba ya dai canka ne kawai....
Rungume AA Prof yay cike da tayashi farin cikin jin ga Maanal a matsayin matarsa, cike da tsokana ya ce,
Wannan karon dai tunda Maanal ta dawo ya kamata nasan labarinta
A mamakinsa murmushi AA yayi, bai kuma musa ba, amma bai ce komai ba dai a bayyane. Maanal AA ta zubama ido, tana son fahimtar mi Prof ke son fa
a, sai dai ya
i yarda ma su ha
a ido har suka isa wani aji bisa jagorancin Prof
in. Sun fara gabatar da lecture ta awa
aya. AA na kusa da Maanal dan haka ta dinga masa tambaya akan abinda bata gane ba dan anayi suna rubutawa ne. Bayani yake
an mata, wasu kuma yace ta bari su koma masauki dan ta samu damar fahimtar Prof
in. Daga school
in wani companyn Prof ya wace da su. Su AS suna a motar su kamar yanda suka zo, ita da shi a mota Mr Li na jansu, sai Prof a gefen driver. Hira suke da AA da Chaines, dan haka Maanal ba fahimta take ba. Sai ta ma maida hankalinta a bitar abinda suka koya yanzun nan. Wani katafaran companyn agogo sukazo. Sosai wajen ya birge kowannensu, suka cika da fatan suma wataran suga companyn su a haka. AA da Prof ne suka jagoranci zagayawa dasu, Prof na musu bayanin komai yanda zasu fahimta su kuma
aru da ilimi. Suna ko
aruwar, dan duk sun nutsu yanda ya kamata. Maanal sai take jin kamar ana wanke mata brain ne, wani sabon karsashi take
ara ji game da zane-zane bama na agogon kawai ba. Anan sukaci lokaci sosai. Bayan sun fito suka maida Prof makaranta, su kuma suka nufi wani wajen. Isowarsu yasa kowa ya fahimci massallaci ne. Sosai nan ma ya birge su Maanal, musamman ma ita da AA ke mata bayanin komai. Hakan ya fahimtar da ita lallai AA yasan Shanghai sosai, kuma da alama yayi zaman garin ma. A karo na farko ta fara kwa
ayin son jin wani abu game dashi bayan rabuwarsu. Lokacin sallar zuhur ne, ita da CFO Faseelat suka nufi sashen mata, su kuma su AA sashen maza. Itama Faseelat ta ta
a zuwa massallacin dan ita wannan shine karo na biyu da akai irin tafiyar nan da ita a
ashin kamfani, sannan a karan kanta tazo Chaina har cikin Shanghai yawon bu
e ido da tsohon mijinta. Kuma duk ta ziyarci massalacin dan yanada tarihi mai girma a wajen musulman Chaina. Koda aka idar da salla zamansu sukai, dan AA
in yace suna nan har magrib. Alkur'ani Maanal ta
auka tai karatu, sai Faseelat ta shagala a kallonta, daga
arshe ta
ingire barci itako Maanal nata karatunta har Asr. Ita ta tada Faseelat
in ta fita ta canja alwala, sun gabatar da la'asar sai suka fito domin shan iska kamar yanda Faseelat
in ta shawarci Maanal. Bata musa mata ba, dan koba komai matar zata iya haihuwar kamarta idan auren wuri tayi.
A mamakinta suna fitowa sai suka hango AA can cikin wata rumfa zaune tare da wani. Kamar ance ya juyo suka ha
a ido. Wani
an sassanyan murmushi yay mata itama sai ta samu kanta da maida masa murtani. Da hannu yay mata alamar tazo. Sai ta
an juya ya kalla CFO. Gani tai itama hankalinta akan AA
in yake, duk da dai tana kallonsa ne cike da basarwa na manyam matan Abuja. Cikin
an kwantar da murya na girmamawa Maanal ta ce,
Bara naje yana kira
Kamar wadda ta daburce CFO ta amsa mata a
an daburce. Ita dai Maanal batabi takanta ba tai gaba. A zuciyarta ko fa
i take (Tsohuwar kawai
walelenki wannan kayan sai Maanal) tai gaba abinta. Tan a isowa wajen AA ya kamo hannunta ya zaunar a kusa da shi, kafin cikin girmamawa ya kalla dattijon mutumin da sai yanzu Maanal taga fuskarsa ya nuna masa Maanal
in da alamu suka tabbatar ya riga ya masa bayani a kanta. Ita kuma ya juya yana sanar mata cewar shi
in malaminsa
ng Chen a lokacin da yay zaman Chaina na tsawon shekara biyu. Murmushi Maanal tayi, cikin harshen turanci ta rissina ta gaida shi. Shi ko dattijo
yawa cikakken bacine da hasken addinin Islama ke zageye da kwarjininsa ya amsa mata da kulawa shima da harshen Ingilishi. Ya
ora da addu'a a garesu. Kan Maanal a
asa take amsawa, yayinda AA ke amsawa kai tsaye.
ng ya shiga yi musu nasiha da bama Maanal
in labarin zamantakewarsa da AA, a labarin Maanal ta fahimci
ng ya taimaki AA sosai a rayuwa, dan har lokacin da suka ha
u AA na cikin depression, shine ya ringa masa addu'oi da shawarwari ya jashi a jiki har ya bayyana masa damuwarsa, cikin ikon ALLAH kuma kafin yabar garin sai gashi abubuwa sun dai-daita masa. A cikin labarin yake basu shawarwarin gina
yawar ala
ar rayuwar aure mai tsafta da dan
o. Sosai Maanal ta jinjina ilimin wannan bawa, ashe mu ba
e musamman a Nigeria da muke
auka kamar mune kawai musulmai ashe namu wasa ne, dan da yawanmu bama
arin neman ilimin addini akwai dai son addinin a tare damu wannan ta shaida kam...
Kiran sallar magrib ne ya tashesu a wajen, ita ta koma sashensu na mata su kuma suka nufi na maza. Alwala tayo dan bataga CFO ba. Sai da ta shiga massalacin ta ganta a sahun gabansu, batayi magana ba tasha ruwa da dabinon da aka basu sannan aka gabatar da sallar magrib. Bayan an idar suka fito domin yin bu
a baki anan harabar massallacin da ake shiryawa gwanin birgewa.
angaren mata daban na maza daban. A yanzu sun gaisa da mutane daban-daban dan matan basu da yawa sosai. Daga ita dai CFO ne kuma ba
ar fata a wajen, duk da Faseelat farace tas-tas da alamar ma ana
arawa da skincare, amma hakan bazai hana a kirata ba
ar fata ba. Itako dama ba
ar ce, kuma Alhamdullah tana alfahari da fatan ta. Ka
an ta tsakuri abincin, lokacin isha'i yayi suka koma cikin massallaci. Anyi sallar isha'i akai asham. Sun gaisa da mutane akai sallama kowa ya fito domin kama gabansa. Sosai rayuwa a massalacin taima Maanal da
i, duk da wani gefe na zuciyarta na missing
asarta ta haihuwa da yanda azumi ke kasancewa musamman na farko da ake kaishi cike da
oki da buri. Waccan shekarar iyanzu suna a Jos ita da su Zeezah, acan sukai azumin sai da yakai tsakkiya suka dawo Kaduna. Sai ta
ara jin wani kalar kewar mutanen gida...
Mi matar Ajwaad ke tunani? Bayan gashi a gefenta
A bazata taji saukar lallausar muryarsa a cikin kunneta, fiskarta da murmushi ta juyo, yana daga bayanta ne ya
an du
o, sai ta samu kanta da kai yatsa ta
an dungure masa kai da fa
in,
Miyasa mijin Maanal ya cika sa ido ne?
Murmushi yayi mai fa
i da
yatarwa, ya mi
a sosai tare da kama yatsar nata cikin hannunsa. Sosai abinda ta fa
a ya wani ratsa masa zuciya da cikata da farin ciki. A hankali ya jawota gabansa, batare da tunanin komai ba balle kunyar mutanen dake
an kai-kawo ya rungumeta, dan su AS har sun wuce wajen mota. A hankali ta kumshe idanunta, shima haka, suka saki ajiyar zuciya a tare zukatansu na sauka a kankali daga nauyin da su kayi. Cikin
aramin sauti mai marmashe zuciya AA ya furta,
Barka da shan ruwa ZUCIYAR AJWAAD
Wani irin zuuu Manaal taji a jikinta. Sosai kalamansa na
arshe suka mata nauyi. Akwai sha
uwa mai girma tsakanin da AA, irin sha
uwar da zata iya rantsewa bata ta
a yi da wani ba.
aya baya
aunar ganin
aya a damuwa, hatta da ciwo sun sha yi a tare. Abubuwa da yawan gaske nasu a tare ne. Amma basu ta
a danganta al'amarinsu da wata kalma ta soyayya ba koda
anuwa. Sai dai suji a bakin mutane na ambatawa amma basu da kansu ba. Zata iya cewa wannan itace kalma ta biyu a rayuwarta da taji daga bakinsa da zata iya kamantata da hakan bayan kalaman
azun da asubahi, amma sai ta basar, kamar yanda suka saba ta
ago fuskarta da dariya tana kai masa mintsini....
Da sauri ya ce,
Ouch! Besty wai a ina kika koyo muguntar nan ne?
Dariya tayi tana
an tafiya da baya, girarta a
age ta ce,
Da zafi ne?
Hararta yay da
an ha
e fuska ya ce,
Kina son sani?
Gira ta
aga masa.
Ya ce,
Okay bari sai munje makwanci zan banbance miki
Duk da gabanta ya fa
i sai ta sanya
ar dariya,
Besty ai nasan kai bawan ALLAH ne baka fa
a cikin azumi
Yanzun kam dariya sosai tazo masa amma ya daure baiyi ba ya saki murmushi tare da takawa ya ri
e hannunta daga
ar tafiyar da take da bayaya. Tafiya suka fara a tare cike da nutsuwa har zuwa wajen motarsu, Mr Li ya bu
e musu suka shiga. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna. Murmushi sukayi a tare, gira a
age AA ya ce,
Yaya kin gaji ne?
Sosai ma, burina kawai nakai kwance yanzu. Gashi kuma ina son duba lecture
in yau
Kafa
arsa ya
an matso mata alamar ta kwanta. Sai da ta kallesa sukama juna murmushi mai sanyi sannan a hankali takai kwance a kafa
ar tana sauke ajiyar zuciya acan cikin
irjinta. Sai kuma ta gyara zamanta tana lumshe ido. Baice komai ba illa
an kallonta da yay ya
auke idonsa. Cikin
anin lokaci Maanal tai barci, har bata san sunzo sun tsaya gidan abincin ranar ba Mr Li ya fita yay musu takeaway dan yasan zuwa anjima dole zasu bu
aci abinci........
*_AJIYA A DUHU na ku
i ne, 500 ne kacal,
ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
*_Typing
*_
AJIYA A DUHU....
*_Bilyn Abdull ce
_Da s
nan Allah, Mai rahama, Mai jin
ai._
*_My TikTok account
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing
ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama
*_BOOK 2_*
Chapter 46 · 0% Book details