← Book details Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 119

Sashe 111

Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yayi da yanda ta katsatstsare ta dinga aibanta yarinyar da mahaifiyarta. Sai gashi yanzu Ammien ce dai tsaye a al'amarin an nata da ta hana ya auri arta... Ji Hajiya Yaya tai abubuwan sun mata yawa. Kamar tana jin nauyin Ammie kuma a asan ranta. Amma dai a zahiri bata nuna ba, ba kuma ta furta ba. Sai dai duk shawarar da Ammie ke bata akana al'amarin Yazeed yi take yi. Yayinda Hajiya Basariyya ke bata mamaki.. Duk da kai-kawo gulma da Hajiya Basariyya keyi hankalinta kuma na'a kan Huznah ne, tama Daddy magana akan rashin jin Huznah in ya nuna mata ta shiga hankalinta ta kama kanta, idan ba haka ba kuma zatasha mamaki. Da yake yanzu tana tsoron komawa gidan Kawu Manu sai tai shiru, sai dai abin na damunta a rai matu a, musamman daya kasance Maman Yaseerah ta mata bayanin komai har wayar da suka dinga yi da Huznah kwanaki ta kuma daina jinta ma gaba aya...... ___________ KANO. Anan Kano kuwa abu biyu ne ke shirin faruwa a angare biyu. Bangaren Huznah mahaifin Sageer yace ya barta taje ganin gida dan a tunaninsu Hajiya Basariyya ta risina yanzu zata kama kanta akan al'amarin auren yaran. Yazeed dai zuciyarsa bata so hakan ba. Amma bazai iya jayayya da iyayensa ba ya amince. Amma ya ro a alfarmar a bari har sai babbar salla dake tunkaro mu. Zuwa lokacin itama ta ara jin sau i sosai duk da dai Alhmdllh zuwa yanzu ma taji sau in. Shi kuma yana samun damar baje hajarsa yanda ya kamata a jikinta, sai dai taci kukanta a oye da jera masa ALLAH ya isa babu damar yi a gabansa dan wani tsoronsa take ji bana wasa ba. A hakan ma sai yaga ta takura kanta da yawa ne yake an sassauta mata. Ko in yaga laulayin ya takura mata, dan wani lokacin takayi lafiya na kwanaki sai kuma jikin ya rikice.. Ga kewar yan uwanta dana mahaifiyarta, dan Alhmdllh a cima babu abinda ta rasa a gidan Sageer. Duk da kasancewarsa talaka yana iyakar arin sa na bata abinda take ci a gidansu. Kuma duk abinda zai sakata a farin ciki yana iyakar arin sa yay mata gwargwadon ikonsa.... _______ angare na biyu kuwa su Baba Sardauna da Baba, Abbah, Uncle Mahmud, Hassan, Hussain, Najeeb da wasu aminansu Baba Sardauna uku a yau suka shiga garin Katsina domin ganawa da dangin mahaifan su Ameerah. Kwarjinin Darma a idanun al'umma da yawa daban ne. Ko sunan wannan family kaji alkairansu nasa kaji kimarsu da girmansu a zuciya. Duk irin alwashi da cika bakin da dangin mijin Hajiya Shuwa suka dingayi akan sai sun nuna mata su in sune a bikin Ameerah sai gashi sunyi kurum. Dan kuwa wata gaban ai tafi gaban a taka... Jikunnansu na rawa suka ma su Baba Sardauna tarba ta mutuntawa, ta girma, ta kuma martabawa. Dan kuwa cikin ikon ALLAH a cikin annen baban su Ameeran akwai mai aiki a arkashin asibitin Abbah. Wato KK HOSPITAL dake garin Kano. Babu wani ja'inja ko kai kawo sukace sun bama Babban Yaya Ameerah, kuma sun yarda a ha e biki dana Fawzan nan da kwanaki goma kenan. Matu ar jin da i su Baba Sardauna sunyi da wannan karramawa. A take Uncle Najeeb ya ajiye sadaki daga aljihunsa. Uncle Hussain ya ajiye ku in gaisuwa dana mungani muna so dama duk wani tarkacen tsarabe-tsarabe na aure. Akai hu ar arzi i aka kuma rabu cikin mutunta juna da karramawa. Suma sukace suna nan tafe Kano nemawa Ameer auren Maimoon. Shi halin girma duk mai shi to mai halin girman ne. Sai kawai Baba Sardauna yace in dai haka ne wace wahala kuma. Ai kawai ayi komai anan a gama sun hutar dasu a ha e ranar aurin aure. Babbar magana. Dangin mahaifin su Ameerah fa mamaki ya sake kamasu da wa an nan bayin ALLAH. A take sukai kiran Hajiya Shuwa suka sanar mata. Ai sai ta sanya kukan farin ciki, babu wani jeka ka dawo tasa Ameer ya tura ma kawunansa ku e. Suma dai a take anan akai hannun kar a kuma hannun bayarwa. Dan suma dai sun ajiye ku in gaisuwar Ameer da sadaki da dukkan abinda ya kamata na aure. Kafin aka sake sabuwar addu'a suka musu rakkiya airport dan dama ta jirgi suka zo. Dan haka komai da komai cikin awanni biyar aka yishi aka kammala tamkar a cikin Kano akayi... ________ Lokacin da duk su Maanal ke dawowa aiki da wannan farin cikin suka iske Oum a ciki, su Mamy dai basu san anayi ba. Sai da su Oum da ayanta da RK da Matarsa dake gidan suka gama farin cikinsu da murna RK da Fawzan harda ma Babban Yaya li in ku i dan neman tsokana. Abin ya bama Oum da Maanal dariya sosai, AA kam sai murmushi yake, shi ka ai yasan a irin kalar farin cikin da yake a ciki yau. Yayinda yake sake girmama al'amarin UBANGIJI. Wani gefe na zuciyarsa na addu'a da fatan ALLAH yasa Mamy kada ta aga hankalinta akan wannan al'amari dan itace kawai damuwarsa ba wata Saheebar banza da wofi ba. Sai bayan sallar isha'i a karo na farko tun bayan bikin AA da Maanal Abah yay kiranyen meeting a sashensa. Tsoro fal zuciyar Mamy kamar tace bazata je ba ita dai, sai dai bazata iya ba, dan koba komai tana matu ar jin kishirwar rashin ganin Abah na tsawon kwanaki. ALLAH ya jarabceta da son bawan ALLAHr nan kwarai da gaske. Zata iya yin komai akan Abah. Jiki a sanyaye ta kimtsa ta amsa kiran ita da Saheeba. Nuratu nason zuwa Mamyn ta hanata. Sanda suke shigowa kowa ya gama hallara. Abah ne kawai da Oum basu fito ba suna bedroom in Abahn. Ganin harda RK da Nuwaira abin ya tsayama Mamy a rai. Amma dai batace komai ba ta zauna. Nuwaira bata ta a damuwa da zuwa gaida Mamy ba a gidan, dan tunda RK ya bata wasu labarai akan Mamy taji ta tsani matar sosai. Haka family in Darma suke akwai kishin nasu. Akan an uwansu komai zasu iya maka suna son juna. Yanzu ma darajar su Babban Yaya dake a wajen taci Nuwaira ta gaisheta. RK ma dai ya gaisheta dan shi akwai iya taku, yanda Mamy ta iya fuska biyu shima baka isa sanin shike ullama Mamyn tsiyataku ta ashin asa ba. Suma su Maanal su Yaya Fawzan duk sun mata Barka da fitowa. Tadai danne duk tana amsawa fuska a sau e. A haka Abah da Oum suka sakko daga sama suna dariya. Daka gansu kasan baibaye suke da kwanciyar hankali da farin ciki, ga tarin aunar junansu da bata oyuwa a cikin idanunsu kida a gaban ayansu ne. Abu mai nauyi ya tsayama Mamy a ma oshi, haka dai ta danne sa da yar Hari Abah ya zauna Oum kuma ta zauna a kusa da ita tana gaisheta fuskarta da fara'a. Dannewa tai ta amsa, Saheeba ma da tunda ta shigo babu wanda ya kulata ta gaida Oum da Abah........ *_AJIYA A DUHU na ku i ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama *_BOOK 2_*
Chapter 111 · 0% Book details