Sashe 79
Ajiya A Duhu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
______________ ........Cike da tsokana RK ya ce, Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya auka fillo ya jefa masa. Cafewa RK in yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta kakkanni, nan fa su Oum suka shiga karesa suma. Anyi wasa anyi raha kafin a koma nasiha da gaba aya ta ta'alla a ne ga AA in, ta yanda zai zama mai ha uri akan mace, ta yanda zai yautata mata, ta yanda zai shagwa ata ya riritata, ya sauke ha okinta da yautatata mata. Ya tattala soyayyarsu kullum taita ara dan o a maimakon rauni da maza da yawa ke saka soyayyarsu yi saboda sakacin sauke ha in da suka dace akan iyalansu. Sun nuna masa muhimmancin sau ama mace saboda kasancewarmu masu rauni. Suka kuma tunasar da shi zaman aure zaman ibada ne ba zama irin na saurayi da budurwa ba, yanzu maganar akin soyayya da farautarta ya are. Lokacine na tabbatar da ita ta jaddadata domin ta ara nauyi a sikeli da dan o fiye da sufagilu. Ha uri da kura-kuran mata dan mu a karkace muke, wanda ya dage ko fariyyyar son ganin ya lan wasamu mun mi e to ya tabbata sai dai mu karye as. Dan haka ya kula yasan miya dace ga zaman auren, ya zama mai tausasawa sai yaci ribar zaman har yay nisan zangon kaiwa wasu shekarun da za'a ringa lissafi shekarun aurensu suma. Daga arshe aka rufe da addu'a mai tsaho da ratsa jiki, sannan aka sallame su dan zasuje sashen Abah su masa sallama da su Babban Yaya. Kasa tashi AA yayi, har sai da Oum ta mi e tana murmushi ta kamasa ta mi ar. Sai kawai ya rungumeta. Harga ALLAH zuciyarsa tai rauni, wai shima yau yayi aure za'a dan ashi ga matarsa ya bar Oum insa da yake manne da ita akoda yaushe, shike nan zai tashi daga saurayi ya koma magidanci. Da yar su RK da jikinsu yay sanyi suma suka janyesa. Dan soyayyar Oum da yaran nan uku musamman Ajwaad na ta a zukatan wannan Family in matu agosa Oum tayi ta share masa guntun hawayen sannan ta kamo hannun Modibbo ta dam a na AA a ciki, sai ta koma ta zauna tana ri e hawayenta itama. Yau finally ta aurar da autanta yaranta sun gama auren fari sai kuma ga masu burin arawa kamar yanda Fawzan yayi. Da yar su RK suka ja AA dake ta kallon Oum suka fita da shi. Sun wuce sashen Mamy, sai suka samu tana barci, anan ko maimakon AA ya samu fa a da nasiha kamar a sashen Mamy sai su Maman Saheeba suka ige da habaice-habaice. RK ne kawai ya fahimci inda suka dosa, sauran ko basu kawo komai a ransu ba sai shi AA in kansa. Dan haka baici komai ba ya mi e yay musu sai da safe ya barsu da ba in cikin sharesun da yay. Haka sukaita zage-zage da aibanta Oum da Maanal dama Darma Family gaba aya har Maanal da danginta basu tsira ba. Sashen Abah shine na uku, daga shi sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain da Hassan insa, anan ma nasiha mai ratsa jiki iyayen sukai masa. Tare da jadadada masa ha insa na miji akan matarsa. Sai dabaru na kula da mace ta yanda aure ke arko da ikon ALLAH. Daga arshe akai addu'a sannan suka taso, sai sashen Babban Yaya. Sun sameshi shi ka ai a falo zaune yana shan shayi yana kallon labarai. Kama AA yay ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Kafin ya agosa yana murmushi ya ri e masa fuska da hannaye biyu. Cike da ra a Babban Yaya ya ce, Finally yau Autan Oum ya mallaki Lilly na, zata maidashi babban mutum, nan da wata tara su haifa min yawawan yara masu kama da su Kunya sosai ta kama AA. Sai kawai ya sake rungume Babban Yaya hawaye na cika masa ido. Dariya babban yaya ya sake yi sauran na tayashi sannan ya zaunar da shi kusa da shi. Shima dai yayma AA nasiha da jadadda masa zama miji na gari a wajen Lilly. Ya rufe da addu'a mai arfi. Daga nan sashen Fawzan suka nufa, shi kam sai Nibras kawai suka samu a falo. Duk tayi wani wujiga-wujiga da alama kuma le ensu take ta window kafin su shigo. Bayan ta gaishesu cikin son danne kanta da yar RK yace ta kira musu Fawzan. Tana mi ewa ma sai gashi yana sakkowa daga sama. Yana zuwa ya rungume AA, cike da ra a yanda kowa baya ji ya ce, Oh oh yau fa Autan Oum zai shiga daga ciki. Babu dokar Aba a kansa Lilly zata dinga masa TAWAI Mintsininsa AA yayi, Yaya Fawzan ya ce, Ouch wane muguntane wanan haka Auta? Cike da sha iyanci AA yace, anwarka ta koya min Yanda yay maganar a fili ya sanya kowa dariya. Dan saika rantse bama shi yay zancen ba, babu wani fara'a a tare da shi. Yaya Fawzan yakai zaune yana fa in, Shike nan na yafe maka kaci albarkacin Lilly, zauna na maka nasiha dan bazan yarda da rashin mutuncin mijin anwa ba lallasaka zanyi idan kai mata ko kallon banza eh . Babu wanda bai dara ba yanzu ma. Kafin Fawzan yaci serious kamar ba shi ba ya fara ma AA nasiha shima, daga arshe suka rufe da addu'a sannan ya sallamesu. Koda AA yace shi bazai masa rakkiyar ba? Sai Fawzan yay shiru, sai da yaga kamar AA ya e fuska sannan ya mi e yace Muje ta ararre kawai. Yanzu dai zamu huta muma Lilly ta kwasa Lokacin da suke ficewa idon Fawzan ya sauka akan Nibras dake oye ashin bene tana kuka sosai. Kansa kawai ya girgiza yay gaba hannunsa ri e dana AA. Shima AA in sarai yaga Nibras in, amma ya basar kamar bai ganta ba. Sauran ko babu wanda ya lura sam.. Wani irin dadda amshi mai sanyaya zuciya da sauke gajiya ne ya fara musu sallama a falon, musamman ga AA daya fara shiga. Gaba aya falon ya auki wani irin yau mai ayatarwa daka kallesa ka san a lallai gidan amarya kazo. Duk zama su RK sukai kowa na sauke numfashi, dan ba aramin da amshin gidan yay musu ba. AA zai zauna Yaya Fawzan ya ce, A'a ango tashi kaje kazo mana da amarya muna nan an jimmm AA yayi, sai kuma ya mi e dan harga ALLAH soyay daga iya nan suyi sallama su koma shi ka ai yaje ga matarsa. Amma bazai iya ba yana jin nauyin Yaya Fawzan insa. Tsayawa yay a ofar akin ya zubama handle in ido na sakanni, dan Amaal ta tura masa text cewar Maanal in na nan asa. Sai kuma ya sauke numfashi a hankali sannan ya mur a handle in kamar baya so ya tura kai ciki da sallama asa- asa. Zuwa yanzu Maanal na kwance ne dan ta gaji da zaman, ga tsoro na shigarta haka kawai, ta kira Didi Amaal tace su dawo dan ALLAH tsoro take ji, shine tace mata ta daure na an lokaci ne gasu AA in nan shigowa. Tun tana kallon ofa harta zame ta kwanta idanunta a lumshe ta fa a tunanin duniya da nazarce-nazarcen ruguntsumin cikinta. A wannan yanayin taji an bu ofa, kafin ma ta nema ba'asin wanene sassanyan amshin turarensa ya shigo mata hanci duk da yanda nata ke tashi da wanda aka sanya ma akin ma. Luff tayi kamar mai barci tana arin saisaita numfashinta har ta fahimci isowarsa inda take ya tsaya cak. Shiru bata bu e idanun ba, yana daga tsaye shi kuma ya zubama yawar fuskarta da yake gani ka an raunanan idanunsa. Kallon fin minti guda sannan ya wani fusrzar da iska mai nauyi sakamakon saukar idanunsa akan ugunta daya wani bada shep ta hanyar fidda lafaffen cikinta zuwa cikar irji dana ugun dan lafayar mai kwantawa ce a jiki. Sannu a hankali kamar wanda baya so ya du o yana kai hannu ya yaye fuskarta da yau, cike da ra a ganin ta i bu e idanun ya furta, Amincin ALLAH ya tabbata a gareki Madam pretender Baki Manaal ta an cuna a karo na farko, amma still ta i bu e idannunta. A karo na farko yay murmushi ka an, sai kuma tunawa da ana jiransu yasa shi sake furzar da numfashin ya ce, I'm sorry drama queen. Ajiye shagwa an muje wajen su Yaya Fawzan mu dawo duk sai ki tattaro kiyi min harta shekara 8 da suka wuce da nayi missing duk zan auka a yau in nan koda ina fa uwa ina tashi ne Shiru nan ma tayi, sai dai ta bu e idannunta a hankali ta sauke a kansa, suka an zubama juna ido, sai kuma ta janye nata tana tashi zaunen a nutse. Taimaka mata yay batare daya janye nasa idanun ba ya mi ar da ita, sai kawai ya sanyata a jikinsa ya rungume. Alhamdullahi! Alhamdullahi! Alhamdullahi! ya jera har suka uku a jere yana sauke ajiyar zuciya. Cikin ra a ya sake fa in, Ya rabba nagode maka daka nuna min wannan rana, kai ne ka bani ita tun tana arama, ka jarabceni da ku ucewarta a ga ar dana gama sakankancewa, ka dawo min da ita a lokacin dana gama sallamawa na rasata, ka bani ita a randa na gama yarda tawa rayuwar ta are kenan gaba aya. Yau gashi ka shigo da ita a cikin gaba aya duniyata a ga ar da nake cikin matsanancin zumu agare, farin cikin kasancewar tamu. ALLAH kai mata albarka, ya rabbi ka tausasa min ita ta zame min mar'atussaliha. Ya rabbi ka arfafa min ita ta zama uwar ana jajurtacciya, ya rabbi kai mata rahama mara yanke wa, ka tsare min ita daga kowanne irin sharri na fili dana oye, ka baibaiyeta da alkairinka da rahamarka, asa ta zama mai koyi da Nana Khadijah, kasa ta zama mai koyi da Nana Ai'sha. asa ta zama mai koyi da Nana Hafsah. asa ta zama mai