Sashe 99
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe idanu ya yi bai ce mata komai ba, itama ba ta damu da sai ya ba ta amsa ba ta kai hannu gefen wuyansa ta ji shi rau ta yi raurau da idanu suka cika da hawaye, zazzabin nan ya takura masa kullum da shi yake wuni har kusan karfe goma, sai can dare zai sake shi daga gari ya waye kuma ya dawo masa sabo dal, abin na damun ta matuƙa har ta gaji da ba shi magani dan har Asibiti suka je jiya aka rubuto masa magani ta sayo masa. Tashi ta yi ta dauki roba mai ɗan girma ta shige banɗaki, ba ta jima ba sai ga ta ta fito da ruwa a ciki ta aje a gefen shi, towel ta dauko ta tsugunna ta kamo hannunsa ya kalle ta, turo baki ta yi ta ce "Tashi ka koma kan katifa zan danna ma jikin ko zai sauka."
Shi dai kawai da ido yake bin ta duk abin da ta faɗa, tashi ya yi suka iso kan katifar ta zaunar da shi ta soma ƙoƙarin cire masa rigar, ya saki jiki sai inda ta juya shi yana bin ta da kallo har ta cire rigar, towel ɗin ta jiƙa ta soma danna masa a jiki..
Sai da taji zafin jikin ya ragu ta aje ta nufi yin girki, shinkafa ta dauko ta haɗo da komai na buƙata ta fito waje ta soma ƙoƙarin ɗaura girki ganin rana ta tafi da faɗawa. Ana kiran Sallar Magaria ta zuba shinkafar ta rufe ta ci gaba da fifita wutar dan yau ma da gawayi take girki, tuni dama ta koma yin girki da gawayi ganin gas ya yi tsada sosai ga shi ita ba ta da wani ƙarfin da za ta ce dole lalle sai da shi za ta musu girki, sayan abinci da cefane ma kaɗai ya ishe ta ballantana sayan wani gas, dan dole ta haƙura ta sayo buhun gawayi take lamarin ta da shi. Abin da ya fi saka ta jin daɗi ma ganin ko ta tari hayaƙi babu wani abu da take ji, yanzu ko maganin ulcer ta daina sha saboda ba ta jin ciwon kamai ga shi ta soma murjewa ta yi fresh duk da damuwar da take ciki, hakan ya sa Maman Amal da ba ta gani ta kyalle yau rana da ta ga ta yi kwalliya ta fito ta dinga kallon ta tana murmushi. Abir da ta gaji da kallon ta ɓata fuska ta ce "Ni fa Wallahi Maman Amal sanin halina ne ba ki yi ba na tsani kallo ya yi yawa, in wani abu kike son faɗa ai sai ki faɗi ba wai kike ruƙo mun na mujiya ba, wannan ai sai ki sa na kasa sakin jikina."
Dariya Maman Amal ta yi tana zama kusa da Abir ta ce "Mayar da wuƙaƙen Jiddo ni fa kawai mamaki ne nake?"
Kallon mamakin me ta mata ita Kuma ta kuma sa dariya, ta muskuta kamar mai tsoron kar aji me za ta faɗa ta yi ƙasa da murya ta ce "Ke wai har yanzu ba ki gane me nake gani a jikinki ba?"
Abir da ta ƙagu taji me ta gane ta girgiza kai, murmushi ta kuma yi ta ce "Ke alƙur'an ciki ne gareki, ke kamar wata ƴar fari ba ki gano kina da ciki ba? Ba ki ga canjin da kika samu ba?" Ta faɗa tana ƴar dariya..
Kwalalo idanu waje Abir ta yi sai kuma itama ta yi dariya ba ta ce komai ba, dan tasan ita dai babu wani ciki da take da shi, Maman Amal kuwa ta yi ta tsokanar ta har Maman biyu ta sa mata ita kuma tana ta murmushi ganin matan gidan sun kama maganar Maman Amal da gaske...
Bayan ta gama Sallah ta zo ta ga abincin ya gama dafuwa ta sauke gefe, zama ta yi tana mamakin ganin Ta Sakkwato yau shuru ba ta dawo gidan ba, bayan an yi Sallar Isha'i ta janyo wayarta jin saƙonni na shigowa ta bude, customers ɗin ta daga Tiktok mutum uku suka yi mata DM suna son lalle, kowanne ya nuna mata kalar wanda za ta masa ta sanar da su ga kuɗin shi suka ce ba matsala sannan ta kwatanta musu Unguwarsu suka ce gobe bayan Asuhar za su zo, murmushi ta yi ta amsa da to sannan ta sauka. Har za ta sauka ta ci karo da labarin da ake yaɗawa na su Alhaji Mustapha, kwafa ta yi tana faɗin "Azzalumai in sha Allah dubunku ta kusa cika, Allah ya yi wa wannan bawan Allah albarka Damisa da ya binciko cutar da al'umma da kuke a karkashin ƙasa." Shuru ta yi can maganar 'yan ta'addan nan ta faɗo mata, jinjina kai ta yi tana fita daga Tiktok ɗin ta ce "Tabbas zan so na ga wannan mutumin mai suna Damisa da har ake danganta mijina da shi."
Saƙon Iman ta gani tana sanar da ita in ta ga saƙon ta kira ta akwai bayani, murmushi ta yi ta danna mata kira, ringing ɗaya ta dauka ko gaisawa ba su yi ba Iman ta soma faɗin "Anty Baby kin san kuwa yau me ya faru a family?"
Girgiza mata kai ta yi kamar tana ganin ta ita kuma ta É—aura da cewa "Wai yau Abba ya kirani yana ce min wai na ba shi number ki wannan."
Abir ta zaro idanu ta ce "To me zai yi da number ta kuma?"
"Hmm ke dai bari, ai yau na sha mamaki Abba ya tirke ni a waya yana ce min shi fa bai san yaushe suka miki aure ba, ni kuma abin ya ƙular da ni amma na danne na ce masa ai kuwa dai sun miki aure tun da jimawa, nan ya dinga ta mamaki da alhini ya ce na ba shi number ki na ce masa ni ma kaina neman ki nake dan an ce kin bi dare kin gudu daga ke har mijin naki an rasa inda kuke, shi ne fa naji duk ya rude ya ce min sai an jima Wallahi ya ba ni tausayi ba ki ga yadda ya shiga tashin hankali ba saboda video call muka yi da shi. "
Murmushi mai ciwo Abir ta yi tana tuna yadda Abba ke nuna masa so kamar zai mayar da ita cikinsa, goge hawayen da suka zubo mata ta yi ta ce "Kar ki ba su number ta dan bana son kowa ya san inda nake, zan ci gaba da rayuwa a nan ni da mijina cikin farin ciki da kwanciyar hankali dan da alama ma Zaiyan ya soma samun lafiya."
Dirkowa Iman ta yi daga kan gado tana washe baki kamar gonar auduga Ikilima da ke gefen ta ta kwashe da dariya, ta gyara wayar ta ce "Kai amma kuwa in har Zaiyan ya soma samu lafiya ina tayaki murna, amma to Anty Baby idan ya samu lafiya ya nuna bai san ki ba fa?Kuma kin ga ba ki san shi waye ba daga ina ya fito? Duk fa ba ki sani ba kila ma yana da mata har da yara, amma dai duk da haka gara ya samu lafiyar zai fi da zaman ci da kai da kike. "
Gaban ta ne ya faɗi rass! Ta dafe ƙirji ta ce" Kin ga in sha Allah ba shi da mata, kuma ina ji a jikina Zaiyan zai warke mu yi rayuwa kamar kowa. "
Jin ta yi maganar a fusace sai Iman ta fashe da dariya tana faÉ—in "Jinjinar ban girma zuwa gareki Anty Baby wannan fusata haka? Kila fa na ce ba tabbatarwa na yi ba, yanzu dai ba wannan ba Ikilima ta ce za ku yi magana ga ta nan za ta kwace wayar."
Sauke ajiyar zuciya ta yi ta a ba ta suka gaisa, Ikilima ke cewa ta yi kewar Abir matuƙa itama ta ce ta yi kewarta, sun jima suna hira sannan suka yi sallama..
Zubo musu abinci ta yi ta tashi Zaiyan ta dinga ba shi da kanta yana ci har ya koshi ta taimaka masa ya tashi ta raka shi banÉ—aki, ita kuma ta kasa cin abincin maganganun Iman sun tsaya mata a rai, janye kwanon abincin ta yi ta fito waje ta rafka tagumi hannu bibiyu...
Cikin dare wajan karfe uku na dare Zaiyan ya kasa kwanciya ya dinga juyi yana murƙususu kamar mai nakuɗa, can dai ciwon ya lafa ya kwanta yana huci..
Abir za ta juya ta ji ta gam an riƙe ta, da sauri ta buɗe idanu ta ga yadda jikinsa yake rawa har haƙoransa suna karo da juna, a ruɗe ta soma ƙoƙarin tashi dan ta rufe shi amma sam ta kasa samun damar haka. Waro idanu ta yi ganin abin da yake shirin aikata mata, tana son yin ihu amma ba ta so aji ta ta dinga zaro idanu numfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta, jin wani baƙon al'amari da ba ta taɓa jin shi ba tun da ta zo duniya ya sa bude baki da kyar tana fisgo numfashi ta ce "M.. Me.. Meye haka Zaiyan ka cikani ma..." Ba ta samu damar ƙarasa maganar ba sakamakon wani azabbaben zafi da ya ziyarce ta, haka ta dinga kai duka tana fisge-fisge kamar sabuwar kamu amma a banza...
Kiran Sallah akan kunnenta aka yi ta yunƙura za tashi ta kasa, juya kai take tana kiran sunan shi amma sam bai motsa ba kamar matacce, kuka ta sa wanda sautin muryarta ba ya fita sosai tana miƙa hannu tana tabo nashi hannun, gajiya ta yi ta yi lamo tana nishi kamar mai nakuda in ta rufe idanuwanta sai taji kanta na mugun sara mata, idan ta buɗe kuma tsoron ganin Zaiyan ya sa taji jikinta ya dauki rawa, ta ci kukan ta marar sauti har ta gaji jin kanta na neman rabewa gida biyu ta haƙura...