Sashe 32
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana juyowa ta ga mutum a bayan ta ya tsura mata idanu ta riƙe baki cike da takaici ta ce "Amma kai ko dai Abdullahi an yi futsararren yaro, yanzu ba na hana ka dinga haye min gado ba? To tashi maza sauka ka bar min ɗaki ka koma na uwarka Sa'ade in kuma da kuɗinka a ciki lokacin da za a sayi gadon sai ka faɗa naji dan na biyaka kayan ka." Ta faɗa tana kai masa duka da tasbahar hannunta. Ko ci kanki bai ce mata ba har ta yi faɗan ta ta gaji, lumshe idanu ya yi yana jin sa ba yadda ya saba jin kansa ba, a hankali ya miƙe ya shige banɗakin Grandma duk da faɗa da zagin da take masa kar ya shigar mata ya share ya shiga, bai jima ba ya fito inda ya ga Grandma ta bar ɗakin.
A palo ya sami Mommy ta yi tsaye tana danna waya, a nutse ya iso inda take ya tsaya yana kallon yadda take saurin duba contact har ta zo kan tashi ta danna masa kira, hannu ya sa ya zare wayar daga hannunta ta yi saurin juyowa sai ta ga shi ne. Ganin yanayin ta ya sa Abdul saurin kamo hannayenta ya shiga tambayar ta.
"Mom me ya faru?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Abdul, Abir ba lafiya yanzu haka jikinta ya yi mugun zafi, shi ne nake son kiran ka ashe ma kana nan."
A ruɗe yake kallon Mom wanda in ka kalle shi ba za ka ce ya shiga damuwa ba game da maganar, amma tashin hankalin da ya ziyarce shi har wani dishi-dishi yake gani hakan yasa ya lumshe idanuwansa zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, buɗe idanu ya yi har Mommy ta cire ran zai ce wani abu ya ja numfashi sannan ya ce "Mom bari na dawo daga Masallaci zan kira Hashim ya turo a duba ta." Ya faɗa yana sakin hannun Mom. To kawai Mom ta ce ta nufi ɗakin Abir cike da damuwa, a ƙudundine ta same ta cikin bargo sai ƙyarma jikinta yake, ta yi hanzari isa bakin gadon ta yaye bargon. Waro idanu ta yi ganin yadda numfashinta ke fita da sauri-sauri ta miƙe ta fita zuwa kitchen, ruwa mai sanyi ta zubo a roba ta ɗauko ɗan ƙaramin towel ta dawo ɗakin. Sakawa ta yi a ciki ta matse ta ɗaura mata a goshi tana ɗan dannawa kaɗan-kaɗan, ta dinga ɗauko ruwan mai sanyi sosai tana goge mata fuska har zuwa ƙirjinta. Haka ta dinga yi tana yi tana kallon lokaci..
Da ƙyar ya nutsu ya yi Sallah gabaɗaya hankalinsa na can wajan ta har ya ƙagara a gama Sallar, bayan an salamce ya yi addu'oi sannan ya fito yana sanya hannu a aljihunsa ya fito da wayarsa IPhone sabuwa dal, number Doctor Hashim ya lalibo ya danna mata kira ringing ɗaya ya ɗauka tare da yi masa Allah ya amsa suka gaisa.
"Aboki yaya dai? Fatan dai lafiya?"
Sai da ya buÉ—e mota ya shiga ya mata key tukun ya magantu, "Hashim please ka turo a duba min Baby zazzabi ya rufe ta." Ya faÉ—a yana jin kamar ya sa kuka saboda sanin irin zazzabin da take wanda in ya kwantar da ita kamar ba za ta rayu ba..
"Subhanallahi! To shi kenan zan tura a duba ta yanzu."
OK kawai ya ce ya kashe kiran ya ƙaraso gida, cikin sanyin jiki ya buɗe motar ya fito ya shige ciki. Daret ɗakinta inda ya samu Mom ta gama shafe mata jiki tana lullube ta, ƙarasowa ya yi ya zauna a bakin gadon Mommy ta dube shi ta ce "Yawwa zo zauna ni zan je na yi Sallah kafin likitan ya zo."
Jinjina mata kai ya yi ta fita, buɗe bargon ya yi ya ƙura mata idanu, sosai ta ƙara haske ta yi wata irin rama kamar ta yi wata a kwance, hannunsa ya ɗaura a gefen wuyanta ya ji har yanzu akwai zafi sosai, ji yake kamar ya mayar da cutar jikinsa saboda tsananin tausaya mata da yake. Wani irin dogon numfashi ya sauke ya shafo cute beauty face ɗin ta, ɗan ƙaramin bakinta da yake sheƙi ya zuba wa idanu yana jin wani lakar yanayi, sake shafo kumatunta ya yi cikin daddadar muryarsa ya shiga tashin ta. "Baby open eyes." Ya faɗa cikin raɗa-raɗa tare da ɗago da ita ya jingina ta da jikin gadon.
Turo baki ta yi ta ƙara lafewa cikin bargon tana jin wani mugun sanyi na shigar ta, a hankali ta soma buɗe idanuwanta tana yi yana saɓa baki gaf take da sakin kuka, sai da ta gama buɗe idanunta tarr a kan shi ta dinga kallon shi ba ko ƙiftawa. Iska ya hura mata ta yi saurin rufe idanu ta turo baki sai ga hawaye sun zubo, saurin matso da ita ya yi cikin tsananin kulawa ya sa hannu ya goge mata hawayen. Jin wani kalar azababben ciwo da ķanta yake ta saki kuka tana kallon shi, dama yasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, a banza ma tana kuka ballantana yau kuma jiki ba lafiya sai ya yi murmushi ya buɗe mata hannu tare da cewa "Oya come here."
Saurin faɗawa ta yi jikinsa tana ci gaba da kuka, ji ya yi kamar an raɓa masa wani abu mai mugun zafi ya lumshe idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya, ƙara gyara mata kwanciya ya yi bai ce da ita komai ba yana jin yadda kukan ta ke hana shi sukoni. Suna a haka ya ji ƙaran wayarsa, hannu ɗaya ya sa a aljihunsa ya ciro wayar ya ga Doctor Hashim ne ke kira ya ɗauka tare da karawa a kunne, sanar da shi ya yi mai duba ta ta riga ta iso ya ce to ya ce mata ta shigo sannan ya kashe.
Suna a haka sai ga Mommy ta shigo tare da Nurse ɗin da ta zo, tana ganin ta ta ƙara ƙanƙame shi tana ƙyarma ta ce "Y.. Ya.. Ya. Kar ka bari ta min allura please." Ta faɗa cikin rawar murya. Shafa kanta ya yi cikin sigar rarrashi ya ɗago da fuskarta ya share mata hawayen ya ce "My Baby ki tsaya a duba ki, ba ki so ki samu lafiya ne?" Ya faɗa yana zaunar da ita a gefen shi. Girgiza kai ta yi ta ma kasa maganar, Mommy ta girgiza kai ta ce "Raguwa kawai, ke kullum in za a miki allura sai ki rikice kamar kin ga wani mugun abu." Tana gama faɗin haka ta fita ta bar musu ɗakin.
Nurse ta ƙaraso ta soma duba ta, bayan ta gama ta ɗauko allura tana murmushi ta ce "Sister gyara a miki allura."
Saurin ja da baya ta yi ta koma bayan Abdul shi kuma ganin haka yasa ya janyo ta tare matse ta aka tsira mata allura, ai kuwa ta kwalla ƙara tana ƙoƙarin kwace jikinta ya ƙara matse ta yana faɗin "Please tsaya mana kar ki yi mutsi a miki a inda ba daidai ba."
Sai da aka mata biyu sannan ta rubuta mata maganguna ta ce "Ranke ya daɗe a sayo mata waɗannan magungunan." Ta miƙa masa paper da ta rubuta maganin ta musu sallama ta tafi.. Zuba mata idanu ya yi ganin yadda ta ɓata masa gaban riga da majina da yawu, girgiza kai ya yi ya ɗago ta ya kama hannun da aka mata allurar ya soma shafa mata wanjan yana faɗin "Sannu my baby."
Harara ta aika masa lokaci É—aya ta tashi daga jikinsa tana kumbura baki, haushin sa ya cika ta sai harara take masa kamar shi ne ya mata allurar, tsakiyar gadon ta isa ta kwanta tana turo baki ta ce "Ni ka bani ruwa na sha." Ta faÉ—a tana kuka. Dariya ta so ba shi amma da yake shi bai cika yin dariya ba sai kawai ya yi murmushi ya tashi ya kawo mata ruwan, sai da ta banka masa harara kana ta amsa ta dinga sha har da lumshe idanu. Ganin za ta sha ya mata illa ya karbe yana faÉ—in "Ya isa haka ruwan bari Mommy ta kawo miki ko da tea ne ki sha." Kawar da kai ta yi tana hura hanci dan ita har ga Allah ba ta so ya hana ta shan ruwan ba, Mommy ta kawo mata farfesu shi kuma ya matsa Mommy ta zauna ya ce "Mom zan fita ina so zan koma office akwai wani kes da aka kira ni na wasu mutane." Murmushi Mommy ta yi ta ce "To Allah ya bada nasara Ubangiji ya tsare gaban ka da bayan ka."
Cikin jin daÉ—in addu'ar ya ce "Amin My Mom." Ya sa kai zai bar É—akin sai kuma ya juyo ya ce "Baby me kike so na dawo miki da shi."
"Ni ai fushi nake ma da kai." Ta faɗa tana amsar tea ɗin da Mommy ke miƙa mata.
"Kin ga ki aje fushin nan in na dawo sai mu yi magana."
"To ka sayo min ice cream. "
OK ya ce mata sannan ya tafi..
Alhaji da su Jarmai bayan sun samu wannan makudan kuɗin suka shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar party a gidan gonar su shi da tawagar su, sosai suka yi shagali suka ya sa aka ɗauko yan mata uku daga cikin wanda suka ɗauko..
Yan matan da ba za su wuce shekaru 17 ba aka kawo gaban su aka aje musu su, su kuma suna ta kuka Alhaji ya miƙe yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya har ya zo kan wata ɓaka yar duma-duma, wani irin lashe lips ya yi yana mata kallon ƙurulla ya kai hannu ya taɓo ƙirjinta yana murmishi ya ce "Sweet girl ta so ki zo nan."
Ya faɗa yana nuna mata inda yake tsaye. Jikinta na rawa ta miƙe sai kuka take ta iso gaban shi ta durƙusa ta ce "Don Allah kar ka kasheni Alhaji, duk abin da kake so ka yi da ni amma kar ka kashe ni." Ta ƙarashe maganar tana rufe bakinta gudun sautin kukan ta ya fito..