Sashe 81
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka suka mayar wa da kowa abin da suka amsa, suna tsaye mai mota ya ƙarasa kulla ƙusa kowa ya shiga suka tayar da motar a guje suka bar dajin. Su kuwa su Bangis jikin su a sanyaye suka kutsa kai cikin dajin suna ta mamakin yadda aka yi Damisa ya shiga motar haya..
Tun da suka kama hanya ba wanda ya yi magana sai Ta Sakkwato da ke yi wa Zaiyan godiya, shi kuma tuni wani baccin ya sake yin gaba da shi.
Sai tara na dare suka iso Kano, sai a lokacin Abir ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ganin ta a cikin gari. Sauke su aka yi Direba sai da ya ga Abir ta sauko ya ja su gefe ya ce "Hajiya yanzu daga nan ina za ki je in haÉ—a ki da wanda suka san gari?"
Sunkuyar da kai ta yi tana riƙe hannun Zaiyan ta ce "Ban san ina za mu je ba ni ma, amma dai ina neman gidan haya."
Ta Sakkwato da ta iso wajan ta ji abin da take faÉ—a ta ce "Indai gidan haya kike so to ki biyo mu akwai É—aki da palo da toilet wanda ba a kama ba."
Shuru Abir ta yi tana tunanin wai yau ita ce za ta zauna a gidan haya, gidan ma wai É—aki É—aya da palo, ganin dai ba ta da wata dabara ta amince za ta bi Ta Sakkwato da mijinta su tafi, godiya ta masa ta ba shi kuÉ—in motarsa ya fito musu da kayan su suka tafi.. Wata motar suka dauka ta kai su har unguwar Rijiyar zaki kofar wani gida, tun da suka fito suke jin tashin kiÉ—a a ciki haka suka biya mai mota suka nufi ciki shi kuma Mijin Ta Sakkwato ya wuce bai shiga gidan ba..
Mata ne jere sun fi ashirin suna cashewa wasu kuma na zaune suna sha'anin gaban su sun cika gidan, wata daga cikin matan ce ta hango Ta Sakkwato da ta washe baki tana fadin "Ga Ta Sakkwato! Ga Ta Sakkwato! Maman Amal Ta Sakkwato ta dawo." Ta faÉ—a tana isowa gaban su. Saurin buya Zaiyan ya yi a bayan Abir ya kwanta a bayanta, murmushi kawai ta yi ta fuskanci matar ganin suna gaisawa da Ta Sakkwato.
"A a, Ta Sakkwato baƙuwa kika tafo mana da ita ba?" Ta faɗa tana kallon Abir da itama ita take kallo fuska dauke da murmushi. Dariya Ta Sakkwato ta yi ta dafa kafaɗar Abir ta ce "Wallahi fa Maman Amina baƙuwa ta nai za ta kama haya a wancan ɗakin da ya rage."
Dariya Maman Amina ta yi tana yi wa Abir sannu da zuwa ta amsa tana murmushi, Ta Sakkwato ta ja Abir da kayan su suka nufi wani ɗaki da ke kusan na karshe a dakunan ta ja birki ta tsaya. Kashe Dijan suka yi wani mai shigar jallabiya milk color ya ɗane hannu yana rataya jaka da kafaɗa ya tattare rigarsa daga kasa ya riƙe ya yo wajan su Abir, ya sha fauda da janbaki sau wani yauƙi yake yana taku ɗaiɗai..
Baki Abir ta saki tana kallon ikon Allah ganin namiji da kwalliya yana taunar cingam sai murguɗa mazaunai yake ga ba wani jiki gareshi ba. Yana isowa ya kalli Abir yana wani waƙine baki ya zagaya su tukun ya dawo gaban su ya riƙe ƙugu, tafi ya yi yana buga cinya ya ce "Chass Wallahi, Ta Sakkwato wannan ƴar shawalwalar tarwaɗar fa? Gaskiya ta yi kalar madara a ina kika samo ta?" Ya faɗa yana ƙara yin dariya ya juyo ya kalli matan ya kuma cewa "Jama'a taro ya tashi aci abinci a tafi gida ga Ta Sakkwato ta iso, kun ga kuwa ai in mai guri ya zo dole ne mai tabarma ya naɗe ko ba ya so." Ya kuma sa hewa suka tafa da wani saurayi da ya iso wajan..
Ta Sakkwato ta ƙara jin kanta a sama ta kalle shi tana wani ciccin magani ta ce "Ladidi minana aka yi a gidan ga da daren nan an kunna kiɗa?"
"Hehehe sawa, wai kin manta da Samira É—iyar Maman Samira jiya aka kai ta dakin mijinta?"
Riƙe baki Ta Sakkwato ta yi tana gyada kai ta ce "E kuma fa haka ne, ina Tabadawa?"
Sai da suka yi shewa sannan suka sanar da ita ta je wajan biki itama, ba ta sake ce musu komai ba ta shiga dakin su Abir suka bi bayan ta, sosai Abir take mamakin wannan saurayi mai suna Ladidi..
Komai ta nuna mata ta buɗe ɗakinta ta fito da wata ƙaramar katifa yar madaidaiciya ta kawo ɗakin, komawa ta yi ta kuma dauko tabarma babba ta kawo tana murmushi ta ce "Ki shinhiɗa wagga Katifa da tabarma ku kwanta kafin ki sayo, dakin a gyare yake."
Murmushi Abir ta yi tana jin daɗin karamcin Ta Sakkwato, a nutse ta ce "Hajiya na gode matuƙa da wannan karamcin, idan Allah ya kai mu ki kaini kasuwa na sayo kayan amfani, amma yanzu a ina zan samu abinci mu saya yunwa muke ji ni da Mijina."
Murmushi ta yi ta kalli Zaiyan da yake wasa da gashin kan Abir, kasa daurewa dai ta yi ta ce " Wai ki na nuhin wagga mijinki na?"
Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi ta ce "E mijina ne shi ba shi da lafiya ne." Tashi tsaye ta yi ta leƙo ta kira Ladidi ya iso ɗakin da sauri yana dafe kirji wannan karon ya ɗaura zani a samar kayan, wani kalar maƙale hannu ya yi yana rausayar da kai ya ce "Haba Hajiya wannan kira haka ai sai ki yi wa masoyina asara, tsakani da Allah muna can muna zuba soyayya sai ki kwalla min wannan kira kamar Maigadin gidanki?"
Tsaki Ta Sakkwato ta yi tana hararar Ladidi ta ce "Dalla can gafara! Ni ba wani ɗumi na ce ka yi min ba ka amshi kuɗi ka sayo wa baƙuwa abinci dan nasan ba lalle yau kun yi ba." Ta faɗa tana kallon Abir ta miƙa mata hannu ta ce "Minana sunanki yarinyar ga?"
Jim ta yi tana tunanin wani suna za ta ce, can dai ta kalle ta ta ce "Sunana Jiddo."
"Ahayye ayiriri nanaye Allah na dawo in ji ɗan yawon duniya caɓas! Wallahi ana yi ina jin sugar ke ban mu tafa Jiddo wannan suna naki yi ya zau kamar Maggi Onga a miyar kuka Chass ni Ladidi." Ya ƙarashe maganar yana miƙa wa Abir hannu.
A kufule Ta Sakkwato ta ce "Ni Ladidi daÉ—i na da ke shisshigi, meye na wani cewa ta ba ki hannu?"
Baki ya riƙe yana fadin "To fa ikon Allah na kwance ya tashi! Hajiya daga harkar arziki sai cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa? To kin ga Jiddo ba ni kuɗi na sayo muku abinci kar Hajiya ta yi min ƙazafi."
Murmushi Abir ta yi dan ita a iya rayuwarta ba ta taɓa ganin ɗan Daudu ba eyes to eyes sai yau, kuɗin ta ba shi dubu biyar ta ce ya sayo mata har da karton ruwa na gora mai sanyi, juyi Ladidi ya yi ya dauko shoki ya dire tare da cewa "Wannan kuɗin na abicin ne ki kawo na ruwan."
Dubu biyar ta ƙara masa ta ce ya sayo mata komai kuma ya yi sauri mijinta kar ya yi bacci, shewa ya yi sannan ya fita. Kama baki Abir ta yi tana bin kofar da kallo, tashi ta yi ta shinfiɗa katifar ita kuma tabarmar ta shinfiɗa a gaban katifar.
Tashi ta yi yana biye da ita suka shiga bandaki, wani irin wani ne ya bigi hancinta ta yi saurin matsewa tana yowa baya, sai da ta jima sannan ta ja shi ta shiga tana done hanci kamar za ta yi amai haka dai ta daure ta yi alwala shi ma ta masa suka fito.
Kayan su ta buɗe ta canja wani ta sa hibaji sai ta kasa bambance ina ne ƙibila, leƙowa ta yi ta ga Ta Sakkwato na ta sababi ta tambaye ta ina ne ƙibila ta nuna mata tukun ta koma ciki..
Bayan ta gama sallolin ta tana zaune sai ga Ladidi da kaya, sannu ta masa ya amsa ya miƙa mata abinci da ruwan tare da ba ta sauran canji, godiya ta masa ya tafi..
Abincin ta aje musu amma fir Zaiyan yaƙi cin abicin sai ya kwanta a cinyarta, sosai abin ya dame ta ganin yau ba su ci komai ba tun safe sai yanzu amma ya ce yaƙi ci, haka dai ta ci kaɗan ta rufe.
Wayarta ta dauko ta buɗe nan da nan kiran da aka mata wayar na kashe ya dinga nuna mata, Baba ya mata kira ya fi goma, Hafsat ta mata kira 6, Iman 4 sai Suhal da ya mata biyu. Duddubawa take ko za ta ga na Abdul amma ba ta gani ba sai sabon text message da ya turo mata wanda tana shiga ta ga yadda aiko mata munannan kalamai wanda wasu ƙwaƙwalwarta ta kasa ɗaukan su sai share hawaye take, na ƙarshe har da barazanar zai ce ta yi kisan kai. Ta zaro idanu tana fita a number. Ba wanda ta yi gangancin kira ko yi masa reply ta kashe wayar ta tashi Zaiyan daga kan cinyarta suka nufi ɗaki, haka ta dinga juyi tana kuka bacci ya kaurace wa idanuwamta....
_Maman Nusaiba ce_
[11/20, 10:13 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na (40)
Kiran Sallar assalatu ne ya tayar da Abir daga baccin da ya shure ta, a hankali ta buɗe idanuwanta ta yunƙura za ta tashi ta ji ya kanannaɗe ta, idanu ta zuba masa tana kallon kyakkyawar fuskarsa mai kewaye da baƙin saje, hannu ta kai ta shafa fuskar tana ɗan bubbugawa ko zai tashi. Juyi ya yi a kanta ya gyara kwanciya yana ƙara matse ta kamar ya samu pilo, runtse idanu ta yi jin zafi ta sa hannu ta soma ƙoƙarin ɓamɓare shi daga jikinta amma ta kasa, mintsinin shi ta yi a wuya ya buɗe idanunsa tar a kanta, turo baki ta yi tana faɗin "Ka tashi mana mu yi Sallah an fa kira."