Sashe 55
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muna tsaye a bakin ƙofar ɗakin da aka shigar da ita ni da Abban ta duk hankalin mu a tashe, sai da suka kwashe minti talatin kafin aka buɗe ƙofar, da sauri muka nufi likita muna tambayar shi jikin Abir wanda ya kasance uba ne ga Doctor Hashim. Cewa ya yi mu bi shi office ɗin shi, Kamar na shiga ɗakin amma haka na haƙura muka rankaya zuwa office ɗin sa. Bayan ya gama rubuce-rubuce ya soma mana bayanin abin da ke damun ta.
"Alhaji gaskiyar magana yarinyar ku ta kamu da cutar asma, yanzu ma abin da ya tayar mata da cutar hayaƙi ta shaƙa shi ne musabbabin ganin ta a haka. Amma ku kwantar da hankalin ku in sha Allah za ta samu lafiya zan ɗaura ta a kan wani magani wanda in ciwon ya taso mata za ta shaƙa shi, sannan zan ba ku ƙwayoyi ta yadda zai dinga kawar da cutar a hankali har ta warke."
Tashin hankalin da muka shiga ba shi da iyaka na yi ta kuka saboda ita kaɗai na haifa da zan kalla na ji sanyi irin yadda kowacce mace ke ji in ta kalli ɗanta. Bayan ba mu shawarwari da magunguna ya ce za mu iya ganin ta ƙila ma ta farfaɗo, ni ce a gaba na riga shi shiga inda na hango ta zaune a kan gadon tana ta kallon ɗakin, ganina ya sa ta dinga kiran sunana tana cewa "Mom nan ɗin ina ne?"
Rungume ta na yi ina kuka Likita ya zo ya cire mata allurar ƙarin ruwan da ya sa mata ta ƙare, ya rubuta mana sallama muka dawo gida..
Tun daga ranar na ƙara sa idanu akan ta bana bari ta je inda ake tashin ƙura ko ta yi gudu, hakan ya sa har ta yi shekara ciwon bai taɓa tashi ba hakan ya yi min daɗi. Ba wanda ya san tana da ciwon a lokacin har kai kanka sai wata rana Abban Abir ke sanar da Kabir da Sulaiman, ban san ya aka yi ba su Farida suka ji maganar ba washegari kamar haɗin baki Hajiyar Baraka ta zo ita da babban ɗanta wanda sai a watan da ya gabata na san shi ne Daddyn Aruf, wanda shi bai yo halin Hajiyar su ba mutum ne mai kirki. Bayan mun gaisa yake sanar da ni matarsa na gaishe ni na ce ina masawa na tambayi Aruf ya ce yana nan lafiya sannan ya min sallama ya tafi. Sai da suka ga ya tafi Hajiya na ta soma zazzagina, ban ce da ita komai har ta zauna naje kitchen na kawo mata lemo mai sanyi da ruwa na aje a gaban ta ina kawar da ɓacin raina na ce "Hajiya sannu da zuwa ga ruwa ki jiƙa maƙoshinki kafin na ƙarasa girki."
Kallon banza ta mini tana yatsina fuska ta buɗe mayafinta tana kaɗa ƙafa ta ce "Kin ga alama yunwa a tare da ni? Ko an faɗa miki ni dangin matsiyata ce da har zan so na ci abincinki wanda ki ka gama barbaɗe shi da guba na ci? To ki kama kanki ƴar matsiyata kawai, kuma Wallahi sai na sa Ibrahim ya sake ki ya auri ƙanwar sa Ilham dan mun gaji da zaman ki a gidan nan bakya haihuwa, sai dai ki ci ki sha ki yi kashi amma ba a iya haihuwa na. Tun da kika haifi wannan ƴar taki mai suffar mayu ba ki sake haihuwa ba, ko da yake ita ɗin ma sunan tana raye ne tun da farfaɗiya take, kin ga kuwa ko ta girma babu wanda zai auri mai cutar hauka da sunan matarsa, dan haka dole ma ki bar gidan nan ko kina so ko bakya so sai kin koma inda kika fito kin mallake mana ɗa sai yadda ki ka yi da shi, har su iyayen nasa kin mallake su to ni da yake a tsaye nake a kan ƙafafuna na gagare ki, shi ya sa duk abin da na ce wa Yaya a kanki ba ya yarda sai ya ce na cika ƙorafi, Allah dai ya raba mu da dangin jaraba 'yan anace."
Hawayen da suka cika idanu ne suka zubo na yi saurin miƙewa ina kawar da kaina gefe dan kar su gani, sai dai ina Baraka ta gani ai kuwa ta sheƙe da dariya tana cewa "Wallahi kuwa Mama ai sai dai mutum zuciyarsa ta buga ya mutu saboda kishi, amma ƙanwata sai ta shigo gidan nan a matsayin matar Yaya Ibrahim. In kuma ƙawar ki za ki nemo ta aure shi kamar yadda kika aurawa Kabir wannan mummunar to sai ki soma kira ta ki faɗa mata. " Tana gama faɗin haka ta wuce dan dama Hajiyar tun da ta faɗa min baƙaƙen maganganu ta bar palon. Damƙo ta na yi ta yo baya ina huci na zabga mata mari mai shiga jiki na nuna da yatsa na ce "Ai da Ibrahim ya auri ƴar tasha gara na aura masa ƙawar tawa, tun da ita mutuniyar kirki ce ba irin ku ba masu bin bokaye da aikata saɓon Allah, kuma maganar na aurawa Kabir ƙawata waye ya ce miki ƙawata ce ita?"
Cikin jin zafin marin ta ce. "Ban sani ba yar wahala, ƙawar ki ce mana Kabir ya faɗa min ke ki ka ce ya auri ƙawar ki ba wani son ta yake ba kawai rabon Abdul ne."
Sake ɗaga hannu na yi zan ƙara mata wani marin naji an riƙe hannunna na juyo a fusace dan a lokacin ina jin komai ba zan iya yi saboda na kai maƙura, kallo na ya yi yana sauke hannuna ƙasa ya ce "Haba Sadiya me ya yi zafi haka ke da kike da mutumcin ki za ki biya marar sa daraja kuke faɗa?."
Ajiyar na sauke na sunkuyar da kaina na fashe da kuka ita kuma Baraka ta tafi riƙe da kunci tana zagina, ruwa mai sanyi ya ba ni na sha sannan naji sanyi a zuciyata, nan ya tambaye ni abin da ya haɗa mu na faɗa masa komai. Tashi ya yi tsaye dan dama shi mutum ne mai fusata kamar kai, ban san me ya faru fa ba dai sai kiran Inna na gani na dauka ta dinga ba ni hakuri akan abin da Hajiya ta mini na ce ba komai...
Haka muka ci gaba da rayuwa ina ta addu'a Allah ya ba ni ciki ko dan gorin da suke min, amma ban samu ba..."
Katse Mom Abdul ya yi ya ce "To amma Mom ya aka yi har tsayin lokacin nan Umma ba ta san Mamana sister É—in ki ba ce ? , kuma na ga a baya da kika yi rayuwar ki ba a kiran ki da Sadiya ko me ya sa?"
Numfashi ta sauke tana murmushi ta ce "Abin da ya sa ba a kira na da Sadiya saboda sunan Mahaifiyar Baba ne, shi ne Mama ke kira na da Hassana sunan tagwaitaka ta, ita kuma Baraka Kabir ne ya ce mata mamanka ƙawata ce saboda ta tsaneni dan ita ba girman nan ba ce a wajan Yasira ta girma ba ta shiga mutane sai girman kai, shi y sa ko wani abu aka yi a familyn ku ba ta sani kuma ko daga baya ta ji b ta damuwa, hakan ya sa wai dan ta ƙuntata min ta dage sai an ba ta kai ta riƙe ka wai kar na goga maka baƙin jini irin nawa. Da farko ya ce mata sam ba zai iya tunkara ta ba ya ce na ba shi kai zai bai wa matarsa ta ci gaba da ruƙon ka, amma fir ta tashi masifa kullum sai ta zo a part ɗi na ta min tatas ta uwa ta uba, wani lokacin ma sai ta kama sunan iyayena yake zagi amma na rabu da ita ta zageni ta gaji ta koma gidanta. Ni kuma ganin hakan na tattara ka na kai mata na ce ga ka nan amana, idan ta yi da kyau za ta gani ta faɗa min baƙar magana na kyale ta na wucewa ta.
Wata rana kwatsam da Asuba Inna ta kira Kabir ta sanar da shi Daddy ya rasu, haka muka tattara muka tafi Kano wajan mutuwa. Muna zuwa na sulale na tafi gidan Baba Malam in da na same shi ba yadda yake, sana'ar da yake jarin ya ƙare ko fita waje ba ya yi da kyar suke samu suna ci, na yi kuka ina cewa Baba Malam "Baba kenan yanzu ba ka dauke ni a matsayin ƴar da ka haifa ba? Me ya sa ba ka sanar da ni ba halin da kake ciki Baba?"
Haƙuri ya ba ni ya ce baya so ya tayar min da hankali ne shi ya sa, haka na wuni a gidan na sa aka sayo buhun shinkafa da duk abin da za su buƙata aka kawo musu gidan dan a lokacin ina busyness ɗin sayar da kayan kitchen..
Bayan an yi sadakar bakwai su Kabir suka tattara Inna suka ce ta dawo kusa da su, da farko ta ƙi yarda ta ce rugar su za ta koma wajan 'yan'uwanta suka ƙi amincewa dole ta haƙura muka tafi Yola da ita. Bayan mun je na samu Abban Abir na sanar da shi halin da Baba Malam yake ciki, inda ya nuna bai ji daɗi ba da ban faɗa masa ba tun muna Kano, na ba shi haƙuri ya ce zai gani zai yi wani abu na masa godiya dan duk Nigeria ba ni da wanda ya kai Baba Malam..
Bayan kwana biyu da maganar sai ya ce na shirya zai kai ni wani waje na shirya ni da kai da Abir in za ka iya tunawa lokacin da muka je wani gida a nan muka samu Baba Malam da iyalansa. "
Gyaɗa kai Abdul ya yi yana ƙara riƙe hannun Mom, tari ta dinga yi suna mata sannu har ya tsaya sannan ta ci gaba..