Sashe 67
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dariya ce ta so subce masa ganin yadda jikinta ke kyarma, a nutse ya sa ɗayan hannun ya ƙaraso da ita ya manne ta da jikinsa. Ajiyar zuciya ta sauke jin ɗumin jikinsa haɗi da ƙamshin turare wanda ta shaƙa lokacin da suka dira Kasar, kanshi ya kwanto a kafaɗarta yana shaƙar ƙamshin jikinta. Shuru ta yi tana jin zuciyarta na narkewa saboda yadda ta tsinci kanta a sabon yanayin da ba ta taɓa ji ba, sakin ta ya yi yana jan mumfashi ya juyo da ita suka yi facing ɗin juna tare da ɗago da fuskarta ya ƙura mata na mujiya..
Turo baki ta yi ganin yadda ya tsare ta da kallo, harara ta aika masa duk da tsoron da take ji ta kwace fuskarta tana riƙe ƙugu ta ce "Kai ni fa ƴar iska ba ce da kake wani shafe min jiki, anya ma kai ba ɗan mafiya ba ne?" Ta faɗa tana kaɗa ƙugu irin ba ta san rainin nan..
Murmushi ya yi yana kallon yadda ta turo baki ya lumshe idanu a kasale, matsalar auren kwaila kenan ba ta aje komai ba sai rashin kunya da son girma. Buɗe idanuwansa ya yi ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce "Ƴar kwailata."
Haushi ne ya kama ta jin ya ce mata Æ´ar kwaila ta sake aiko masa harara, kwafa ta yi ta ce "Ni ce ma kwailar?" Ta faÉ—a tana nuna kanta..
Gira ɗaya ya ɗage mata alamar tabbatarwa, hanci ta shiga hurawa tana tsaye a gaban shi sai murmushi yake mata, sai da ta gaji da tsayuwar ta ɗan ɓata fuska ta ce "Kamar ba a san darajar baƙo ba an bar ni a tsaye, salon man ƙwafrina ya ƙame."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ai kin fi ƙarfin baƙuwa Imani nan duk naki ne ki shiga duk inda kike so babu wanda zai miki shamaki." Ya faɗa yana kama hannunta suka nufi ɗaya daga cikin ɗakunan. Tana saka ƙafa ta shaƙi wani ni'imtaccan ƙamshi mai kwantar da hankali ta ja numfashi tare da lumshe idanu, sosai ƙamshin ɗakin ya tafi da imaninta har ba ta san sun ƙaraso bakin gadon ba sai da ta ji ya zaunar da ita, saurin buɗe idanu ta yi tana murguɗa masa baki ta ce "Wa ya ce ka zaunar da ni?" Ta faɗa tana kafe shi da idanu. Bai kula ta ba ya wuce daga ɗakin, bai jima ba ya dawo da abinci mai rai da lafiya sai ƙamshi yake tashi, tsohuwar yunwar da take ji tun safe ta taso mata ganin abincin. Zama ya yi a kan carpet ɗin ɗakin ya dube ta tare da cewa "Sauko ki ci abinci."
Ba ta musa ba ta sauko ta zauna a ɗan nesa da shi dan kar ma ya ce zai taɓa mata jiki ita kuma tsoro take ji, girgiza kai kawai ya yi sai ya tura mata abincin ya miƙe tsaye ya nufi can jikin gadon. Da wutsiyar ido take kallon shi dan ta ga me zai yi, da sauri ta mayar da kanta kasa tana gwalalo idanu waje ganin ya cire kayan jikinsa daga shi sai ƙaramin wando iya gwiwa, hannu ta kai ta dafe ƙirji tana jinjina rashin kunya irin ta Suhal wai yau a gaban ta yake cire kaya ko irin ya shiga toilet sai ya fidda a can..
Duk abin da take yana kallon ta ya yi murmushin sa wanda yake ƙara masa kyau ya shige toilet..
Da sauri ta shiga cin abinci dan ba ta so ya iso ya same ta tana ci, sai da ta gama tas ta janyo ruwan da ke cikin roba ƴar madaidaiciya wadda aka haɗo da abincin ta wanke hannu a ciki. Tana dauke hannu ya fito sanye da towel ɗan ƙarami a kan kafaɗarsa yana tsane ruwan jikinsa, ƙara tsorata ta yi har jikinta ya soma rawa amma ta daure ta ci gaba da zama. Sai da ya saka single da Gajeran wando sannan ya isa gaban mirrow ɗin da yake shaƙe da mayuka kala-kala kamar ɗakin mata, wani cream fari ya buɗe ya shiga shafe jikinsa da shi yana kare mata kallo ta madubi. Bayan ya gama ya iso inda take bai ce mata komai ba ya dauke kayan abincin ya fita, sai da ta soma jin tsoro ganin yaƙi dawowa sannan ta ji takun tafiyarsa, kamar wata soja haka ta ƙame tana son ya shigo ta ce ya mayar da ita wajan su Mom Yasira. Tun daga kan yatsun ƙafafuwansa ta soma kallon shi har zuwa kan fuskarsa da take ba yabo ba fallasa, kawar da kai ta yi ya yi murmushi ya ce "Tashi muje na miki wanka."
Kwalalo idanu waje ta yi dariya ta kama shi amma ya basar yana ƙara cewa "OK to na gane tashi ki je ki yi da kanki." Ya faɗa yana nuna mata hanyar toilet.
Harara ta aiko masa, in ban da ma ya raina ta ita zai kalla ya ce zai yi wa wanka? Salon ya kalle mata jiki dan ba shi da kunya, kwafa ta yi tana hura hanci ta shige toilet É—in shi kuma ya zo bakin gado ya zauna...
Wayarsa ya buɗe sai ka sakonnin Abir suna ta shigowa har da kira, dafe kai ya yi yana jin zuciyarsa na masa ƙuna da raɗaɗi irin na rabuwa da masoyi, da kyar ya buɗe saƙon nata inda ta masa dogon rubutu ya soma dubawa gaban shi na dukan uku-uku, ba ya so Abir ta kalle shi a matsayin ma ci amana alhali shi daga gareshi ba hakan ba ne..
_"Assalam alaikum, Yaya Suhal ina fatan kana lafiya dai ko? To Alhamdu Lillah. Yaya Suhal na ga abin da ya faru kuma na yi imani da Allah cewar kai ɗin ba ba ne mijina, ina so mu ɗauki haka a matsayin ƙaddara daga Allah, sannan don girman Allah Yaya Suhal ka riƙe min ƴar'uwata da amana, idan har ka cutar da ita to tamkar ni ce ka cutar hakan kuma zai azabtar da zuciya da gangar jikina, ga amanar Iman nan ka yi haƙuri da duk abin da za ta yi ma saboda abin ne ya mata girma, da farko ta tubure amma daga ƙarshe ta yi haƙuri ta rungumi kaddara. Ina muku fatan alkhairi Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba baɗi muje bikin suna bissalam."_
Lumshe idanu ya yi yana jin kamar ya ce ya fasa auren Iman, amma in ya yi wani tunani sai ya ga gara ya rungumi ƙaddara domin yi wa wadda ke son shi da gaskiya halacci, gabadaya ji yake komai ya masa zafi dauriya kawai yake ba ƙaramin azabtuwa yake da wannan gagarumin aikin da ya daukar wa kansa akan masoyiyarsa.. Tashi ya yi ya dauko mata kayan bacci masu kyau green color masu ya aje mata bakin gadon sannan ya fita.
Leƙowa ta yi ta ga ba ta gan shi ba ta fito daure da towel fari sol, da mamaki ta kalli kayan da ya aje mata tana tunanin to ita yaushe aka zo har aka kawo mata tufafi? Jinjina kai ta yi tuna maganar su Ammi zuciyarta ta karye tuna Abir hawaye suka zubo mata ta sa hannu ta goge, kayan ta dauka tana juyawa ganin riga da wando ce wandon iya gwiwa ne rigar kuma ko cibiya ba za ta kai mata ba. Zama ta yi tana jan tsaki ita zai raina wa hankali ya ba ta kayan 'yan iska irin wanda ya gani a Turai? Ganin dai babu sarki sai Allah ya sa ta miƙe ta isa gaban mirrow ɗin ta dauki man da ya shafa itama ta shafe jikinta da shi sannan ta sa kayan. Bakin gado ta dawo ta rafka tagumi tana jiran ya dawo ta tafi burin ta ya mayar da ita wajan su Mom Nabila amma kamar an aiki bawa garinsu, da haka dai bacci ya dauke ta sai asuba ta farka..
Washegari misalin karfe 8:am ya zo ya tayar da ita taƙi tashi ai kuwa ya sunkuce ta ya kai ta toilet, ba ta ankare ba ta ji ta a ruwan ɗumi ta buɗe idanu da sauri tana waiga ko'ina sai ganin ta ta yi a toilet. Zaro idanu ta yi tana kare jikinta ya yi murmushi shi dariya kawai take ba shi in ta yi wani abin, bai jira komai ba ya saɓe ta da soso da sabulu ita kuma ta kulle idanuwanta tana kuka wiwi kamar wadda ake zanewa. Bayan ya gama mata da kan shi ya dauko ta suka fito ya canja mata kaya ya shirya ta cikin riga da sket dinkin shadda, cewa ya yi ta yi Sallah ta ce masa ai akan kunnenta aka kira Sallah tana maganar tana murguɗa baki har ta kai karshe. Girgiza kai ya yi ya janyo hannunta suka fito palo inda suka tarar an gama shirya musu kayan kari masu rai da lafiya, da kyar ta ci kaɗan tana cewa ya kaita wajan 'yan'uwanta. Suna gamawa ya fito da ita zuwa wajan su Ammi suka gaisa ya fita ya bar ta..