Sashe 19
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi dai bai ce komai ba kansa a sunkuye yana ta daddana waya, shi kawai ba ya so ne ya shigo ya gan ta ba kyan tsari duk sai ya ji zuciyarsa na tafasa na barin kanta da ta yi ba gyara, ga bakinta da yake mugun wari in ta yi magana hakan ya tabbatar masa ba ta yin broch sai warin dauɗa da na baki, hakan ne ya sa duk ya ji ya tsane ta ga ƙarin abin haushin ma kayan da ya sayo wa Abir ta kwashe kusan rabi ta ba ta tana saka wa ko kyau ba sa mata saboda rashin gyaran jiki. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Yi haƙuri Grandma, kawai ni bana son ƙazanta ne shi ya sa nake ce mata ƙazama. "
"Na ci butar ubanka Abdullahi, da haƙurin ya mutu sadakar nawa ka bayar? Shashasha kawai tashi ka bar mana palo ka koma na gidanku, da alama dai Baraka ta soma koya ma ɓakin hali." Ta faɗa a fusace kamar za ta kai masa duka.
Bai sake cewa komai ba Mommy ta tashi ta kawo wa Uncle Aruf abinci da lemuka masu sanyi sannan ta dawo ta zauna ta ce "Babana ka daina shiga harkar Laraba please, babu ruwanka da ita ta yi duk abin da take so ai ƙuruciya ce za ta fasa duk abin da take da zarar ta yi hankali."
To kawai ya ce wa Mommy ya miƙe ya bar palon ya nufi ɗakin Grandma, ai kuwa ta juyo ta ce "Marar mutumci dawo kar ka shigar min ɗaki tun da ita ta gyara min."
Ko sauraron ta bai yi ba ya yi wucewar sa yana jin haushin yadda suka taru suna masa magana akan Laraba..
Abir ta dubi Uncle Aruf ta ce "Uncle ina tsaraba na?"
Sai da ya haɗiye lomar da ya kai baki sannan ya ce "Oh! Kin ga na manta ta cikin mota, ki bari in na gama zan ɗauko miki ko nasa Maigadi ya fiddo yanzu? Ya ƙarashe maganar yana mai tambayarta. Cikin zumudi da son ganin abin da ya kawo mata ta ce "Yes, Uncle ." Maigadi ya kira a waya ya ce ya zo zai sa shi wani aiki sannan ya kashe, yana aje wayar ya shigo da sallama ya rusuna ya gaishe da su Grandma Mommy ta amsa amma ban da Grandma da ta yi shuru tana bin su da kallo, ya mika masa makullin motar ya faɗa masa abin da zai ɗauko sannan ya fita. Bai ɗauki lokaci ba ya dawo da manyan ledoji baƙaƙe ya aje, godiya ya masa sannan ya ɗauki leda daya ya miƙa wa Grandma ya miƙa Mommy ɗaya ya miƙa wa Abir, ta yi saurin amsa tana kwance ɗaurin sai murmushi take har ta gama kwancewa. Tana buɗewa ta ga dogayen abayu masu kyau 'yan Dubai guda 6 sai riga da wando jins masu kyau sun kai kala goma, ta yi ta ɗaga wa tana dariya tana faɗin "Thank you my Uncle, Allah ya ƙara arziki mai yawa." Ta faɗa tana kara ɗaya daga cikin abayar. Amin ya ce mata yana murmushi, Mommy kuwa Material ne kala biyu sai atamfa kala uku sai mayafan su, haka Grandma ma atamfofi kala shida ya kawo mata har da takalmi da mayafi sai sa masa albarka take kamar ba yanzu ta gama zagin shi ba...
ÆŠaki ta nufa ta bar su a palon dan tana so taje ta gwada kayan ta ga yadda za su mata, shi kuma ya wanke hannu ya dubi Mommy ya ce "Mom wai ya ake ciki akan lamarin Abie? Sun kira kuwa?"
Nan-da-nan annori fuskar Mom ya ɗauke ta girgiza kai ta ce "Ai dama tun da suka sa ce su ba su taɓa kiran ɗaya daga cikin familyn gidan nan ba har Abir ta samu ta kuɓuto daga hannun su."
"To amma Mom ita Baby za ta iya gane ko da fuskar mutum É—aya daga cikin su ne?" Ya faÉ—a yana jin mugun kewar Abie har idanuwansa sun kaÉ—a sun yi jajur .
"Kayya Aruf! Ba tambayar da ba a mata ba amma ta ce ba ta taɓa ganin ko da fuskar mutum ɗaya ce duk fuskokinsu a rufe suke zuwa inda take." Nan ta ba shi labarin yadda aka yi mahaukaci ya cece ta, sosai Uncle Aruf ya cika da al'ajabi matuƙa wai mahaukaci ne ya ceci ƴar'uwarsa? Gyara zama ya yi ya ce "To ai kuwa ya kamata itama ta yi wani abu game da mahaukacin nan." Ya faɗa yana kallon Mommy. Nisawa ta yi tana murmushi ta ce "To ai yanzu haka maganar da nake ma can ne za su je ka tsayar da su, ta ce tana son ta kai shi Asibiti ko Allah zai sa in an ɗaura shi akan magani ya samu sauƙi."
"Yawwa very good." Ya faÉ—a yana yin jinjina da hannu. A fusace Inna ta ce "Kasan Allah n..
Ba ta ƙarasa ba ya yi saurin tarar numfashinta ya ce "Yes." Sake fusata ta yi ta ɗauki filon da ke kusa da ita ta jefa masa ya cafe yana dariya ta ce "Wallahi sai na zazzage ka in ka sake yi mana wannan yaren muna magana." Dariya ya kuma yi Grandma ta ƙanƙance idanu za ta yi magana suka ji sautin kukan Abir ta iso palon ta faɗa jikin Mommy.
"Ke lafiya kike kuka." Mom ta faÉ—a tana É—ago da ita.
Kasa magana ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfin ta har da ta tsagaita tukun ta ce "Waiyo Allah! Mommy na shiga uku na lalace ya zan yi da rayuwata? Shi kenan za su kashe bawan Allah bai ji ba bai gani ba ya zan yi da hakkinsa Mommy?" Ta faɗa tana kara fashewa da kuka..
Cikin rashin fahimta Uncle Aruf ya ce "Baby me yake faruwa kike wannan munanan kalaman? Ki sanar da mu mana."
Kasa ba shi amsa ta yi tana kuka har da majina, sosai hankalin su ya tashi suka zuba mata idanu har sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta É—ago hawaye na zarya kan kuncinta ta ce "Uncle ina Yaya Abdul don Allah ku kira min shi Wallahi zuciyata za ta buga, na ja wa bawan Allah masifa." Ta faÉ—a ta sake kuma rushewa da kuka wanda ya fi na yanzu tayar da hankali. Ganin haka ya sa Uncle Aruf ya kira Abdul ya ce ya yi maza ya fito akwai matsala, hankalin Abdul ya tashi ya fito daga wanka kenan a É—akin Grandma ya jiyo sautin kukan ta, ya É—auka kukan da ya zame mata jiki ne take yi sai da Uncle Aruf ya ce ya zo sannan ya yi saurin fitowa..
Da sauri ya nufo wajan Mommy yana faÉ—in "Baby me ya faru?" Jin muryarsa yasa ta tashi daga jikin Mommy ta faÉ—a jikinsa tana sakin kuka ta ce "Yaya na shiga uku sun sace shi."
"Wa kenan aka sace?" Ya faÉ—a a kiÉ—ime.
"Zaiyan ɗin mana sun sace shi." Kowa nanata sunan yake dan su ba su san akwai wani mai suna haka a cikin familyn su ba, sai da ya sake tambayar ta sannan ta tsagaita kukan tare da dagowa daga jikinsa ta ce "Yanzu da na shiga ɗaki sai na kira Baba ina son na ce masa yau ba za mu samu damar zuwa ba sai gobe da Yamma sh... Kasa ƙarasa maganar ta yi kuka ya ci ƙarfinta har jikinta rawa yake, ganin hakan yasa Abdul ya kama hannunta suka zauna a kan kujera Uncle Aruf ya miƙa mata ruwan da ke gefensa ta amsa ta shanye duka, haka ta dinga sauke ajiyar zuciya akai-akai har sai da ta ji ta dan samu sauƙi sannan ta soma faɗa musu komai.
"Baba ya ce min suna tsaye da Zaiyan yana ce masa gani nan zan zo yana murna sai ya juya ya tafi, ko nisa bai yi ba wata mota ta zo ta ɗauke shi, Yaya don girman Allah ka taimakeni ka samo min shi Wallahi yana cikin halin neman taimako. Dama nasan dole su dawo su neme shi tun da shi ya ceceni a hannunsu dan su rama abin da ya musu, yanzu ga shi sun yi nasarar ɗauke shi wa ya sani ma ko sun kashe shi." Ta ƙarashe maganar tana sake ɓarkewa da sabon kuka har da jan zuciya take kamar za ta shide saboda tsabar tashin hankalin rashin sanin a wani hali a yanzu yake ciki..
Shuru suka yi suna kallon ta tana kuka, Grandma da itama take nata kukan ta face majina ta ce "Amma su ko waɗannan mutane sun cika marassa imani, shi mahaukaci me ya sani da har za su ɗauke shi? Allah dai ya tsine musu cikin kwando.. Ajiyar Abdul ya sauke ya ce "Uncle dole na koma Office na shigar da ƙaran nan, dama alfarma na nema dan na kai Baby can na dawo daga wajan aiki."
Jinjina kai Uncle Aruf ya yi ya ce "Haka ne. Tashi mu je a fara bincike sannan a kira shi Baban ya mana bayanin kalar motar da ta É—auke shi ko za iya gano inda suka kai shi.."
Jan majina ta yi ta ce "Un.. Uncle Wallahi ba su da imani mutanen nan, yanzu haka ma sun kashe shi." Ta sake ƙara wa kukan ta volume. Rarrashin ta suka dinga yi har suka samu bacci ya ɗauke ta, Abdul ya kira Abba ya faɗa masa komai sannan suka wuce zuwa station ɗin su Abdul..
Suna cikin tafiya ne wata mota ɓaka ta dinga bin su daga baya duk inda suka nufa sai su ta biyo su a baya, Abdul ne ya nakare da ana bin su ya yi saurin janyo inda yake aje bindigarsa ya fito da ita ya riƙe a hannu ɗaya, Uncle Aruf ya dube shi ya ce "Ya da ɗauko bindiga?"
"Ba ka ga ana bin bayanmu ba?" Hannu ya miƙa ya saita madubin gefen motar ga lalle fa motar nan su take bi. Sai da suka kusa isa Police station sannan wannan motar ta fasa bin bayan su...