← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 120

Sashe 36

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Idanu waje take kallon shi har ya gama ba ta labarin, to in har su Baba suna Asibiti su kuma waɗanda ta gani à gidan su waye ? Ko kuwa suma aljannun ne kamar matar da ta gani? Sai da ya girgiza ta ta yi firgigit nan-da-nan tsoro ya shige ta, cikin kiɗima ta ce....

WhatsApp number : +966577675904

_*Taku har kullum Maman
[6/20, 7:48 PM] Ummu Amjad: Shafi na (19)

Cikin kidima ta ce "Y.. Yayaaa.." Ta ja sunan tsoro karara ya baiyana kan fuskarta. Dagowa ya yi a nutsu ya dube ta, ganin yadda ta rude sai ya kamo hannayenta ya kai kan fuskarshi yana mai tsare ta da idanu, sai da ya dauki kusan minti biyu a haka kafin ya yi kafin halin janye idanunshi daga cikin nata.

Ita kuwa sumar zaune ta yi abubuwan da suka faru sun tsaya mata a rai, yar karama masarrafarta n'a neman kasa daukan wannan abu mai cike al'ajabi. Shin idan har yayan nata gaskiya yake fada mata su Baba suna Asibiti su n'a gida su waye ? Ko kuwa dai sun mutu ne suka mata fatalwa ?

Ganin ba ta yi motsa ba Abdul ya girgiza ta ta yi birgigit ta dawo haiyacin ta, doguwar ajiyar zuciya ta sauke ji take kamar ta kurma ihu saboda hargitsewar da yar karamar kwakwalwarta ta yi, dago da kai ta yi cikin wani kalar yanayi ta tsare shi da idanu. Sai da ya gaji ra shurun sannan ya nisa ya ce "Baby ki fada min abin da kike ɓoye min, na ga kamar akwai abin da kike son faɗa." Ya ƙarashe maganar a daidai lokacin da suka ƙaraso gida..

Shuru ta masa gabaɗaya ta rikice, ganin haka ya sa Abdul ya mata nuni da ta fita a lokacin da aka gama yin packing, ba muso ta ɗauki handbag ɗinta jiki a saluɓe ta soma ƙoƙarin fita daga motar.

"Baby ki kwantar fa da hankalin ki." Ta ji muryarsa lokacin da ta zuro ƙafafuwanta waje, dakatawa ta yi da fitar ta juyo ta kalle shi.

"Yaya ina so ka kaini na ga su Baba a Asibitin, idan kuma ba za ka samu dama ba ka sa a kaini." Ta faɗa tana ɓata rai. Ɗaure fuska ya yi bai ce da ita komai ba ya buɗe motar ya fito, gabaɗaya ya rasa gane kan ta babu abin da ta iya in ba kuka ba nan ta fi kauri, shi kuma baya son saurin kukan nan da take haushi yake ji, shi ya sa wani lokacin yake rabuwa da ita ta yi ta ta yi, har sai in ya ga abin zai zame mata matsala ya rarrashe ta.. Goge hawayen da suka zubo mata ta yi ta fito ta nufi ciki. Da sallama ta shigo kanta a ƙasa kamar wata munafuka, Grandma da ke shafa mai a ƙafa ta ɗago tana amsa mata sallamar. Ganin yadda ta shigo ya sa Grandma ta taɓe baki tana kawar da kai gefe, zama ta yi a kusa da Grandma ta saita nutsuwar ta a sanyaye ta ce "Grandma barka da hutawa."

Janye ƙafafuwanta ta yi daga kusa da Abir tana ƙara mulke su da mai, sai da ta sha ƙamshi sannan ta ce "Zan ga dai wanda zai aure ki yar nan, ace kina mace amma ba ki da kuzari irin na yaran da suka balaga kike ɗan kazar-kazar mana, ke duk komai naki a sanyaye yake kamar wata raguwa. Ni kam ban taɓa ganin mutum irin ki ba, ba dan ba kina da sunana da ba zan taimaka miki ba. "

Ɗago kai Abir ta yi ta kalli Grandma tana yin murmushin yaƙe, in da sabo ai ta saba da irin wannan maganganun na Grandma, a nutse ta ce" Ke dai Grandma kullum sai kike cewa wai za ki taimaka min, amma har yau ban ga taimakon ba shuru kake ji kamar shaho ya ci shirwa. " Ta faɗa tana tashi ta wuce ɗakinta da ɗan saurin ta dan kar ma ta ji rashin darajar da Grandma za ta mata..

" A ni Hauwa'u." Ta riƙe baki sannan ta ci gaba," Da alama kema yanzu wannan ƙaton banzar ya soma koya miki rashin kunya, in ban da ma ni kin rainani ina matsayin uwar ubanki ki ce min wai kin ji shuru kamar shaho ya ci shirwa? Uwar taki za ta zo ta same ni ina jiran ta har shi fitinannan ɗan'uwan naki duk na ishe ku riga da wando har da ɗankwalin ɗaurawa. " Tana cikin yin sababin sai ga Abdul ya shigo palon, kallon shi ta yi cikin masifa ta ce" Uban me ka zo yi a sashena? " Ta yi micin-micin da idanu tana gyara zama..

Zama ya yi ya riƙe kanshi ya lumshe idanunsa, sosai zuciyarsa ke wani irin lugude sam ya kasa nutsuwa, da sauri ya buɗe idanunshi wanda suka yi jajur ya kalli Grandma. Itama kallon shi take ganin yadda idanuwansa suka yi ja ta sauke ƙafafuwanta ta dube shi ta ce "Abdullahi, me yake faruwa wai? Na ga wannan figaggiyar ta shigo fuskarta da alamun damuwa, ko faɗa kuka yi ne?"

Sauke hannayenshi ya yi daga kan ya juyo ga Grandma, ya É—aga baki zai yi magana ta dakatar da shi ta tashi ta iso inda yake ta kama hannunsa suka nufi É—akinta..

Suna isa ta zaunar da shi a bakin gado ta É—auko ruwa mai sanyi ta ba shi tare da cewa "Ka sha ruwan."

Bai musa mata ba ya amsa ya shanye duka ya aje cup ɗin, ajiyar ya dinga saukewa idanunsa lumshe, wani irin zafi yake ji ƙirjinsa na masa matuƙa. Grandma ya nisa ta ce "Wai me ke faruwa?" A hankali ya ɗan matso kusa da ita ganin haka ya sa ta kwanto da kanshi kan cinyarta ta soma shafa masa ta soma masa nasiha..

"Abdullahi ko ma mene ne yake damun ka ka yi haƙuri, dukkan tsanani yana tare sauƙi ka kwantar da hankalin ka ka yi aikin ka cikin nutsuwa da adalci."

Sai a lokacin ya ji zai iya magana, ya ce "Grandma mutane ba su da amana, mutane mafi yawan su duk azzalumai ne, ban san wani abu Abie ya yi musu ba suka kashe shi. Hakan bai musu ba suke neman rayuwar iyalinsa, Wallahi! Wallahi ! Wallahi! Kin ji na rantse sau uku to sai na binciko duk abin da aka binne duniya ta sani, sai na lalata musu komai na hana su jin daɗin rayuwa kamar yadda suka hana mu ji, hatta gidan nan akwai abin da yake faruwa n cin amana wanda kowa ya kasa fahimtar hakan, ni kuma na yi alƙawari sai na gano wannan maƙarƙashiyar da ake ta shiryawa tsayin lokaci. " Ya ƙarashe maganar yana tashi zaune ya fuskanci grandma..

Shuru Grandma ta yi tana nazarin maganar tana É—aura ta akan mizani na hankali, tabbas ita kanta ta kasa nutsuwa da wasu daga cikin 'yan gidan. Kallon shi ta yi cikin wani yanayi ta ce "Indai akan gaskiya ne za ka yi aikin nan Abdullahi ina goyan bayan ka É—ari bisa É—ari, ni yanzu ban ma yarda mutanen nan ba sa bin rayuwar mai sunana ba." Ta faÉ—a tana jan numfashi..

Bai ce da ita komai ba ya tashi ya bar É—akin..

Ko da ta shiga ɗakin mamaki ne ya hana ta ƙarasawa ciki ganin yadda aka rikito mata kayan cikin drawer ta duk an barbaza su a tsakar ɗakin, da ƙyar ta ƙarasa shigowa ta aje jaka da mafi ta zauna a bakin gado tana mai kallon kayan, ko ba ta faɗa ba wanda ya rikito mata kayan nan akwai abin da yake nema a cikin drower. Tashi ta yi ta soma tattare kayan tana yi tana ɗaɗɗaga kayan tana ƙare musu kallo, bayan ta gama ɗaukewa ta rufe har ta juyo ta ga ƙyallin wani abu a ƙasa, baya ta dawo ta sake baza idanunta tana son sake ganin abin da ta gani. Sai da ta sunkuya ta duddubawa sannan ta hango shi ta kai hannu ta ɗauko, ɗankunne guda ɗaya sai walƙiya yake yi ta koma ta zauna a bakin gado tana juya ɗankunnen ta ji an buɗe ƙofar ta yi saurin ɓoyewa..

Da kallo yake bin ta har ya shigo ya zauna ya kalli hannunta da ta yi baya da shi, hararar ta ya yi ya ce "Meye kika ɓoye Baby?" Ya yi maganar yana kamo hannun nata, ganin haka sai ta kwace hannun ta buɗe ta nuna masa ɗankunnen, ta ce "Yaya akwai wanda ya shigo min ɗakin nan bayan tafiya ta." Labarin yadda ta ga kayan sawarta ta ba shi, shuru ya yi na 'yan wasu daƙiƙu yana kallon ɗankunnen, ya taɓa ganin wannan ɗankunnen amma ya rasa a jikin wace ce ya gani, kallon ta ya yi ya ce "Baby shin kafin hakan ta faru kin taɓa ganin wani abu wanda ba ki san da shi ba a drowerki?"

Kai ta ɗan ɗaga sama alamar tunani, can ta kalle ta ce "Akwai wata rana na zo ina gyara kayana na ga wani abu ɗan ƙarami, wanda ni dai da kaina ban san da zaman shi ba a drower, shi ne na samu guri na ɓoye shi."
Chapter 36 · 0% Book details