Sashe 116
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waro idanu Mamma da Mai martaba suka yi har da su Kilishi da suka zama 'yan kallo, Mai martaba ya kalli Zaiyan yana tariyo rayuwarsu ta baya, yadda suka ci burin zuwan shi duniya a lokacin, hannu ya miƙo wa Zaiyan shi kuma ya rarrafa kamar wani yaro ya iso gaban Mai martaba. Rungume shi ya yi yana jin ƙaunar yaron nasa na ratsa jikinsa, alama ya yi wa Abir da hannu ta zo, ta ƙaraso ya haɗa su ya rungume yana sanya musu albarka. Sai da suka gama kukan farin ciki Abir ta kasa daurewa ta matso gaban Mamma ta fashe kuka, hankalin Mamma ya tashi ta ruƙo ta tana tambayar ta ko wani abu aka yi mata? Jan majina ta yi tana shashshekar kuka ta juya ta janyo handbag ɗinta ta buɗe jikinta sai rawa yake, wani babban photo ta ɗauko ta miƙa wa Mamma.
Da wani irin sauri Mamma ta kalli Abir baki na rawa ta ce "W. W. Wannan ai photon 'yan'uwana ne sa ni a ina kika same shi Æ´ar nan?"
FaÉ—a wa ta yi jikinta cikin kuka ta ce "Mamma muma É—iyanki ne ni da Yayana, ni É—iyar Hassanarki ce yayana kuma É—an kanwarki Hajara."
Rasa me Mamma za ta yi a wannan lokacin ta yi, wai yau É—iyan yan'uwanta ne a gaban ta tare da nata yaran? ÆŠagowa Abir ta yi ta nuna Abdul tana murmushi ta ce "Ba mafarki kike ko gizo ba Mamma zahiri ne, mu É—in jininki ne."
Tsabar farin ciki Mamma sai furta Alhamdu Lillah kawai take tana shafa fuskar Abir ta dawo ta taɓa hannun Abdul da Zaiyan, sun dauki lokaci a haka sannan Mamma ta gyara zama ta ce "To amma me ya sa ba ku zo da su Hassanata ba? Ko dai suna baya a gaba za su zo, kai ma ina Inna Asabe take?"
Sunkuyar da kai Abir ta yi tana kuka ta ce "Mamma sai haƙuri ƙanwarki ba a daɗe da yi muku wannan wutar ba ta rasu, ita kuma Mom ba ta fi shekara biyu da rasuwa ba, wannan gaisuwar da Suhal ya je to ita ce ta rasu har ita Inna Asaben duk sun riga mu gidan gaskiya." Tsabar kiɗimewa da Mamma ta yi sai gani suka yi ta yi baya ta zube a kan Mai martaba a sume, da sauri Ikilima ta tashi tana kuka ta ɗauko ruwa tana yayyafa mata tare da cewa "Mamma don Allah ki tashi ka da ke barmu, kin ga ke kadai kika rage musu a rayuwa." Ta durƙusa tana jijjiga ta.
Numfashi ta ja tana buɗe idanu ta tashi da sauri za ta miƙe Mai martaba ya yi saurin janyo hannunta ta dawo ta zauna, shi kansa jarumta yake nunawa idanuwansa sun yi jajur sai kallon Zaiyan yake, ji yake kamar ya maida shi ciki.
"Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Hassanata da ƙanwata da Inna Asabe duk sun rasu? To yanzu ina mahaifiyata? Ko itama ta rasu?" Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya.
"Bayan an haifi Yaya Abdul ta rasu."
Sosai Mamma ta sha kuka har idanuwanta suka kumbura, ta so ace ta ga 'yan'uwanta da kuma Inna Asabe amma mutuwa ta musu yankan ƙauna , Kilishi ta girgiza da ganin Zaiyan a matsayin babban ɗa ga mijinta, ita kanta Sarauniya Bilkisu mamaki ya hana ta cewa komai sai bin shi take da kallo.
Mamma ta tashi taje ta wanke fuska ta dawo ta kira Abdul da Abir suka zauna kowanne a gefe ɗaya, hannu ta sa ta zagaye su Abir ta yi murmushi tana jin wani sanyi na ratsa zuciyata ga ta ka twins sister ɗin Mom Kuma mahaifiyar mijinta, shi kansa Abdul wata nutsuwa yake ji gani yake kamar a jikin Mom yake. Abinci ta sa aka jera musu suka zauna aka fara ci, Kilishi ta kasa daurewa tana kallon Abir ta ce "Fulani ko dai mun samu ƙaruwa za ayi mana jika a gidan nan?"
Saurin sunkuyar da kai Abir ta yi tana jin kamar ta nutse ƙasa dan kunyar su Mamma, murmushi Mamma ta yi tana aje cokalin da take cin abinci ta kalli Abir tare da cewa " 'Yata wai haka ne?"
Girgiza kai ta yi tana yatsine fuska jin cikinta yana hautsina mata, da sauri ta miƙe ta wuce sai ta rasa ina za ta bi ga amai ya tafo. Tashi Mamma ta yi ta bi bayanta ta same ta tana tofar da yawu sai yunƙurin amai take, da hanzari Mamma ta kama hannunta ta nufi ɗakinta da ita ta kai ta toilet. Sai da ta amayar da abin da ta ci yau sannan ta samu sa'ida, wanke bakinta ta yi tana mayar da numfashi gabaɗaya jikinta ya dauki rawar sanyi ta lallaɓa ta fito. Mamma na jikin ƙofar tana jira ta fito ganin ta ta ƙanƙame jiki ya sa ta janyo ta ta kaita kan gado ta kwantar, jikinta ta taɓa ta ji zafi rau ta zauna a bakin gadon tana jero mata sannu. Sai da ta lullube ta ta wani lallausan bargo mu kauri sannan ta fito wajan cin abincin, Zaiyan duk ya kasa nutsuwa sai juya cokalin yake a cikin abincin.. Suhal ya yi murmushi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska, dafa shi ya yi murya ƙasa-ƙasa ya ce "Yaya tashi ka bi matarka ba sai ka dinga mana cin magani ba."
Hararar shi Zaiyan ya yi yana hura hanci, murmushi ya yi ya juyo ya ga itama Iman taƙi cin abincin sai kumbura baki take, gira ɗaya ya ɗage mata ya ce "Ke kuma fa? Me kike so?"
Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Ni zan je wajan Anty Baby."
Da hannu ya mata alama da ta tashi ta je, da hanzari ta tashi sum-sum ta wuce har tana tuntuɓe.. Kallon su Mamma ta yi ta girgiza kai suka ci gaba da cin abinci har suka gama suka dawo palo, Mamma ta sa Suhal ya duba Abir ai kuwa Zaiyan ya ce bai isa ya gan masa mata ba sai dai su je tare, dariya duk suka yi Abdul ya ce "Iyye sannu masu kishi."
Banza ya masa suka jera shi da Suhal suna tafi gwanin birge wa kamar 'yan biyu. Duba ta ya yi ya rubuta maganin da za a sayo sai Zaiyan ya ce masa ai akwai maganinta da take sha kullum, ya bukaci a kawo masa ya gani. Jakar Abir Iman ta ɗauko ta duba maganin ta miƙa masa, sai da ya dudduba su da kyau ya ga suna da kyau sannan aje ya, kamo hannun Iman ya yi yana dariya ya ce "Kin ga My Imani zo mu bar musu ɗakin mu tafi namu kar Yaya Zaiyan ya cinye ba ko gishiri." Dariya Iman ta yi suka wuce tare da rufo musu kofa..
Gadon ya hau ya yaye bargon ya zuba mata idanu, yadda take bacci numfashinta na fita a hankali sai ya ji ta birge shi, hannu ya kai ya shafo fuskarta ta soma motsi. BuÉ—e idanu ta yi tana kallon samar É—akin sai ta ji mutum a gefen ta, juyowa ta yi suka haÉ—a idanu ta sakar masa murmushi, shi ma ya mayar mata da martanin murmushi cikin wani kalar yanayi ya ce "Baby sannu kin ji, yanzu ya kike jin jikin naki?"
Yawu ta haɗiya saboda maƙoshinta ya bushe ta ce "Da sauki Nury."
Janyo ya yi ya ja bargon ya rufe ta yana shafa kanta har bacci ya yi awon gaba da ita. Ya jima yana kallon ta sannan ya tashi ya fita ɗakin ya koma wajan su Mamma da suke ta hira Abdul na ba ta labarin family Maitama har abin da Umma da Daddyn Aruf suka yi wa 'yan'uwanta. Wani Sabon kukan Mamma take tana cewa ba za ta bar rayu kan 'yan'uwanta su tafi a banza ba, yadda Umma ta yi sanadin barin su lahira itama sai ta tsaya kai da fata an hukunta ta, Iman na bayan Suhal ta sunkuyar da kai sai zubar da hawayen baƙin halin Umma take.
Washe gari Mai martaba ya sa aka zaga ko'ina da su Zaiyan ana nuna shi a matsayin babban É—ansa, sosai kowa ke mamaki sai kwasar gaisuwa ake duk in da ya yi sai a zube ana gaishe da su, suna gamawa Suhal ya sa aka shirya musu fita shan iska. Sosai suka ji daÉ—in garin Abir sai sambatun kyan rastaurant É—in da suka je take wai sun iya abinci mai daÉ—i ta ci masa da miya..
Kilishi ta zubar da makaman yaƙinta ganin Mamma ta mata nisa, amma kuma tana tsoron shiga cikin su in ta tuna yadda ta musguna wa Mamma a baya, ita kuwa Sarauniya Bilkisu sabon shiri ta yi ta kasa samun kwanciyar hankali na bayyanar Zaiyan, ga shi ita ba ta taɓa haihuwa ba bare ta ce ta ƙarfi da yaji ɗanta zai gaji sarauta.
Sai da suka yi sati sannan ne Abdul ya ce su fa za su koma Nigeria su shigar da ƙara kotu, Mamma ta ce ba za a bar ta ba dole ta je ta tsaya a bi mata haƙƙinta na sanadin mutuwar 'yan'uwanta. Mai martaba ya ce suje in an fara zama zai zo shi da su Suhal, Zaiyan ba dan ya so ba ya zauna dan shi cewa ya yi ya fi jin daɗin zamansa a Nigeria, sannan shi ma yana da kes da su Alhaji Mustapha amma Mai martaba ya ce ya bari Abdul zai shigar da ƙara su kuma za su biyo su daga baya. Haka Mamma da Ikilima da Abdul da Abir tare da Salim suka tafi Nigeria Zaiyan ya yi kamar ya ce a bar masa matarsa amma kunyar Mamma ta hana shi cewa komai, yana kallo jirginsu ya ɗaga zuwa Nigeria..