← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 120

Sashe 88

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta gama girki ta je ta tashi Zaiyan amma yaƙi tashi ko ta ɗago shi sai ya saki jiki ya yi baya, haƙuri ta yi ta shiga wanka kafin ya tashi su ci. Har karfe shabiyu da rabi bai tashi ba ita kuma yunwa take ji hakan ya sa ta zubo ta fito zuwa ƙofar Ta Sakkwato, samu ta yi mijinta ya zo sai ta yi baya za ta koma ya ce ta zo shi zai shiga daga ciki...

Karfe 2:30 mijin Maman Amal da mijin Maman Samira suka zo, sai da suka ci abinci suka fita daga gidan sai ga yaro ya yi sallama yana tambayar ina Maman Samira, da sauri ta ce. "Gani nan yaro yo nan wajan." Ta faɗa tana hararar Abir da ta ɗago. Yana zuwa ya miƙa mata wata baƙar leda ya ce "Wai in ji Sabitu ya ce kuɗinki ne dubu ashirin da biyar da ya dauka ba ki sani ba, ya ce in ya dawo zai miki bayani." Yaron na faɗin haka ya wuce abin sa..

Saroro ta yi tana kallon ledar da kuɗin yake ciki, ɗagowa ta yi suka haɗa ido da Abir ta yi saurin kawar da kai ta fito da kuɗin ta lissafa ta ga har da ƙarin dubu 5 akai, jikinta ne ya yi sanyi ta kalli Maman Amal murya kasa ta ce. "Ashe Sabitu ya dauka har na ce waccan ta dauka."

Kafin ta ba ta amsa ta ga Gamboliya a gaban ta ya miƙa mata hannu yana wani zaro ido ya ce. "Miƙo mana kuɗin da Alhaji ya biya ki tun da kin samu nakin."

Jiki a sanyaye ta miƙa masa kuɗin tana bin shi da kallo.

"Tsuww an ji kunya dai, Wallahi ke dai Maman Samira kin yi faɗuwar sokana, yanzu don Allah ina mutumcin haka zuwa Makkah da kare? Kin liƙa wa ƴar mutane har da dukan ta ashe ma ƙasurgumin ɓarawon yana ɗakinki, a dinga bincike in za ayi abu." Yana gama faɗin haka ya warci kuɗin fuu ya wucewar shi ya dawo wajan su Abir..

Miƙa wa Abir kuɗin ya yi ya ce " Ƴar shawalwala ingo ki sa a aljihunki, kuma Wallahi in kika yafe wa su Maman Amal sai mun ɓata da ke, wannan cin zarafin da suka miki ai kotu ce kawai za ta rabamu da su. In ban da sun raina ki ina abin ma yake wai mayya ya ci jariri! Ai kowa ya gan ki ya san kin fi karfin dubu 25 Wallahi, dan ba ma gidan har suka samu kwarin gwiwar isa inda kike ma." Zama ya yi yana ci gaba da sababi Abir ta murmusa, ita dai in su Ladidi suna magana kawai kallon su take yadda suke maƙale hannu suna tafi abin na ba ta dariya, kuɗin ta dauka ta miƙa wa Ta Sakkwato ta ce "Hajiya ki amsa ki aje masa in ya dawo sai a ba shi, sannan ki miƙa min godiya ta a gare shi na karramawar da ya min."

Ta Sakkwato ta kalli gefen su Maman Amal ta wurga musu harara ta amshe kuɗin ta kalmashe ta soka a gefen cikinta. Sai da ta kusa cinye abincin da ta zubo ɗagowar da za ta yi ta ga mutum a tsaye a gaban ta, turo baki ya yi sanye yake da wando iya gwiwa da singlet, da sauri ta haɗiye abincin da ta kai baki ganin faffadan ƙirjinsa mai cike yalwataccan gashi baƙi, kallon su Ta Sakkwato ta yi ta ga suma shi suke kallo sai ta wayance ta dawo da kallon ta kan shi ta ce "Muje ciki ka yi wanka sai ka ci abinci."

Zama ya yi a gaban ta ya sa hannu ya dauko abincin ya nufi bakinta da shi, ba dan ta so ba ta daga baki ya sa mata, ganin zai kuma daukowa ta riƙe hannun nasa ta ce "Tashi muje ciki na ce ma." jimƙe wanda ya dauko ya yi ya nufi bakinta ta kauce ai kuwa ya yaɓa mata a kunci, zaro ido ta yi ya kuma kai mata ta kauce ya yaɓa mata a haɓa..

"Chass Wallahi, Æ´ar shawalwala tashi ku shiga daga ciki wannan mijin naki É—an rigima ne." Cewar Ladidi.

GabaÉ—aya kunya ta rufe ta ta dauke plate É—in ta kama hannunsa, har sun kusa isa Ta Sakkwato ta ce "Jiddo in kin gama ina son ganin ki."

Jinjina mata kai kawai Abir ta yi suka shige É—aki..

A ɓangaren su Alhaji Mustapha liyafa ta ci gaba, saboda yanzu lokacin zaɓe ya yi sun kuma je sun cike form na 'yan takarar Gwamna, Alhaji Mustapha shi suka sa a matsayin wanda zai yi takarar gwamna in ya haye kuma su yi mulki su uku..

Yau ma sun haÉ—a taro na yan mata da da samari masu yi musu campaign suna ta tsara yadda komai zai tafi, Alhaji Mustapha ya mike ya kira zugar yan sara-suka suka tsaya a gaban shi suna fadin "Sai ka yi mai dubun nairori kai ne gwanan Yola ko suna so ko ba su so dan uban mutum sai ka É—are kujera."

DaÉ—i sosai Alhaji Mustapha ya ji ya fito da É—aurin 'yan rafa guda biyar É—aurin dubu É—ari-É—ari ya ba su, saurin amsa shugaban nasu ya yi Alhaji Mustapha ya ce "Ku je ku ji daÉ—inku da wannan kuÉ—in, indai kuka min abin da nake so zan ba wa kowannen ku mota da kuÉ—i masu tsoka."

Ihu suka kwasa suna faɗin "Allah dai ya biya muna godiya." Da haka ya sallame suka tafi ya dawo kan matan, suma kuɗi ya ba su kamar yadda ya ba wa mazan, gyara tsayuwa ya yi ya kalli wata matashiyar mata wadda za ta kai shekaru 35 ya ce "Bisho ku sha ruwa da wannan indai na ɗare kan kujera za ku ga yadda zan muku duk abin da kika nema a wajena, ku ne za ku tafi ƙauyuka zan sa a baku atamfofi da taliya da sauran abubuwa wanda za a raba wa duk wanda suke goyon bayan mu."

Rusunawa Bisho ta yi ta ce "An gama ranka ya daÉ—e godiya muke."

Har ya juya zai koma wajan zamansa ya hango wata tsaleliyar budurwa fara sol ta ci kwalliya, sanye take da doguwar rigar atamfa ta rufe jikinta da mayafi, sake kiran Bisho ya yi ya nuna mata yarinyar wadda ko kanta ba ta É—ago ta kalle su ba bare ta san da ita suke ba. Isa ta yi ta kira ta tare da mata rada a kunne ta jinjina kai, sai bayan taro ya tashi sai ga ta ta dawo Alhaji Mustapha na tsaye yana jiran ta, tana isowa ta rusuna ta ce "Ranka ya daÉ—e gani."

Wani kallon ya bi ta da shi yana shafa gemu ya ce "Wato yarinya kawai na ga kin mini ne, ina gayyatarki nan da kwana uku zuwa wani waje mu fahimci juna, dan gaskiya na gani na ƙyasa."

Hade rai ta yi ta ce "To yanzu sauri nake ranka ya daÉ—e ka ba ni adress É—in inda za mu hadu."

Wani ƙayataccan murmushi ya yi ya ce "Ba ni number ki."

Ƙaramar wayarta ta ciro ta bashi number, ganin wayar ya ce mata tana babbar yarinya bai kamata ta kasa riƙe iPhone ba, ta ce masa ba da kuɗin sayan iPhone ɗin ai sai ya ce da sun hadu zai saya mata, haka ta mai sallama ta fita a gidan...

Tana fita ta warware mayafinta ta ƙara yafawa, sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta buɗe Jakarta ta dauko wayarta ta daddana ta danna kira, bayan sun gaisa ta yi murmushi ta ce "Oga yanzu na dawo daga gidan wadmɗancan marassa mutumcin, sannan akwai ƙarin wata cakwakiyar kuma abin ya matuƙar girgiza ni sosai."

Daga can ɓangaren Damisa ya ce "Ai za ki ga abin da ya fi ma haka ma Jk au na manta Laraba."

Dariya ta yi ta ce. "Haba Oga kaima Laraba za ka ce kamar a gidan aikin nawa?"

Tashi ya yi zaune ya goya hannunsa baya ya ce "Yanzu meye abu na gaba, saura sati ɗaya na duro ƙasar?"

Daɗi sosai ya kama Laraba dan ta ƙagara ta hadu da ƴar'uwata, haka ta dinga faɗa masa duk wani abu da su Alhaji Mustapha suke ƙullawa, ƙarshe suka yi Sallama ta wuce da sauri ta samu mota ta shigo sai gida...

Abir sai bayan kwana uku ta tuna Ta Sakkwato ta ce tana son magana da ita, hakan ya sa ta yi jiran dawowar ta gida. Bayan ta dawo ta shiga É—akinta ta bar Zaiyan zaune yana kallo a computer ta, zama suka yi Ta Sakkwato ta ce. "Ya dai mi ya ka hwaruwa ?"

Murmushi ta yi ta ce "Kin ce ki na son magana da ni, to na manta sai yau na tuna na zo."

Gyara zama Ta Sakkwato ta yi dan dama abin ya daÉ—e yana damun ta tun haduwar ta da Abir, nisawa ta yi ta ce "Wai shin ina iyayenki suke? Kuma ya anka yi ki na cikin nutsuwar ki kika yarda aka aura miki mahaukaci wanda ba zai amfane ki da komai ba?" Ta faÉ—a a tausashe.

Sunkuyar da kai ta yi idanuwanta sun cika da ruwa, a hankali ta ce "Ni marainiya ce ba uwa ba uba ba dangin uwa, dangin uba kuma sun tsaneni ba sa son zamana a cikin su shi ya sa na yi wa kain hisabi, shi ma mijina ba shi da kowa a duniya sai ni sai waɗanda suka riƙe shi suna taimaka mana lokacin da muna kai shi Asibiti." Labarinta ta faɗa mata babu abin da ta boye mata har auren ta da Suhal duk ta sanar da ita, jin Ta Sakkwato take tamkar mahaifiyarta shi ya sa ta sanar da ita ko ta samu sassauci a zuciyar ta..
Chapter 88 · 0% Book details