Sashe 64
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Idanuwan Iman ne ya cika taf da hawaye Abir ta kamo ta suka rungume juna ta saki kukan da take danne wa, rarrashin ta Abir ta yi tana faɗa mata ai za su yi waya da sun je za ta kira Mom Yasira su gaisa, da kyar Mom Nabila ta ɓamɓare ta daga jikin Abir tana kuka tana waiwayen ta har suka bar ɗakin .. Umma ta rungume Iman tana murmushi ita kuma tana ta kuka tana cewa ba za ta tafi ba, da kyar ta lallami ta shigar da ita mota suka tafi.. Daret airport suka tafi nan suka haɗu da dangin Ango nata jiran su, ba su daɗe ba jirgi ya sauka suka shiga ya ɗaga su zuwa kasar Niger....
Yasmin kuwa ta ci alwashin sai ta yi wa Abir abin da za ta zama abin kwatance da zarar sun dawo daga kai Iman, itama Ammi haka ta ƙudurta za ta saita wa Abir zama...
_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~
+966577675904
Shafi na (31)
Cikin dare zazzaɓi mai tsanani ya rufe Abir sai rawar sanyi take tana ƙara ƙudundunewa a cikin bargo, da kyar ta ɗaga idanuwanta ta kalli gaban ta ko za ta ga wayarta amma ba ta gani ba. Wani irin murɗawa cikinta ya yi ta runtse idanu tana fitar da wani irin numfashi mai zafin gaske, juyi ta dinga yi tana salati ji take kamar ana yankan 'yan hanjinta in cikin ya murɗa. Zuwa can ya lafa ta shiga sauka numfashi sai zufa ta dinga karyo mata kamar an mata feshin ruwa, dogon numfashi ta ja tana jin kanta ya mata mugun nauyi ga wani irin zafi da ya ɗauka daga ciki ji take kamar an kara mata kan a gaban tukubar gashin tsire. Ciwon cikin ne ya ƙara taso mata gadan-gadan wannan karon ko addu'ar ta gagare ta sai miƙa take tana lauyewa kamar maciji, wani irin abu mai nauyi ta ji an sakar mata shi akan ƙirjinta wanda ya yi barazanar ɗaukewar numfashinta in ta fesar da iska ba ta iya shaƙowa, nan da nan ta fita haiyacin ta ta dinga shure-shure kamar wacce take kan gaɓar mutuwa sai kumfa da ke fita daga bakinta idanuwanta sun kalli sama.. Ta jima a cikin wannan yanayin kafin daga bisani idanuwanta suka dawo daidai amma nauyin da take ji yana nan kamar ƙara mata ma shi aka yi, wani haske ta gani ya baiyana a gefen ta ya haske mata fuska aka dauke wutar ɗakin..
Cikin shiga ta kamala ta baiyana fuska ɗauke da murmushi, kallon ta Abir take har ta iso kan gadon ta zauna ta kai hannu ta shafa mata ƙirjin, ɗayan hannun ta ɗaura a kanta tana kallon ta cikin idanu. Kamar cirar ƙaya haka Abir ta ji zazzaɓin ya sauka har ciwon kan da nauyin ƙirjin duk babu su ras take jin ta, a hankali ta yaye bargon da ta lulluɓa ta tashi zaune ta fuskance ta tana kallon ta ba ko kiftawa. A hankali ta kama hannun Abir hakan ya sa Abir jan numfashi jin wani sanyi ya ratsa mata jiki, murmushi ta kuma yi ta ce "Hauwa'u duk na ga abin da ya faru da ke, amma ki yi haƙuri kamar yadda masoyanki ke faɗa miki, rashin auren Suhal shi ne alkhairi a gareki dan da Allah ya sa kuna da rabon aure to tabbas maƙiyan ki za su iya mayar da ke abin tausayi a idanun duniya. Yanzu haka ma baƙaƙen aljannu ne aka turo miki waɗanda za suke firgitar da ke in tsakiyar dare ta yi, so suke lalle dole sai kin bar duniya sun danne duniyarki da mahaifinki ya bar miki. Yanzu dai mafita ɗaya ta rage miki matuƙar ki na son ki samu salama a rayuwarki. " Ta faɗa tana kafe ta da kallo.
Sosai tsoro ya mamaye Abir tana jinjina lamarin, shin ita kaɗai ce me wannan baƙin jinin ko akwai wanda aka tsana irin ta a duniya? Me ta yi da ake son ganin lalle sai ta mutu? Girgiza kai ta yi cikin tsoro ta ce "Mama yanzu ni ba ni da damar da zan yi farin ciki a duniya? Me na musu da har ba a so a ɗaga ido a ga ina cikin walwala? Don Allah ki faɗa min su waye maƙiya na bayan 'yan'uwana?"
Tashi ta yi daga kan gadon ta koma jikin bango ta maƙale ta zauna kamar tana ƙasa, waro idanu Abir ta yi tana kallon ta cike da tsoro, ita kuwa ƴar dariya ta yi cikin ƴar siririyar murya ta soma magana.
" Hauwa'u kenan, ke dai ki dage da addu'a saboda maƙiyan ki sun fi masoyanki yawa a rayuwarki, ba kuma zan faɗa miki wannan mafitar ba za ki gani da idanuwanki kuma ki bi hanyar, sannan ba zan faɗa miki maƙiyan ki na waje ba har sai lokaci ya yi zan sanar da ke komai da kike tambaya ta. "
Rausayar da kai ta yi cikin rashin sanin madafa, to ita taya za ta bsamu sassaucin wannan rayuwa da take ciki? Nisawa ta yi ta dube ta ta ce "To amma Mama me ya sa ba za ki sanar da ni wani abu da ya shafi Zaiyan ba? Kin ga yanzu ni nake kula da shi ya kamata ki faÉ—a min komai nashi ta yadda in ya samu lafiya na sada shi da ahalinsa." Ta faÉ—a tana zubar da hawaye.
"Ki daina arhar hawayen ki a inda ba a san darajar su ba, ka da ki ce a gaban kowa za ki zubar da hawaye, in kuwa ki ka ci gaba da haka tabbas maƙiyan ki za su ci gaba da samun nasara a kan ki, lokaci ya yi da za ki shiga hankalinki ki nutse ki daina kuka a inda ba a san ke mutum ba ce. Zaiyan shi ne mafitar ki a daidai wannan gaɓar, ki jira lokaci zai nuna miki Zaiyan ne mafitar matsalar da kike ciki. "
Tana gama faɗin hakan ta ɓace ɓat kamar ba ta taɓa wanzuwa a ɗakin ba..
Dafe kai Abir ta yi tana jin komai ya cinkushe mata, Zaiyan da bai san ba kanshi taya zai zama maganin matsalar da take ciki? Buɗe idanu ta yi ta juya gefen ta ta lalibo wayarta ta ga har karfe biyu da rabi ta yi na dare, da sauri ta sauko ta nufi toilet ta dauro alwala ta zo ta tayar da Sallar nafila. Bayan ta gama ta ɗaga hannu ta na kwararo addu'o'in Allah ya kare ta ya mata tsari da duk wani abin cutarwa, ta yi wa Mom addu'a da Iman da Abdul da dukkan musulmai bakiɗaya sannan ta shafa. Sai da ta kwanta sannan ta janyo waya ta leƙa Tiktok dan ta ga me ke faruwa, da maganar auren ta ta fara cin karo a commet section mutane dayawa sun jajanta mata wasu har zagin Suhal suke suna ce masa mayaudari, runtse idanu ta yi ganin commet ɗin wata fans ɗin ta da ta jero ruwan ashariya tafi kala goma ta yi wa Suhal har da su tsinuwa. Gaba ta yi nan ma magana ake akan auren wasu har video daurin auren suka ɗaura, mutane da dama ba su ji daɗin abin da ya faru da ita ba, wani sanyi taji ganin kowa na alhinin abin da ya faru da ita ta yi gaba. Posting ɗin wani gaye ta gani mai suna da manyan marufa *BIG BOY* Ya yi posting ɗin video daurin auren ta tare da yin rubutu wanda yake nuna bacin ransa akan lamari.
_"Gaskiya Yarima Suhal ka zama cikakken mayaudari, na rantse da Assamadu da ace a Nigeria kake saboda da friend ɗi ta Abir in ban sassoka maka wuƙa ba shege nake, kai alƙur'an duk ranar da na gamu da kai sai na sare ma kafaɗa."_
Riƙe baki Abir ta yi tana ganin yan comment na goya masa baya, gyaɗa kai kawai take tana kallon ikon Allah masoyanta kowa sai da ya sa abin da ya faru da ita a fagen ɗin sa yana mai nuna alhini. Sai da ta ji bacci na fusgar ta ta aje wayar ta tashi zaune, ayatul kursuyu ta karanta ƙafa bakwai ta soma duk ƙafa ɗaya a kowacce kusurwa gabas, yamma, arewa, kudu, sama, ƙasa, ta karshen ta shafe a jikinta sannan ta karanta ƙulhuwa, falaƙi da saani tukun ta kwanta...
Hafsat ko ƙawayenta ba ta bari ba sun zauna an sayi baki ba ta zaro kuɗi daurin dubu ɗari ta ba su, da mamaki duk suke kallon ta wata yar ajinsu ta ce "Hafsy wannan fa?" Murmushi ta yi ta yaye mayafin da aka rufe mata fuska ta sauko daga kan gadon, kallon raini ta musu ta ce "My Husband ne ya ce ba ya son surutu dan haka ya ba ni kudin sayan baki da kun kawoni na ba ku ba sai kun jira shi ba." Ta faɗa tana cire ɗankwali ta yi jifa da shi..