Sashe 97
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wata rana ta sake zuwa ta ce min na yi mata aikin da zai yi ajalin matar wanda take so dan ita ta tsani kishiya musamman ma wadda za ta tarar, haka na mata aiki ta tafi tare da aje min kuɗi, bayan wasu kwanankin ta dawo ta ce min ai buƙata ta biya matar ta rasu har ma an yi sati biyu da mutuwar, nan ta ce na sa a takurawa shi mijin matar ace sai ya yi aure kuma ita zai aura tun da ɗan'uwanta ne shi, haka na mata aiki babu jimawa aka yi auren su ita da shi, tun daga lokacin da kalar aikin da da ta zo da shi, ta zo na yi wa mijinta aiki akan duk wani nema nasa ya zamana yana tafin hannunta. Haka take zuwa na buƙatata da ita nake biya mata tata buƙatar har ta haifi ƴarta ta farko, a lokacin ta zo min da cewa matar da aka yi wa aiki kar ta haihu tana nan yau ta haihu na yi wani abu a kai, na buga ƙasa amma na kasa yi mata komai a lokacin na ce ta bari har sai yarinyar ya ɗan girma tukun sai ta zo ayi komai. To bayan wasu shekaru ta dawo na mata aiki aka daurawa yarinyar cutar asmah, tare da baƙaƙen aljannu wanda za suke tsotse mata jini tana ramewa kar ta girma ballantana kyanta ya ƙara bayyana ta riga yaran su a aure, babu muso na mata aiki ta aje min kuɗi masu yawa ta tafi, wata rana ta dawo ta ce na yi mata aiki akan Yayan mijinta ya yi wa wannan Mamar yarinyar kishiya ya auri ƙawarta, na buga amma na kasa saboda kullum cikin tsarin Ubangiji mijin yake, a lokacin ita kan ta matar ta dukufa da neman kariya shi ya sa na ƙasa musu komai dole ta haƙura . To can baya ta zo ta ce na sa yarinyar da ɗan kishiyarta su dinga lalata har su samu ciki ba wanda ya ankara har sai cikin ya fito, na ce to ta tafi amma na kasa yin wannan aikin har wani abokina na sa ya tayani amma shi ma ya kasa, ganin haka ya sa ta ce a mayar da yaron ya zama kamar mace ya kasa amfanuwa ta fannin auratayya, nan ma bai yiyuba. Watanni kaɗan da suka wuce ta zo ta ce min uwar yarinyar ta rasu amma kafin ta rasu an soma maganar auren ƴar. Nan y asanar da ita yadda suka yi har aka fasa auren Abir da Suhal ya dawo kan Iman.. "
Laraba da hawaye ke bin kuncinta ta fusata ainun ta tashi ta zabga masa mari, nuna shi da yatsa ta yi ta ce " Mugu azzalumi ci gaba ina jin ka wanda ya dauke kayansa daga gaban rahamar Ubangiji. "
Sosai ya ji marin ya shige shi, ya dafe kunci ya ci gaba da cewa "Aikin da na mata na kusa-kusar nan shi ne na yi wa duka Familyn nasu aiki suka tsani yarinyar, babu wanda yake damuwa da ita har shi wannan Yayan nata, nan ma dai bayan lokaci ta zo ta ce a yi mata aiki yarinyar ta tubure ta ce wani mahaukaci da take jinya shi take so a aura mata, haka kuwa aka yi nan da nan sai ga aiki ya kama yarinyar ta tubure a satin aka ɗaura musu aure, karshe ma ta kuma cewa a kaɗa su su bi duniya daga ita har mijin su wahala har su mutu. Na yi aiki cikin dare inda aikin nawa ya zo aka gaɓa ranar Yayanta ya je ya mata duka, na raba mata hankali ta rasa sukoni ta tattara kayansu ta bar gidan, na sa duk familyn nasu suka manta da shafin rayuwarta babu wanda yake son ayi masa maganar ta indai dan family su ne, yanzu kuma ta zo ne ta ce min tun da na gano inda suke nasa mijin ya mata faɗe na fitar haiyaci, wanda za ta kamu da cutar yoyon fitsari ta ruɓe. Yanzu haka maganar da nake miki tuni na gama yin aikin akan mijin kuma take ya isa gare shi." Ta faɗa yana zare idanu..
Laraba ta yi saƙare tana jin kalar rashin imani irin na wannan malam bokan, dauke kuɗin ta yi ta ce "Maza ka warware aikin da ka yi wa mijin nata yanzu."
Rausayar da kai ya yi ya ce "Hajiya ai ko da zai warwaru to fa sai nan da kwana uku."
"To naji warware in kwana ukun ya yi sai sihirin ya bar jikinsa, sannan ka warware na Family da mijinta, cutar da ka saka wa baiwar Allah ka warware mata kafin na fasa kanka da bindiga, su kuma sauran bayin Allah da ka cuta sun mutu za ka je gaban Allah ku haÉ—u a can."
Tana zaune sai da warware na Family tas da Daddy na Abir duk ta sa ya warware su duka, ta kuma mishi barazanar cewa duk ina ya gudu dan ya tsere musu suna da mutane a kowacce Jaha, duk inda ya shiga a faÉ—in Nigeria za su kamo shi su kashe, kuma ya kuskura ya sanar da Umma ya warware aikin da yake mata zai ga abin da zai same shi, to ya dinga faÉ—i yana Allah-Allah ta bar gidan dan wani zawo yaji ya tafo masa , tana fita ya runtuma a guje banÉ—aki sai karan zawo kake ji...
Tana fitowa ta goge hawayen da suka zubo mata ta shiga motar suka bar wajan, yau ta ji abin da ya girgiza mata masarrafa sai share hawaye take tsananin tausayin Abir na ratsa mata zuciya...
_Maman Nusaiba ce_
[11/30, 2:03 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na (48)
Yau tun bayan Sallar Asubahi Gandma ta fito palo tana shige da fice ko za ta ga kiftawar Abir amma shuru har ƙarfe tara ta buga ba ta fito ba, mamaki sosai ya kama ta ta zauna kan kujera tana kallon ƙofar ɗakin, ganin dai lokaci na tafiya ta nufi ƙofar ɗakin ta soma kwankwasawa tana faɗin "Ke kasa uwar bacci ki tashi ki fito rana ta take kina shema bacci, maza ki fito so nake ki rakani Ruga yau." Shuru ta ji ba a amsa mata ba sai ta murɗa ƙofar taji a kulle ɗakin, kwafa ta yi tana cewa "Ƴar banza mai zubin taliya ƴar murji, mutum ya neme ki da abin arziƙi ma sai kin nuna masa isa da izza kamar jinin sarauta, yo ko ke ce Suhal ai sai haka busasshiyar banza jiki duk ƙashi, daga yau ma kin daina rakani in zan je Rugar sai na ga ta inda za ki ga kayan tarihi iri da namu na Fulani. " Tas ta gama sababin ta amma shuru ko motsi ba ta ji ba na alamar za a buɗe mata kofar, ta dawo ta zauna tana kaɗa kai sai ga Abba ya iso palon shi da Daddy Fatima na riƙe da hannun Abba, zama duk suka yi tare da gaishe ta tana kaɗa ƙafa ta amsa sai hura hanci take, Abba da ya gane hakan sai ya rausayar da kai ya ce "Inna ke da wa da farar safiyar nan?"
Tsaki ta ja ta ce "Ni da Hauwa'u mana, ina ta kiran ta ta yi mursisi taƙi fitowa daga ɗaki." Kafin Abba ya ba ta amsa Fatima ta yi caraf tana dariya ta ce "Kai Grandma da alama rikicin tsufa ya soma kawo miki ziyara, Baby da ta jima da yin aure me kuma zai kawo ta ta zauna a gida ga gidan mijinta?"
Duk kallon ta suka yi baki sake, Inna ta zaburo ta watso mata daƙuwa ta ce "Ingo nan dan cucun uwaki Faɗima, Hauwa'un ce ta yi aure ba tare da mun sani ba? To uban wa ma ta aura in har da gaske kike? Sannan wa ya ɗaura mata aure? Nasan dai su Sulaimanu ba za su mata aure ba su shawarceni ba."
Abba ya yi shuru yana son tuno yaushe suka mata aure amma ya kasa, hankalinsa ya tashi jin yadda Fatima ke rantsuwa da zatin Allah Abba da Daddy da Abdul da Salim da Daddyn Aruf ne suka ɗaura wa Abir aure, kuma a ranar suka ce ta bar gidan ta tafi gidanta. Kuka Grandma ta sa tana tafa hannu tana kallon su, su kansu sun rasa me ya shiga kan su har suka mata wannan cin zarafin a matsayinta na ɗiyar yayansu kuma amana a gare su, Abba ya miƙe tsaye yana zarya dan duk cikinsu ya fi su shiga tashin hankali idan ya tuna yadda ɗan'uwansa ke jaddada masa ko ya riga shi mutuwa a riƙe masa Abir amana. Number ta ya lalibo ta kira ya danna mata kira, sai aka ce masa an yanke layin, zama ya yi yana kallon Daddy da shi ma ɗin shi yake kallo ya nisa ya ce "Ko kana da ɗayar number ta?"
Girgiza kai Daddy ya yi dan ya ma kasa yin magana, Abba ya ce Fatima ta ba shi dayar number Abir ta ce ita ai ba ta ma da numbobin ta ko ɗaya, tashi duk suka yi suka ce wa Grandma za su nemo duk inda Abir take. Kuka sosai Grandma ta dinga yi tana faɗin "Kai jama'a! Kenan dai da gaske sun aurar da yarinyar nan? To ni kuma ina wani waje har aka yi hakan ban sani ba?" Tunawa da Laraba ya sa ta tashi ta nufi ɗakin Laraba tana kwaɗa mata kira, murɗa ƙofar ta yi ta ga babu kowa a ɗaki sai gado da drower, haka ta juyo tana sallami ta dawo ta zauna duk ta rikice, can dai ta tuna Laraba ta tafi wajan ahalinta sannan ta ji sauki ta koma kan labarin jikartata..
Ko da Abba ya fita sai ya koma part É—insu ya samu Ammi zaune tana chatting, ganin sun dawo ne ya sa ta É—ago kai ta kalle su cike da mamaki ta ce "Abbansu lafiya kuka dawo?"