← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 120

Sashe 23

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an gama yi wa Abie wanka aka kira ɗaya bayan ɗaya suka dinga masa addu'a, Abir ita ce ƙarshe tana kuka tana kiran sunan Abie da ƙyar aka ɓamɓareta daga ruƙon da ta yi wa gawar Abie aka fito da ita palo, ba ta ƙara rikicewa ba har sai ta ga an ɗauko Abie a makara za a wuce palo ta yi wani irin kukan kura ta kwace ruƙon da aka mata ta nufi mazan da suke shirin barin palo.

Da mugun sauri Abdul dake bayan su ya yi saurin tare ta ya ɗauke ta cak ya nufi ɗakinta, ita kuma kuka take tana faɗin "Yaya Abie na Wallahi bai mutu ba ka ce su bari na masa magana zai tashi." Tana gani suka bar palon ta kwalla wani irin ƙara sai ta saki jiki a jikin Abdul, a ruɗe ya kwantar da ita a kan gado ya ɗauko ruwa ya shafa mata a fuska ta ja ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da buɗe idanunta. Ganin shi a kusa da ita yasa ya faɗa jikinsa tana kuma sakin wani kukan..

Bai hana ta yin kukan ba har sai da ya ga taƙi bari sannan ya ɗago da ita, sake komawa ta yi cikin jikinsa tana ci gaba da kuka ya kuma ɗago da ita zuciyarsa na masa wani irin azababben zafi, dafa kafaɗunta ya yi cikin wata kalar murya wadda bai san yana da ita ba ya ce "Babyyy." Ya ja sunan idanuwansa sun cika da hawaye suna ƙoƙarin zubowa shi kuma yana ƙoƙarin mayar da su. Cikin kukan ta ce "Ya.. Yaya Abie na." Ta faɗa cikin shashshekar kukan da har ya kai muryarta ta disashe. Kamo hannunta ya yi yana murzawa a hankali bai ce da ita komai ba ita kuma tana kuka ta ƙura masa idanu, sai da ya ji ta yi shuru sannan ya ɗago da idanunsa wanda suka tashi daga farare suka koma jajur kamar an watsa masa barkono ya soma yi mata magana.

"Ki yi haƙuri kin ji, kukan ba shi da wani amfani Addu'a Abie yake buƙata ba kuka ba, tashi ki wanke fuskarki ki zo ina jiran ki." Ya faɗa yana miƙar da ita tsaye ya ja ta suka nufi toilet. Ganin ta ki yin komai ya janyo ta ciki ya isa bakin famfo ya wanke mata fuska sannan suka fito. Da ƙyar ya rarrashe ta yana mata nasiha tukun ta yi shuru har ta yarda suka fito palon ya zaunar da ita a kusan Grandma ya fita zuwa maƙabarta...

Yana zuwa ana saka gawar Abie a cikin makwanci ya runtse idanu yana karanto Addu'o'in nema wa Abie yafiyar Ubangiji, yana tsaye aka gama aka bar su Abba a kan ƙabarin suna ta Addu'a shi ma ya tsugunna aka yi da shi sannan suka tashi...

Bayan an dawo daga maƙabarta aka kafa runfuna a harabar gidan. Tuni labari ya yadu a cikin gari da waje An tsinci gawar Shahararren ɗan kasuwar nan Alhaji Ibrahim Abdullahi Maitama bayan shafe watanni da ya yi ba a san ba inda yake.

Kowa na ta tofa albarkacin bakinsa duk inda ka nufa a cikin garin Yola maganar ake ko Social media ka hau da labarin za ka ci karo, wasu na cewa ƙila abokan kasuwancinsa ne suka kashe shi, wasu kuma su ce makiya ne a wani waje da ban kowa na faɗin ra'ayinsa..

Haka aka yi ta karɓar 'yan gaisuwa daga garuruwa daban-daban kama daga kan abokan Abie na kasuwanci da yaran da suke aiki a kamfaninsa da abokansa wasu garuruwa, gidan kullum haka ake wuni ana tabar ɓaki. Mommy kuwa ba ta cewa i ba kuwa ta cewa a a, tana zaune tana kallon kowa da haka aka yi sadakar uku ya rage sai 'yan'uwa na kusa a gidan. Ana yin sadakar bakwai kowa bayan an yi Addu'o'i sauran mutanen da suka rage suka tafi aka bar na gidan.

Bayan sati biyu

Yanzu Abir ta sadakar da cewa lalle fa Abie ɗinta ya mutu, gabaɗaya ta ƙara koɗewa duk da ita ɓaka ce amma sai ta yi fari saboda kullum da zazzabi take kwana, Abdul na ta kula da ita har Mommy kanta da take cikin takaba haka take wuni da ciwon kai, Grandma kuwa su Abba ke mata jawafi suna zuwa su daɗe a wajan ta sai sun ga ta saki ranta sannan su tafi..

A haukace Alhaji ya dawo daga Germany sakamakon wayar da yaran suka buga masa suna sanar da shi yaron da suka kawo fa sun neme shi sun rasa a gidan, hankalinsa ya tashi matuƙa hakan yasa ya cire ticket ya dawo Nigeria ko gidansa bai isa ba ya wuce gidan da suke. Haka ya dinga faɗa yana yin wurgi da duk abin da yake kusa da shi, Nadumbuza ya dakatar da Alhaji ya ce "Matuƙar kana son ci gaba da komai naka dole sai ka kawo mana jinin ɗanka an yi aiki da jininsa."

A gigice Alhaji ya ce "To amma Nadumbuza me zai hana ka yi aikin ka daga nan ba sai na kawo shi ba."

" A a bari na tambayo Uwa Dudu naji mai za ta ce a kan hakan." GyaÉ—a kai kawai Alhaji ya yi shi kuma Nadumbuza ya tafi wajan Uwa Dudu, bai É—auki lokaci ba sai ga shi ya dawo yana dariya, ganin haka yasa Alhaji ya ja dogon numfashi sannan ya ce da shi "Ya dai Nadumbuza?."

"Uwa Dudu ta ce za ta yi ma alfarma É—aya tak."

Da sauri ya ce "Wacce kenan? Ba na so ne a kawo shi nan ina so ayi komai ta yadda ba za a gane ba."

"Ta ce ba sai an kawo shi ba nan, ita za ta ji da komai."

Dariyar farin ciki Alhaji ya yi yana cewa "Uwarmu maganin kukanmu."

Har ya juya zai fita Nadumbuza ya ce "Alhaji ina buƙatar a kawo min yarinya ɗaya na kashe ƙishina a kanta."

Dariya su duka suka ɗauka suna kallon Nadumbuza wanda shi ma dariyar yake, ɗaya daga cikin su ya ce "Nadumbuza mai abin mamaki yo ni na ɗauka irin ku ba sa buƙatar mace."

Shafa ƙasumbarsa Nadumbuza ya yi ya ce "Wa ya ce maka? Ai mun ma fiku son hakan." Dariya suka kuma yi Nadumbuza ya ce Alhaji ya zo kafin a kawo masa yarinyar ya ce to suka shige wani ɗaki wanda daga shi sai Nadumbuza suke shiga..

Ɗaki ƙarami daga ciki yana da ƙofa uku, a tsakiyar ɗakin suka tsaya Nadumbuza ya aje sandar shi cikin sauri ya cire hular fatar da ke kansa yana faɗin "Ka yi sauri fa Alhaji kar ka karya aikin ka."

Da sauri shi ma Alhaji ya cire kayan jikinshi, Nadumbuza ya ɗauko wata gwalba daga cikin aljihunsa ya lakato wani mai wari, jikin Alhaji ya shafe man yana wasu irin yare. Bayan ya gama yana daga tsayen suka dinga aikata luwaɗi shi da Alhaji, (Allah ya shirya mana al'ummar musulmi). Sai da suka kammala Nadumbuza ya ɗauki wata allura ya soka a jikin Alhaji yana yin yarukan tsafi, jini kaɗan ya fito ya janyo wani ƙyalle fari mai ɗan girma da ke gefen su. Goga jinin ya yi a jikin ƙyalle yana wani irin nishi kamar mara lafiyan da jiki ya yi tsanani, Alhaji ya sunkuya ya ɗauki kayan shi ya mayar ya gyara.

"Za ka iya tafiya Alhaji ka ji daɗin ka, ka yi duk abin da kake so a duniyar nan na tsaya maka." Cewar na Nadumbuza yana nannade ƙyallen.. Murmishin jin daɗi Alhaji ya yi ya fito daga ɗakin, sai da ya yi wa yaran gidan kashedi kar su kuma sake yin sakaci su kula 'yan matan da ke gidan duk da yasan babu ta inda za su a wannan gurin da suke su gudu daga gidan. Da to suka amsa ya ciro 'yan rafa ɗaurin dubu ɗari-ɗari ya miƙa wa kowanne, cikin jin daɗin suka masa shi kuma ya yi tafiyar sa yana jin kansa na ƙara girma ya zama fitaccan mai kudi...

Doctor Hashim ne ya kira Abdul yake sanar da shi Zaiyan ya farka amma lamarin nasa sai a hankali saboda duka yake kai wa duk wanda ya nufi inda yake, sun samu da ƙyar sun masa allurar bacci ita ma nan da minti kaɗan zai tashi, dan haka ya sa ya yi maza ya zo su san abin yi. Lokacin yana zaune a ɗakin Abir yana nuna mata wasu kadarori na Abie da ke cikin garin Abuja, bayan ya gama wayar ya sanar da ita ta ce masa su je tare, bai musa ba suka fito ya sanar da Mom abin da ke faruwa sannan suka tafi..

Lokacin da suka isa likitoci sun rirrike shi yana ta faɗin "Ku sakeni na tafi wajan Anty." Abin da yake faɗa kenan yana ƙoƙarin kwacewa daga ruƙon da suka masa. Da sauri suka iso cikin ɗakin a daidai lokacin ya masge wani likita tuni ya faɗi warwas, ya yunƙura zai sauko suka kuma riƙe shi ya kwace ya sauko zai fita ta yi saurin damƙar hannunsa.. A zabure ya juyo ya kalle ta, kallon ta yake ba ko ƙiftawa yana ɗaga kai sama zuwa can kuma ya Shagwaɓe fuska tare da juyowa gabaɗaya ya tsaya gaban ta, raurau ya yi da idanu irin na yaro in ya ɗauki tsayin lokaci bai ga mamansa ba. Hanunsa ya ɗaura akan nata sai gani ta yi ya soma kuka yana langaɓar da kai ya ce "Antyyy.!!"

_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_

[10/25, 3:55 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_

*Arewabooks.com: Saratalkasum1897*

_+966577675904_

Shafi na (14).
Chapter 23 · 0% Book details