← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 120

Sashe 107

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda tsananin tashin hankali ban san lokacin da na miƙe tsaye dafe da ƙirji ba, baki na rawa na ce "Mo.. Mom da gaske kike Anty Khairat ba ɗiyar Daddy ba ce? To a ina shi uban nata yake? Amma dai Iman ɗiyar Daddy CE Ko? Don Allah kar ki ce min itama Iman ba jinin gidan nan ba ce." Na faɗa hawaye na ambaliya kan kumatuna.

Kamo hannuna Abie ya yi ya zaunar yana bi na da kallo ya ce "Ai duk yadda kike tunanin Baraka da wuce haka ita da É—an'uwanta Sadisu."

Jinjina kai Mom ta yi ta ce "Tabbas haka ne ba ƴar gidan nan ba ce, ni da kaina na kama su dumu-dumu suna aikata zina ita da malaminta lokacin ba a fi wata biyar da auren su ba, sannan kuma daɗin-daɗawa Kabir ba shi da lafiya a lokacin, ni da Abie ɗin ki muka kai shi Asibiti lokacin yana cikin tsananin kewar ƴar'uwata. Dalilin kai shi Asibiti kuwa shi ne, hatsari ya yi na mota wanda har ya samu rauni a mararsa ba wani mai girma ba, hakan ya sa kawai aka sa masa magani sannan suka sanar da mu ba matsala in sha Allah, bayan sati sai abin ya zo da wani irin yanayi ko fitsari Kabir zai yi sai ya sha azaba. Ganin haka ya sa Abie ɗinki ya kira family Doctor ɗin su ya zo ya duba shi ƙarshe ya ce mana gaskiya sai an je asibiti ya masa gwaje-gwaje dan akwai abin da ya kasa ganewa, muka shirya muka tafi da shi aka masa komai washe gari muka koma amsar result, bayan mun je nan yake sanar da mu Kabir ba zai sake haihuwa ba a halin yanzu saboda jijiyar da ke haɗe da kwayoyin halittar haihuwarsa ta taɓo sosai, amma ya ce zai ɗaura shi akan magani na wata takwas idan har bai ji sauyi ba to sai dai ya tura shi ƙasar waje wajan wanda suka fi shi kwarewa. Hankalinmu a tashe muka dawo gida sai shi Kabir ɗin ne ma yake kwantar mana da hankali, na dauki waya zan kira Mama na sanar da ita abin da yake faruwa su dakatar da aura masa Baraka amma fir Kabir ya ce kar na faɗa musu halin da yake ciki hankalinsu zai tashi fiye da namu, da farko na ce masa sam sai na faɗi amma ya yi ta haɗa ni da girman Allah dole muka ja bakinmu muka yi shuru, shi kuma ya ci gaba da shan maganin da aka ɗaura shi dan lokacin saura sati biyu a ɗaura aurensu da Baraka.

Tun da aka yi auren ba ya kwana a ɗakinta itama kuma ba ta damu da hakan ba, haka zai gudo part ɗinmu ya shiga ɗakin da yake nasa ne kafin ya yi aure ya kwanta, wani lokacin ma ba ma sanin ya zo har sai mun fito muna karyawa sai mu ka ya fito.. Auren su da wata uku ranar Baraka ta kama rashin lafiya muka nufi Asibiti da ita, gwajin farko aka sanar da mu cewa tana dauke da ciki na tsayin wata biyu da sati ɗaya, na girgiza sosai da jin wannan batu da farko sai na yi tunanin ko dai ya samu lafiya ne? Hankalina ya kasa kwanciya na ce ya rakani Asibiti dan kar ma yaƙi zuwa ban ce shi za a duba ba, shi kuma sai murna yake wai zai ƙara zama Daddy. Bayan mun je aka nuna masa waje aka ce ya kwanta, kallona ya yi ya ga ba wasa a fuskata sai ya nufi inda suka nuna masa, bayan an gama gwaji aka tabbatar min da har yanzu ba a samu wani solution ba game da rashin lafiya tasa, sai dai a bari ya gama shan maganin a gani. Ranar da muka dawo ya daina kwana a part ɗin mu ya koma nasu, ranar da zan yi mugun gani ta zo part ɗina ta ce min na yi mata ɗanwake tana so, sai na ce to na tashi na mata na aje ina jiran ta zo ta amsa amma shuru, hakan ya sa na tashi na nufi part ɗinsu ina ta kwaɗa sallama amma shuru.. Har zan juya na ji surutu a ɗakinta hakan ya sa na nufi ɗakin dan a lokacin Kabir ya fita aiki zuwa Abuja, ɓude ƙofar da zan yi na gan su haihuwar iyayensu ita da wani gardi na kwashe salati. Sun tsorata da ganina ta kama kukan ƙarya tana ce min na rufa mata asiri ba za ta sake ba, haushi ya sa na daka mata tsawa na ce ta sanar da ni gaskiya tun yaushe take cin amanar mijinta? Ta ce ai tun kafin ta yi aure suke aikata iskancin su, hakan ya sa naji tashin hankalin da nake ciki ya ƙaru na kuma ce mata ta faɗa min shi ne wanda ya mata cikin ko kuma na Kabir ne?

A lokacin ta kuma sa kuka ta ce "Wallahi ba na Kabir ba ne nasa ne, tun da na shigo gidan nan ban taɓa haɗa shinfida da Kabir ba, dama can ni ba shi nake so ba mijinki shi nake so."

Na dinga nanata Kalmar Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Na mata faÉ—a sosai sannan na fita na bar su a É—akin. Ko da na dawo ka rasa taya zan sanar da Kabir dan shi a lokacin ta gama shanye shi ba ya jin maganar kowa sai maganarta, ashe wai Malaminta ne da yake mata aikin akan duk wanda take son hawa kansa, na ji hakan ne bayan ta zo part É—ina ko kunya babu take cewa Kabir wai ita ya kaita England a can za ta haifa masa Baby, shi kuma sai murna yake na bi shi da kallon tausayi. To bayan ya tafi ne sai na shige É—aki zan dauko wani abu ina fitowa naji wayar da take da shi, inda take sanar da shi wai aiki ya ci ban tona musu asiri ba kuma Kabir ya amshi cikin a matsayin nasa. Ban nuna naji komai ba...

Da haka har ta haifi Æ´arta mace wadda aka sa mata suna Khairat, yarinyar kana kallon ta sak ubanta ce kamar ya yi kaki ya tofar...

Sai da aka daɗe da yaye Khairat a lokacin ne kuma ta Kabir ya samu lafiya, bayan wani lokaci aka haifi Iman. Iman tabbas ɗiyar Kabir ce dan har gwajin jini sai da na kai ta aka yi mata ita da Kabir, a lokacin in da za ki tuna mun je amsar maganinki. " Ta ƙarashe maganar tana jan dogon numfashi..

Kamar an yi ruwan ƙanƙara a jikina haka na dinga rawar sanyi, sai da Abie ya taɓa ni sannan na ɗan ji sauki na goge hawayen tausayin Khairat. Tun daga ranar da na kalle ta sai naji idanunwa sun cika taf da kwallar tausayinta ina tuna ranar da za ta san ko ita wace ce a gidan nan... "

Kuka ne ya ci ƙarfinta ta faɗa jikin Zaiyan, Tun da aka fara labarin jikin kowa ya yi sanyi, Khairat kuwa kuka take bil'haƙƙi tana kallon Umma da ta yi tsuru-tsuru sai muzurai take babu alamar nadama a tattare da ita..

Sai da ya rarrashe ta sannan ta daina kukan ta kalle su ɗaura da cewa "Bayan sun ba ni labarin nan sai Abie ya dauko wani ɗan ƙaramin abu kamar memorie ya ba ni ya ce na adana shi kar na bari kowa ya san da shi, ya kuma tattara takardunsa na filaye da duk wata kadara tashi ya ba ni su ita kuma Mom ya ba ta wata takarda ya ce ta aje masa. Bayan mun gama karyawa ya ce na zo na raka shi gidan gonarsa ina murna na janyo Hijabi muka wuce..

Muna isa ya zazzagaya da ni inda ake kiwon kaji, har mun juya za mu dawo sai ga Umma ta shigo ita da Daddyn Aruf da abokansa Daddyn Hafsat da Jarmai da Manager Abie. Da mamaki ya kalle su ya ce "Yaya Ku ne a gidan gonar tawa ba ko sanar wa?" Dariya suka yi masa sai abin ya ba shi mamaki, Daddyn Aruf ya ce da Abie, "Kai Ibrahim miƙo mana wannan memorie."

Murmushi ya yi ya ce "Ai Wallahi ko me za ku yi ba zan ba ku ba, ashe ku ne azzaluman da suke safarar 'yan mata ƙanana? Wallahi Yaya Sadisu ka ba ni matuƙar mamaki, ban taɓa tunanin zaman da kake a England safarar Mata kake yi ba,in sha Allah sai na kai wannan bayanin wajan babban kwamishinan 'yan sanda. Ke kuma marar kunya futsararriya fasiƙa ki fita idona na rufe, zan sanar da Kabir duk rashin darajar da kike min."

Dariya duk suka saka Manager ya dawo gefen Abie ya ce"Ni ma bana goya bayan su kuma in sha Allah da ni za ka je kai wannan ɓannar da suke yi, Wallahi Alhaji Mustapha kun ba ni mamaki matuƙa."

Ganin Manager ya dawo wajan Abie sai suka shiga ba wa Abie hakura shi kuma ya nuna sam ba zai ba su abin da suke so ba, haka suka fita suka bar wajan.. Sai da Yamma mun dauko hanyar dawowa muna cikin tafiya kawai sai ga wasu ƙarti sun tare mana hanya, a lokacin hanyar banki muka nufa saboda Abie zai kai kuɗinsa. Haka suka zagaye motarmu wasu suka fito da Abie wasu kuma suka fito da ni suka sa mu a cikin motocinsu tare da rufe mana idanuwa, muna ji ana ta tafiya da mu sai dare sosai muka ji an tsaya a wani waje, haka suka sauko mu suka dinga jan mu muna bin su idanu a rufe. Suna ɓude mana fuska nan muka yi arba da su Daddyn Aruf, zabura na yi na maƙale a jikin Abie na sa kuka Umma ta dauke ni da mari tana huci ta ce "Idan har ubanki yana son ki to ki ce masa ya yi mana abin da muke so." Kallon Abie na yi tare da ce masa, "Abie don Allah ka ba su kar su taɓa lafiyarka mu koma gida."

Girgiza min kai ya yi ya ce "Sam ba zan yarda na ba su ba ki rabu da su."
Chapter 107 · 0% Book details