← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 120

Sashe 80

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Godiya ta masa suka isa tasha ya kai ta wajan abokinsa lokacin yana lodin Kano, bayani ya masa ya amshi kayan nata ya sa a bayan mota ta juyo ga wanda ya kawo ta ta ce " Na gode sosai bawan Allah ga wannan. " Ta miƙa masa dubu goma ai kuwa ya dinga mata godiya yana jaddada wa abokina ya kai ta har inda take so ya ce kar ya yi wasa wani abu nasu ya ɓata ya amsa da to, shiga motar suka yi daman ta cika mai motar ya ja suka hau hanyar Kano.....

Ga duk mai son cigaban labarin nan ya nemeni ta wannan number.

*+966577675904*

_Maman Nusaiba
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na (39)

Tun da suka shiga mota Abir kuka take tana kallon gefen hanya, kukan rabuwa da ahalinta da kuma rashin sanin inda za ta je in an sauke ta a garin Kano take. Sai da suka kusa isa Kano cikin wani daji motar tasu ta yi wani kalar ƙara ta yi gaba ta yi baya kafin ta tsaya, hankalin waɗanda suke cikin motar ya tashi ci kuwa har da Abir dan ta ma fi su firgicewa ganin inda suke tsaye, ƙanƙame Zaiyan ta yi da ya rungume ta ya kwanto da kansa bisa kafaɗarta tana mayar da numfashi. Mai motar da yaron mota suka fita dan ganin abin da ya samu motar, duddubawa suka dinga yi inda suka ga tayar motar ce ta fashe yaron motar ya dawo wajan masijojin nasu yana fadin "Ba wanda ya samu rauni duk kuna lafiya?" Ya faɗa yana shiga cikin motar tare da dudduba su. Wata mata da ke zaune a gefen su Abir ta kalli yaron motar tana haki ta ce "Wallahi sai da na suma na wucin gadi, wagga wacce irin mota ta haka? Shin dama motarku na da matsala ba ku hwada ba?"

Haƙuri ya dinga ba ta tana sababi ita da mijinta har ya samu suka hakura, Abir ta yi tagumi tana jin matsananciyar faduwar gaba.

Rana har ta soma sanyi anan suka yi La'asar ƙarshe ma duk fitowa suka yi kowa ya samu waje ya zauna, su kuma suna ta ƙoƙarin kunce ganin sun canja tayar ko sun tafi daga cikin dajin, ana haka sai ji suka yi ana dirowa daga kan bishiyoyin da ke zagaye, kowa ya ruɗe ganin gardawa sun fi goma tsaye gaban su fuskokinsu a lulluɓe, haka ma hannayensu riƙe yake da bindugu manya-manya sai zare idanu suke. Tsawa suka daka musu suka ce duk su zauna a waje ɗaya, wasu da rarrafe ma suka iso inda aka nuna musu, Ta Sakkwato da mijinta har sun fi kowa shiga ruɗu, Direba suka damƙo cikin rashin imani suka yi boll da shi ya wuntsila ya faɗi a kan Zaiyan da ke jikin Abir har lokacin bacci yake wanda bacci nasa ya ba wa Abir mamaki ganin hayaniyar da ake ba ta sa ya tashi ba. Ɗaya bayan ɗaya suka ce kowa ya zo ya fito da abin da yake jikinsa ko ya yi ta ransa, haka maza suka fara zuwa ana lalibe su har takalman su ake cewa su cire ko sun maƙala kuɗi a nan, bayan an gama aka kira mata wanda dukan su su shida ne, kowacce ta zo sai suce ta cire dankwali ta fito da komai na jikinta har su warwaraye da sarƙa duk sai an amshe. Ganin hakan ya sa Abir ta laliba sarƙarta wadda ta kasance ta gold ce da Abie ya saya mata a matsayin kyauta lokacin da ta yi candy, sai da Kowa ya je ita ce ƙarshe ta tashi a hankali ta kwantar da Zaiyan a dandan ƙasa ta mike ta isa wajan mai amsar kaya, ɗankunne ta ba su da sarƙarta har zoben da Abdul ya saya mata da jimawa aka ce sai ta fitar da ita, haka ta cire tana zubar da hawaye suka ce ta cire ɗankwali ko akwai abin da ta ɓoye ta cire suka ga ko kitso kan babu tukun suka ba ta umarnin tafiya.

Har ta kai gwiwowinta ƙasa za ta zauna ta ji ɗaya daga cikin su ya daka mata tsawa ya ce "Shi wannan na kwancen uban wa ya ce yaƙi tashi mu lalibe shi?"

Jikinta ne ya ɗauki rawa da kalle shi ta kuma kalli Zaiyan da ita kan ta baccin nasa ya dame ta, baki na rawa ta ce "Wallahi babu komai a jikinsa hasali ma ba shi da lafiya shi ya sa ka gan shi haka." Ta yi maganar tana riƙe hannun Zaiyan.

Dariyar basawa babban su ya yi cikin taku irin na rikakkun gardawa ya tako ya iso gaban Abir ya tsaya tare da ɗaura bindiga a gadon bayan Zaiyan ya ce "Idan har kina so mu rabu da shi to sai dai ki zaɓi ɗaya a cikin biyun nan da zan faɗa miki, ko ki ba ni kanki mu zagaya ta can baya ko kuma na kashe shi sai ki zaɓa." Ya faɗa yana taune lips ɗin sa na ƙasa. A mugun firgice Abir ta ɗago ta kalle shi ta haɗe hannaye biyu ta ce " Don Allah ku min rai karku wannan zaraɗin ya min tsauri dayawa, idan har kuɗi kuke so zan ba ku ina da shi a jakata sai na ba ku, amma ka da ku kashe min miji Wallahi ba shi da la...

Marin da ya zabga mata ne ya sa ta yin shurun dole, yana huci ya ce "Na ma fasa ba ki zaɓin dole ki amshi buƙata ta, kai gabaɗaya matan nan sai mun zagaya su dan na ga alama har bakin magana kuka samu, kai Bangis ɗauke ta ka kai min ita in na gama sai ku zo ɗaya bayan ɗaya." Yana gama fadin haka ya ja da baya ya harɗe hannu yana bin ta da wani irin kallo. Daƙas-daƙas Bangis ya nufo Abir fuskarsa kan ta abin tsoro ce, ganin dai da gaske ɗaukan ta za su yi ta kama hannun Zaiyan ta fashe da kuka tana fadin "Zain don Allah ka tashi ka ceceni a hannun waɗannan marassa imanin za su keta min haddi." Jijjiga shi take amma sam ko motsawa bai yi ba sai ma wani irin gurnani da yake kamar mai ciwon farfaɗiya in ciwon ya tashi, Bangis ya kama hannun Abir yana daka mata tsawa ya dinga janta a ƙasa tana kurma ihun kiran Zaiyan amma shuru, Ta Sakkwato ta koma bayan mijinta ta ruɗe sosai har ba ta san lokacin da ta saki fitsari ba ta soma surutai, "Waiyo Allah ka kawo mana dauki, kun ce ku na biɗar kuɗi mun ba ku yanzu kuma ku ce kowatta sai kun mata hwaɗe, wagga zalunci har ina?"

Sai da Bangis ya kai Abir inda Ogan nasu ya umurce shi ya kai ta na daure ta sannan ya dawo, kuka da kururuwar kiran mijinta kawai take saboda an daure mata hannu a jikin bishiyar, wajan ta ya isa yana fadin "Yarinya idan za ki tsaya na yi abin da nake so ki tsaya, idan kuma gardama za ki min zan bi ki ta karfi da yaji sannan na kashe mijin naki har ke karan kanki zan alburushe ki."

Shuru ta yi tana girgiza masa kai ya kwashe da dariya yana kai hannu ya dafa kafaɗarta da nufin ya mata kiss, ƙara ƙwalla wanda har dajin kansa ya amsa kowar muryarta ta kira sunan Zaiyan da ƙarfi a lokacin da ya zabga mata mari, a kuma daidai lokacin ne Zaiyan ya daina wannan gurnanin da yake ya buɗe idanuwansa ya tashi tsaye da sauri yana murza idanuwansa, kiran sunan shi da ta ƙara yi ne ya sa shi saurin janye hannayen daga fuskarsa ya ɗago kai ya kalli yan fashin. A zabure Bangis ya yi baya ya ɗaga murya ya ce "Oga! Oga! Damisa! Damisa!"

Haka ya dinga maimaitawa yana nufar inda Ogan nasu yake. Ya kai hannu zai yaga rigar da ke jikinta cak ya tsaya jin abin da Bangis ya faÉ—a, afujajan ya iso yana haki ya nuna masa da hannu ya ce "Oga Wallahi Damisa na gani."

Tashi ya yi tsaye yana hura hanci ya ce "Kai fa mahaukaci ne a ina kasan fuskar Damisa da har ka gane yana cikin wadannan mutanen?" Ya faɗa kamar zai kai masa duka saboda ya ci alwashin yin abin da yake so da Abir. Ganin sun shiga yin gardama a tsakanin su Abir ta saɓule ɗaurin da aka mata ta kwasa a guje ai kuwa suka mara mata baya, tana isa ta faɗa jikin Zaiyan da ya yi tsaye kamar gunki yana kallon su fuskar nan tashi a haɗe. Turus Bangis ya yi jikinsa ya dauki rawa ya ce. "Oga billazil Azim wannan Damisa ne, ba na taɓa ce ma na taɓa ganin fuskar Damisa ba shekarun baya? Kuma wannan dai shi ne Damisa." Ya faɗa yana yin baya.

Wani irin kallo yake bin su da shi ya sa hannu ya É—ago da Abir ya ce "Anty waye ya sa ki kuka?" Ya faÉ—a yana goge mata hawayen. Da hannu ta nuna masa su Bangis ta ce "Su ne za su keta min haddi."

Shuru ya yi ita kuma ta ci gaba da kuka, Ta Sakkwato da mijinta da sauran mutane duk bayan Zaiyan suka dawo kowa sai rawar jiki ya yi, kallon su ya yi cikin wata kalar murya wadda Abir ba ta taɓa jinsa da ita ma ya ce "Wa ye a cikin ku ya taɓa ta." Ya faɗa yana raba Abir da jikinsa ya nufo su.

Durƙusawa suka yi Bangis ya ce "Shi kenan yau kwanan mu ya kare, tabbas wannan muryar Damisa ce."

Dukan su ya dinga yi suna ba shi haƙuri suka ce za su mayar wa da kowa kuɗinsa da suka amsa, sai da Abir ta isa ta kama shi tukun ya daina dukan su ya juyo ya kama hannunta yana huci bai ce mata komai ba, ita dai da mugun mamaki take kallon shi gani take kamar ba Zaiyan ɗin ta da ta sani ba da in an taɓa ta yake birkicewa fiye da haka.
Chapter 80 · 0% Book details