Sashe 40
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai fi minti uku da tura saƙon ba wata number ta turo masa saƙo.
_"Oga yau dai na gano maka komai game da wannan kes din namu, ga bayanan nan na turo ma."_
Cikin zallar farin ciki ya jumƙe hananyensa duka biyun ya ce "Yess."
Rufe computer ya yi
Taku har kullum Mom Nusy.
[6/20, 7:50 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~
+966577675904
Shafi na (21)
Rufe computer ya yi yana jin zallar farin ciki, can kuma sai ya ɗaga kai sama ya lula duniyar duniya. Riging wayarsa ne ya dawo da shi daga tunani, janye hannun da ya yi tagumi ya yi ya janyo wayar dan ya ga waye da daren nan yake kiran shi, ganin mai kiran ya sa ya shi jan tsaki ya aje wayar yana jin ɓacin rai na ziyatar shi. Sake kira aka yi wannan karon ya ƙara fusata ya yanyo wayar ya amsa kiran bai ce komai ba.
Sai da ta sauke ajiyar zuciya yana jin ta daga cikin wayar, jin ta yi shuru ya ƙara fusata ya tashi daga inda yake zaune ya koma kan kujera ya zauna, sai da ya shaƙi ƙamshi son ran shi, so yake ya nuna mata in ta wannan ɓangaren ne ya dame ta ya shanye. Sai da ta ji dai ba zai ce komai ta yi gyaran murya yana jiyo wata murya ƙasa-ƙasa wadda ba tata ba, tsaki ya ja yana hura hanci shi fa in ba dan ba yana bin umarnin Maimartaba ta tuni ya kakkarya yarinyar nan da ba ta aiki sai yawon gidan ƙawaye, kuma wai a haka ake cewa a aura masa ita mace ba kamun kai ba tarbiya. Har ya yi niyar kashe wayar amma ya fasa kashewa jin muryar namiji yana magana.
_"Haba Fauza me ya sa kika maƙale wa wannan yaron da ba ƙaunar ki yake ba? Mene ne ni bana miki a rayuwa? Duk abin da kike so ina miki ina biya miki buƙatarki da nema ina saya miki duk kayan shaye-shayen da kike so me kike nema a wajan shi? Ko ni na miki kaɗan ne bayan kin san ni din jarumi ne?"_
Riƙe baki Suhal ya yi yana nanata kalmar biyan buƙata da jarumta, kenan dai duk abin da ake faɗa akan wannan yarinyar gaskiya ne? Tsaki ya ja ya kashe wayar ya soma safa da marwa, lalle ya zama dole ma ya samu hanyar za a daina maganar auren shi da ita, in ba haka ba yana zaune lafiya za a kwaso cuta a yaɓa masa, a rayuwar Suhal ya tsani ya ga mace ba ta kamun kai ko kuma mai hulɗa da maza, sai ga shi wai shi ake son laƙabawa mai halayen da ya fi ƙyama a duniya. Numfashi ya fesar ranshi n ƙara ɓaci ya koma ya zauna gabaɗaya jikinshi ya yi sharkat da zufa, tuna abar ƙaunar shi da ya yi sai ya ji ɓacin ran na sauka ya ɗago wayar ya lalibo number ya danna mata kira. Sai da ta gama ringing ba ta ɗauka ba bai haƙura ba ya sake kira, wannan karon sai da kusa tsinkewa kafin ta ji an ɗaga kiran.
Cikin magagin bacci ta ce "Hello Ya Suhal.." Ta faɗa tana ɗauke hannunta a kan wayar ta bar ta akan kunnen. Sai da ya ja dogon numfashi jin yadda muryarta ta ƙara masa daɗin sauraro, ji ya yi kamar kar ta fasa magana ta ci gaba da yi yana sauraro har sai bacci ya ɗauke shi, wani ƙayataccan murmushi ya saki sannan ya soma magana cikin nutsuwa da kamewa.
"My Princess am so sorry na tashe ki a bacci ko?" Ya yi maganar yana matse pilon da ke gaban shi ya lumshe idanu.
Itama ƙara shigewa ta yi cikin bargon ta tana jin bacci na fusgar ta, da ƙyar ta iya tattaro kalaman da za ta faɗa masa, ta ce "Yaya Suhal bacci."
Ƴar dariya ya yi yana gyara kwanciya, sai da ya soma jin saukar numfashin ta ya gane da gaske fa baccin take ji ba wasa take masa ba, hakan ya sa ya kira sunanta ya ji ta amsa sama-sama ya ce "Princess don Allah za ki aure ni?"
Shuru ya ji babu amsa ya yi murmushi ya kashe wayar ya yi addu'o'i sannan ya kwanta...
A ɓangaren Abir kuwa tana jin shi da niya ta kyale ya kasa ce masa komai, wani irin bawai take jin in ta tuna maganar neman auren ta da ya yi, ba ta jima ba bacci ya kwashe..
Washegari ta shirya ta tafi makaranta, kasancewar yau tana da jarabawa dan haka duk take sauri ko abinci ba ta ci ba ta fito harabar gidan. Kiciɓus suka yi da Abdul yana son shiga part ɗin su, ɗan ja da baya ta yi ta zuba masa idanu, dam ta ji gaban ta ya faɗi ganin yadda idanuwansa suka yi jajur sai lumshe su yake yana buɗewa, a nutse ta matso kusa da shi ta ce "Good morning Yaya."
Shuru ya yi bai ce mata komai ya lumshe idanu, so take ta wuce amma tana tsoron masifar shi ya ce ta raina shi, a sanyaye ta kuma cewa "Yaya ba ka da lafiya ne wai?" Ta Yi maganar murya na rawa dan ta ƙagara ta wuce school..
Sai a lokacin ta iya buɗe idanu ya zuba masa su yana jan numfashi, gabaɗaya ji yake wani irin zazzaɓi na son rufe shi har ya fara jin sanyi, fesar da zazzafar iska ya yi daga cikin shi sannan ya ce da ita, "Muje na sauke ki." Ya faɗa yana yin gaba sosai yake jin gaɓaɓɓan jikinsa na yin sanyi. Ganin ya yi gaba ta turo baki tana wani langaɓar da kai gefe kamar yana gaban ta sannan ta bi bayan shi zuwa mota, tana turo baki ta shiga gaba bsi jiira komai ba ya danna hon Maigadi ya zo da sauri ya buɗe masa suka bar gidan..
Sai da suka yi nisa da gida sannan ta ga ya gangara bakin hanya ya tsaya, da sauri ta ɗago da idanunta karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna, wani irin bugawa zuciyarta ke yi hango wani irin abu cikin kwayar idanuwansa. Ita ta fara janye nata idanun ta sunkuyar da kai sai ga hawaye sun soma zarya, yau gabaɗaya ta kasa gane kan Yayan nata mai faranta mata rai kullum da koyaushe, hannu ta sa ta goge ta sake ɗagowa ta dube shi, wannan karon yana kallon gefe sai ajiyar zuciya yake saukewa ita kanta ta tsorata ta gani yadda y sauke numfashi kamar mai irin cutar ta ta asma in ta tashi. A hankali ta ɗaura hannunta kan nashi ta soma shafawa kamar wanda wani abu ya cije shi, dogon numfashi ya sauke ya lumshe idanu, wani irin yanayi yake ji mai wuya fassarawa a baki. Murya na rawa ta kuma cewa "Yaya are you OK?".
Wani irin rawa ya ji jikinshi ya É—auka bai san lokacin da ya janyo ta ya rungume ta ba, sosai ya shigar da ita jikinsa yana sauke numfashi da sauri-sauri..
Waro idanu ta yi jin yadda yake matse ta kamar ya samu É—iyar roba, mutsu-mutsu ta soma yi jin yana shafa mata baya tsoro ya shige ta ta ce "Y...Ya..Yaya.." Ta ja sunan cikin wani kalar firgici..
Ƙara matse ta ya yi ya ɗaura kan shi a kan kafaɗarta ya lumshe idanunsa, hawaye ne suka cika masa idanu suna shirin zubewa ya soma ƙoƙarin mayar da su amma ina tuni har sun ɗigo a gadon bayan ta. Da ƙyar ya saita nutsuwar shi jin yadda take kuka tana kiran sunan shi, a hankali ya ɗago kanshi ya sa hannu ya tallabo fuskarta ya ƙura mata idanu, wani irin zaro idanu Abir ta yi ganin sawun ruwan hawaye a kan kumtunsa ta kai hannu ta taɓo dan tabbatarwa, da gaske dai hawaye ne a fuskar Yayan nata cikin tashin hankali ta soma tambayar shi.
"Yaya wai me ke faruwa ne? Hawaye fa na gani da kan kuncinka Yaya, shin wani abin ya faru marar kyau?" Ta jeru masa tambayoyi tana kafe shi da idanu, gabaÉ—aya ji ta yi zuwa makarantar ma ya fitar mata a rai sakamakon ganin hawayen Yayan nata mafi soyuwa a rayuwarta..
Wani yawu mai ɗaci ya haɗiya sannan ya ce "Ba komai Baby, kawai dai kaina ne min wani azababben ciwo, kuma kin san dai in ina ciwon kai haka idanuna ke fitar da ruwa." Dogon Numfashi ta ja ta yi fuskar tausayi ya ce "Amma dai har da zazzaɓi ko?" Ta yi maganar a sanyaye.
Gyaɗa mata kai ya yi bai kuma bari ta masa wata tambayar ba ya daure ya kunna motar suka ci gaba tafiya. Suna ƙarasawa School ta fito ta rataya handbag ɗinta ta sunkuyo suka haɗa idanu ta ce "Yaya please ka je Asibiti a duba min lafiyar ka kafin ka isa office." Gyaɗa mata kai kawai ya yi ya zuge glas ɗin ya wuce..
Ji ya yi kamar kar ya je aiki yau, amma ba yadda ya iya saboda yana da aiyuka masu tarin yawa a office dole ya je ya samu ya É—an rarrage ko ba yawa ne.
Zaune suke a babban wani palo su uku palo ya kacame da hayaniya.
Alhaji Mustapha ya miƙe tsaye ya ce "To billahillazi ba zai yiyuba, taya a matsayin ka na babba da mu a wannan harkar ace kai ne za ka fara taka dokokin wannan lamarin? To b zai yiyuba ka yi abin da Nadumbuza ya ce in har kana son zaman lafiya. Ka samo inda aka ɓoye yaron nan tun da jinin ɗanka ba shi da ƙarfi kamar wancan mahaukacin, in kuma ba haka ba duk za ka jaza mana masifa." Ya ƙarashe maganar cikin tsananin fushi kamar zai kai wa Alhaji duka..