Sashe 27
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Suhal barka da zuwa, ya hanya?" Cewar Maimartaba yana jin son ɗan nasa na ratsa ma'adanar sirrinsa. Matsowa ya yi gaban Maimartaba ya ce " Alhamdu Lillah Papa, ya gidan?" Ya faɗa yana ƙara sunkuyar da kanshi ƙasa kamar zai kwanta a kan cinyar Maimartaba. Hannu ya kai a kan Yarima Suhal shi kuma ya yi saurin ɗauke hular sumarsa ɓaka ta bayyana a kwance luf, shafa kan nasa ya yi ya ce "Allah ya yi maka albarka Suhal, yanzu tun da ka gama karatunka ka samu aiki ai sai ka nemo mata ayi maka aure."
Rausayar da kai ya yi cikin nuna so ga mahaifin nasa ya ce "Haba Papa shi kenan dan na samu aiki sai ka ce na nemo mata, 'yan matan nan fa yanzu sai ka duba kafin ka samu mai nutsuwa da hankali." Ya faÉ—a yana wani yamutsa fuska.
Murmushi Maimartaba ya yi ya ce "To shi kenan ai ina dai kallon hanya, idan har ka bari haƙurina ya ƙare zan aura ma duk wadda na ga dama, jiya ma mun yi magana da Sarki Agadez akan ƴar wajansa na ce masa ya bari tukun ka dawo sai na gani ko kai ko Sultan wani sai ya je ya ganta."
Kilishi da ta cika da haushin Suhal ko gaishe da su bai yi ba ta muskuta tana yin murmushin yaƙe, cikin kissa ta ce "Suhal ya hanya? An dawo lafiya? Gaskiya har yanzu ba ka canja hali ba yaron nan, ka zo ka same mu ko ka gaishe mu a matsayin mu na iyayenka, anya Suhal?" Ta faɗa tana ƙurawa Maimartaba na mujiya dan ta ji me zai ce..
Sosa kai ya yi yana jinjina lamarin Kilishi, can ciki-ciki ya ce "Ku yi haƙuri na sha'afa ne saboda murnar ganin Papa." Ya faɗa yana sunkuyar da kai.
Gyaɗa kai ta yi kamar ƙadangaruwa ta yi wa Sarauniya Bilkisu kallon ya kika ga salon sannan ta dawo da kallon ta kan Maimartaba ta ce "Ranka ya daɗe ai ina ga tun da Sultan ne babba shi ya kamata ace ya auri ƴar Sarkin Agadez, ba wannan solobuyon ba da ko maganar auren aka masa sai yake wani ciccin magani kamar ya ga abin kyama. " Ta faɗa tana hararar shi haɗi da murmushi..
Wani irin sanyi ya ji dan dama shi kwata-kwata Æ´ar Sarkin Agadez ba ta kwanta masa a rai ba, ta cika wayewa da yawa hakan yasa ya yi hamdala da maganar Kilishi..
Maimartaba ya ce "Kuma fa Kilishi kin kawo shawara mai kyau, yanzu zan sa shi Sultan É—in ya je ya ganta duk da ya santa, amma wannan zuwan maganar aure ce ba ziyara ba."
Taɓe baki Sarauniya Bilkisu ta yi tana kaɗa kai ta saki murmushi cikin tausasa murya ta ce "Allah ya taimake ka ni ai nake gani mai zai hana a haɗa Suhal aure da Fauziya, tun da dama son shi take ta ɓoye dan ita mace ce mai kamun kai da kunya ba za ta taɓa tarbar shi ta sanar da shi ba." Ta faɗa tana wani irin malalacin murmushi tare da kallon Kilishi da ta saki baki tana jin bayanin Sarauniya Bilkisu..
Saurin kallon ta Suhal ya yi ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ni Papa bana son ka aura min Fauziya, yarinyar da ba ta jin maganar kowa za a aura min ita?"
Maimartaba ya ce "Ai kuwa Fauziya za ta dace da kai, ka ga duk inda za ka je sai ka tafi da matarka."
Ƙara ɗaure fuska ya yi yana jin zuciyarsa na masa zafi, in ban da ma Sarauniya Bilkisu da makirci taya ma za ta kawo maganar ya auri Fauziya yarinyar da kullum tana yawo gidan ƙawaye? Kwafa ya yi yana kuma tuna cewa da ace Mahaifiyarsa na magana ai ba za ta taɓa bari a aura masa wadda ba ya so ba, ya tashi tsaye ya ce "Papa zan je na ɗan huta kaina ciwo yake min."
Cikin tausayawa Maimartaba ya kalle shi ya ce "To shi kenan ka je zan sa Likita ya shiga a duba ka."
"A a Papa ba sai an duba ni ba, tafiyar nan ce tasa kaina ke ciwo."
Mamma itama ta miƙe ta yi wa Maimartaba nuni da ita ma za ta wuce sashenta ya ce ta tsaya, ba dan ta so ba ta bar Yarima Suhal ya fita da sauri yana ƙara jin haushin Sarauniya Bilkisu..
"Ku É—an bamu waje ina so za mu yi magana da Fulani."
Bakin ciki ne ya mamaye zuciyar Kilishi ta ce "Wato Maimartaba na lura a matan naka ma son kai kake yi, yanzu dan za ka yi magana da ita sai mun bar palon nan kamar ba ka yarda da mu ba? Indai maganar auren Suhal ce ai muma iyayensa ne mu yakamata ma ace mun zauna da kai an tsara komai, ko sayayyar kayan lefe za ayi mune dai ya kamata ka nema ba wadda ta haife shi ba. Amma tun da ka nuna mana mu ba iyayen shi ba ne ba komai."
"Ba ban yarda da ku ba ne, magana zan yi ni da ita kawai abin bai shafe auren Suhal ba." Ya faÉ—a yana komawar sarkin sa, amma duk da haka Kilishi ta ce ba inda za su je ayi komai a gaban su. Sai da suka gaji da yin shurun ganin fuskar Maimartaba ba wasa yasa suka tashi suka bar palon, sai bayan sun tafi ne Maimartaba ya juyo ga Mamma ya kamo hannayenta cikin kulawa ya soma mata magana..
"Ki yi haƙuri Fulanina, in sha Allah kema wata rana za ki kike magana kamar kowa karki saka wa kanki damuwa."
Hawayen da suka cika kwarmin idanuwanta ne suka samu damar zubowa ya sa hannu ya share mata, cikin tausasa lafazi ya shiga kwantar mata da hankali ita kuma ta nuna masa ba ta son Yarima Suhal ya auri Fauziya dan ta ga baya son ta. Bayan sun gama tattaunawa yasa aka kira Jakadiya ta zo ta É—auke ta suka koma sashenta...
*NIGERIA*
Cikin shigar ta riga da wando ta fito daga cikin kitchen hannunta ɗauke da glass cup, a nutse ta zauna a kusa da Mom sai kuma ta turo baki gaba ta saurayar kai cikin Shagwaɓar take kallon Mommy. Hararar ta Mommy ta yi ta ce "To me kuma aka yi da kika sakani a gaba kina min kallon ƙurulla?"
Turo baki ta yi ta yi raurau da idanu kamar za ta kuka ta ce "Mom ki ce wa Yaya ya faɗa min inda ya kai Zaiyan, so nake ya kaini na gan shi yaushe rabona da shi tun fa ranar da muka zo nan kusan kwana goma kenan." Ta faɗa idanuwanta na cika da hawaye wanda kaɗan ya rage su silalo, wani irin yanayi take ji wanda baki ba zai iya musalta shi ba, sosai kewar shi da son ganin shi suka hana gangar jiki da ruhinta sukoni. In ta yi wa Abdul magana sai ya ce mata ba yanzu ba, hakan ya sa ta daina kula shi ko gaishe da shi ba ta yi in ya zo sai ta ƙi fitowa ta yi zaman ta a ɗaki ta kulle dan kar ma ya shigo mata ba ta sani ba. Mommy da take jan casbaha tana lazumi ta dakata da ja ta dube ta ce "To yanzu ni me kike so na ce masa?"
Ai kuwa kamar jira take ta ɓare baki ta shiga rera wa Mom kuka har da shure-shure kamar yarinya ƙarama, ko kallon ta Mommy ba ta yi ba ta dinga rusar kuka har sai Mommy ta ga abin ba mai ƙarewa ba ne ta juyo suka fuskanci juna.
"Kukan ya isa haka yi shuru, ba dai so kike ki duba shi ba?"
Saurin gyaÉ—a kai ta yi tana goge hawaye, Mommy ta yi murmushi ta ce "Zan amsa magana sai ya sa a kaiki ki gano shi." Dariya mai haÉ—e da hawaye ta yi ta rungume Mommy ta ce "Thank you my sweetheart. " Ta faÉ—a tana sumbatar ta a kumatu sannan ta tashi ta É—auko wa Mommy wayarta ta tsare gida ta ce sai Mommy ta kira shi yanzu ta faÉ—a masa, girgiza kai Mom ta yi ta amshi wayar ta lalibo number Abdul tana shiga ya É—aga, bayan sun gaisa ta sanar masa ya zo ya Ä·ai Abir inda Zaiyan yake ta addabe ta da kuka..
Yana zaune a cikin office ɗinsa ya yi kwafa, wato ma har kai ƙaran shi take dan ya ƙi kaita wajan shi? Zai dawo gidan ai tun da ita in ta kafe akan abu ba ta saduda kamar ɗiyar maguzawa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Wallahi Baby ta fiya neman rigima, ni fa na ce da zarar na shirya zan kai ta gan shi."
Mommy ta ce "To ni dai kazo ka rabani fa fitinarta bana son wannan kukan nata ƙi ƙarewa har taja wa kanta ciwon kai."
To ya ce zai sa a kaita sannan ya katse wayar yana sakin murmushi, Mommy ta ce "Sai ki shirya ai ga shi zai sa a kaiki."
Da sauri ta tashi har tana tuntube ta shige ɗakinta, zama ta yi tana murmushi ta buɗe wata leda dake gefen gadonta, kayan sawa ne kala-kala sun kai kala goma har da takalmi ta haɗe su duka a leda ɗaya, buɗe drower ta yi ɗauko chocolate mai yawa ta zuba a ledar. Har ta miƙe sai ta ga wani abu ɗan ƙarami ɓaki mai kama da memory, da mamaki take kallon abin ta sa hannu ta ɗauka tana jijjuyawa. Cike da al'ajabi ta ce "To shi kuma wannan ɗin meye?" Ta faɗa tana ƙara juya abin. Ganin tana ɓata lokaci sai ta bude inda take aje kayan zakinta ta aje abin ta sanya hijabi har ƙasa ta fito.
Ko zama ba ta yi ba É—aya daga cikin masu tsaron gidan ya ce ta fito su tafi, sai ta dawo ta cewa Mom ita kuma ta ce Allah ya tsare ta amsa da amin..