← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 120

Sashe 83

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kama ta suka yi suka shigar da ita ɗakin zuwa lokacin da kyar take jan numfashi tari kawai take, handbag ɗinta take nuna musu da hannu hakan ya sa Maman Amal ta janyo jakar ta zarge ta zazzage ta, maganin shaƙa na cutar asma ta gani hakan ya sa ta gane shi take so a ba ta, da sauri ta kai bakinta ta ta fesa ta shaƙa ta ƙara mata sai ta saki jiki. Baya suka yi da ita suka zaunar da ita akan gatifar tare da jingina ta da bango suna jera mata sannu sai ajiyar zuciya take saukewa ɗaya bayan ɗaya tana lumshe idanu, da sauri Zaiyan ya shigo ɗakin ganin ta a zaune sun saka ta gaba sai ya iso kan katifar ya zauna yana kallon ta tare da zaro fararen idanuwansa, wuyanta ya taɓa sai kawai suka ga ya soma kuka yana tattaɓa ta yana fadin "Anty me suka ba ki?"

Maman Amal ta miƙe da sauri baki buɗe tana kallon Zaiyan sai ya ga Ladidi ya leƙo daga bakin ƙofa, ganin Zaiyan na kuka sai ya sheƙe da dariya ya ce "Oh ni Ladidi! Wasu dai sun rako maza duniya, kai yanzu saboda lalacewa kuka ne kake?". Ya faɗa yana nuna Zaiyan. Kallon shi ya yi ya tsayar da kuka ya ce "Ba su ba ne suka mata wani abu."

"Ahaiye caɓas, billahillazi ka ba da maza ɗan matashi, yo kai wani kalar soloɓuyon namiji ne Allah ya yi? Hmm ikon Allah to ba da ni ba rakiyar fatalwa na yi nan." Ya faɗa yana sake yin dariya ya wuce.

Turo baki ya yi ya taɓa fuskarta ta buɗe idanu ta kalle shi, nisawa ta yi ta kalli su Maman Amal ta ce "Na gode muku Allah ya saka da alkhairi, kai kuma daina kukan ka fita ka ci abinci kafin na yi wanka." Ta faɗa tana janye hannunsa daga kan kuncinta..

Maman Amal dai ta yi tsaye kamar gunki riƙe da baki, sai da ta ji godiyar da take musu sannan ta sauke hannun ta gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa ta ce "Shin ni kuwa Jiddo wannan ƙanenki ne?"

Murmushi ta yi ta ce. "No, he is my husband."

Shuru Maman Amal ta yi kawai abin da ta gane a kalaman Abir Husband tasan dai miji ake nufi, kallon Zaiyan ta yi ta ce "Wato dai in na fahimta mijinki ne?"

Gyaɗa mata kai ta yi hakan ya sa ta ƙara cika da mamaki, tashi suka yi suka bar mata ɗakin suna mata Allah ya kiyaye amma suna ta jinjina maganar wai Zaiyan mijinta ne.

Ganin sun fita ta kwashe kayan handbag É—in ta tashi ta zuba wa tukunyar ruwa ta dauke abincin har na Zaiyan ta kawo masa É—aki ta ce ya zauna ya ci, bai musa ba ya zauna ya ci gaba da ci ita kuma ta kwanta jin wani zazzabi na shirin rufe ta babu jimawa bacci ya kwashe ta..

Tun da Grandma ta dawo ba ta ga Abir ba sai ta yi tunanin ko a gidan Abdul take, sai da Abba ya shigo tana palo Laraba na matsa mata ƙafa ta ka dubi Abba ta ce. "Wai ni kuwa Sulaimanu ina wannan shashashar yarinyar take? Na ga tun da muka dawo ban gan ta ba ko ta koma gidan Abdullahi da zama ne?"

Wani ɓacin rai ne ya ziyarce zuciyar Abba jin kalaman Grandma dan shi ya ma manta da babin Abir, da kyar dai ya ce "Ai ta yi auri wannan mahaukacin da take kula da shi."

Maimakon Grandma ta yi mamaki ko ta shiga ruɗu sai kawai ta ja tsaki ta ce "To ai shi kenan." Ba ta sake cewa komai ba daga haka suka daure hira, hankalin Laraba ya yi mugun tashi ganin yadda duk suka yi kamar ba su damu da Abir ba, da sauri ta miƙe ta kalli Grandma ta ce "Inna zan je na kira Mamata mu gaisa tun da muka dawo ban kira ta ba."

To Grandma ta ce ita kuma ta wuce da sauri ta nufi ɗakinta har tana tuntuɓe, tana isa ɗaki ta soma zarya tana huci sai haɗa zufa take, tsayawa ta yi ta harɗe hannaye ta lula duniyar tunani. Ta fi minti biyar a haka tukun ta saki murmushi ta soma magana.

"Tabbas lokaci ya yi da za ku san wace ce Laraba, lokaci ya yi da zan kawo karshen duk mai sa hannu akan wannan mutanen, lokacin yaƙi ya yi kuma ba makawa sai an yi." Ta ƙarashe maganar tana janyo gana mostgo ɗin kayanta ta soma binciko kayan tana watsi da su. Computer ta zaro daga can ƙasan gana mostgo ɗin ta kulle kofar ɗakin ta dawo ta zauna, kunnawa ta yi ta sa code ta buɗe ta shiga wani waje ta dauko wata number, sake sa hannu ta yi ta fito da waya iPhone 12 ruwan fauda ta kunna ta buɗe ta sa wannan number ta danna kira. Sai da ta yi ringing ta gama ba a dauka ba sai ta aje ta dawo kan computer ta soma yin rubutu cikin sauri, tana tsaka da yin rubutun sai ga number an kira ta ta yi saurin dauka ta kara a kunne.

"Hello Sir Jk ce ke magana, lokacin zuwan ka Nigeria ya yi dan sun aikata maka babban zunubi..."

_Maman Nusaiba ce_

[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na (41)

Shuru ta yi tana sauraron shi sai gyaÉ—a kai, zuwa can ta tashi tsaye tana goya hannayenta baya ta soma magana.

"Haka ne Oga ina ganin yau ɗin nan aikina akan wannan ahali ya kammala, amma ni abin da nake son samu kafin na bar ƙasar, ina son na gano wani hali ƙanwata take ciki a hannun wadannan azzaluman? A ƙara min ko da weekend biyu ne na binciko inda take zama."

Daga cikin wayar Damisa ya ja numfashi sannan ya ce "Jk ka da ki karaya komai ya kusa zuwa karshe, ni nasan inda kawarki take a halin yanzu, sai dai rayuwar da take a wannan waje ta ƙazartar dan haka nake ta shiye-shiryen dawowa na kawo karshen wasan. Tabbas sun aikata babban zunubi mafi muni a rayuwarsu kuma zan tabbatar musu da hakan da yardar Allah, amma su na gidan kike lura da duk wani shige da ficen su ki gano mana me suke shirin ƙullawa akan ta. "

Jikin Laraba ne ya ɗauki rawa ta dafe ƙirji ta yi ƙasa da murya ta ce "Oga da gaske kake ƙanwata tana raye har ka gano inda take?" Ta faɗa hawaye na zubo mata.

"Hmm Jk ki nutsu ka da jin na ce nasan inda take ki kasa haƙuri mu gama aikin nan, da zarar na sauka zan amso ta."

Jinjina kai ta yi kamar yana kallon ta, sai da shuru ya ratsa su na 'yan sakanni tukun ta nisa ta ce. "Babu damuwa Oga ba zan karaya ba, zuwa an jima zan tura maka da bayanai na jiya kuma yanzu zan turo su."

OK ya ce mata sannan suka yi sallama ta aje wayar, dawowa ta yi kan computer ta ƙarasa rubutun da ta soma ta tura masa sannan ta kashe, kwashe su ta yi ta mayar da su muhallin su ta janyo ƙaramar wayarta ta gyara zama.

Numbers Abir ta dannawa kira amma ta ji ta a kashe hakan ya sa ta dafe kai ta aje wayar, toilet ta shige ta wanke fuska ta fito da hanzari ta fita zuwa kitshen É—aura girki..

Yau sammako Umma ta yi ta isa zuwa gidan malamin nata fuskarta ɗauke da farin ciki, tarba ta samu daga malam ta musamman har da abinci ya kawo mata ta ce ta ƙoshi, gyara zama ta yi ta soma mi shi bayanin komai.

"Gaskiya Malam aiki ya yi kyau sosai, yanzu haka maganar da nake maka kaf family Maitama kowa ya tsane ta kuma ya manta da babin rayuwarta a cikin family, ƙarshe ma dai ko gidan ba ta zuwa tun da aka ɗaura auren. Yanzu kuma abin da nake so ina son a cikin samarin gidan Sarautar Niamey a samu ɗaya a cusa masa son Khairat ya aure ta. " Ta faɗa ɗukar da kai kamar za ta masa sujjada.

Murmushi ya yi ya soma rubutu a cikin ƙasa bai ce mata komai ba, sai da ya gama ya ɗago yana murmushi ya ce "Hajiya to ai ita yarinyar da mijin nata sun bar garin kusan sati ɗaya kenan, kuma ba wani abu ba ne ya sa ta barin ganin sai dan tsira da ranta da na mijinta."

Kwalalo idanu waje Umma ta yi tana dafe ƙirji ta ce "Ni fa yanzu Malam ba na so a kashe ta, ina so a bar ta a haka ta wulaƙanta a duniya, amma waye ya mata barazanar mutuwa?" Ta faɗa tana kallon Malam.

Gyara zama Malam ya yi ya saki murmushi ganin yadda Umma ta ruÉ—e ya ce "Ya na ga hankalinki ya tashi da jin labarin nan? Ke da kike cewa a kashe ta ya da haka?"

Sauke hannu daga ƙirji ta yi ta ce "A'a Malam, ni fa ba tausayin mayyar yarinyar nan naji ba, kawai dai bana so wani ya min katsalandan ya ɓata min aikin da nake a kanta tun kafin ta zo duniya, na tsane ta fiye da kima wanda ya mata hakan nake son jin shi ko waye shi."

Jinjina kai Malam ya yi ya ce "Yayanta ne shi ya mata barazanar zai kashe ta ta bi dare ta gudu, yanzu haka tana garin Kano amma ban gano takamaiman inda take zaune ba."

Dariya ta yi ta kaɗa kai tana kallon Malam ta ce "Ina son inda ta je ɗin ma su tsane ta kowa a garin ya hana ta muhalli, ba tana tunƙaho da dukiyar mahaifinta ba? To yanzu tun da ta bar komai na uban nata so nake ta yi rayuwa mai mugun matsatsi wadda babu talakan da ya taɓa yin irin wannan rayuwar a fadin duniya. " Ta faɗa tana huci.

"Na riga da na faɗa miki Hajiya yarinyar nan fa ba ke kaɗai ba ce kike bibiyar rayuwarta akwai maƙiyan babanta."
Chapter 83 · 0% Book details