← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 120

Sashe 119

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kus-kus kowa yake da na kusa da shi suna tsine wa Umma, wasu kuma suna ƙara jinjina son zuciya irin na su Umma, Inna da su Abir suna ta kuka Inna sai faɗi take "Amma ku dai Allah ya tsine muku dau dubu, yanzu Baraka ke da Sadisu aka haɗa baki baki da ku aka kashe min yaro saboda wani kuɗi dauɗar duniya kuka kashe ɗan'uwanku da matarsa? Rashin imanin naku ya kai har kuke ɗauke ɗiyan al'umma kuna kaisu ayi zina da su a ba ku kuɗi? Kaicon ku da wannan bakar zuciya irin taku.."

Rarrashin ta Mamma ke yi ita kan ta idanuwanta sun yi jajur saboda kuka, ta ƙara tabbatar da lalle mutanen nan ba su da imani gabaɗaya a rayuwarsu. Sai da aka lafa sannan Barrister ya matso kusa da Alhaji Mustapha ya ce "Kun ji abin da abokiyar aikinku ta faɗa? Gaskiya ne ko akwai in da ta faɗa ba daidai ba?"

Alhaji Mustapha ya wani ɗaure fuska ya ce "Duk abin da ta faɗa ƙarya take abu biyu ne zan ce gaskiya, shi ne amsar kuɗi da muke a hannun matasan da ya taimakawa sai wanda muka je ya gida muka amsa bayan mutuwar sa."

Jarmai da yake zubar da hawaye ya yi saurin cewa "Wallahi babu ƙarya a maganarta duk abin da ta faɗa mun aikata shi."

Wani irin kallo Alhaji Mustapha ya masa shi kuma ya sunkuyar da kai, Barrister ya ce "Idan har ita ƙarya take shi ma Jarmai ɗin ƙarya yake?"

Ganin fa ba sarki sai Allah ya sa suka amsa lefin su, Jarmai ya kalli Barrister ya ce "Kuma Alhaji Mustapha ne ya sa 'yan daba suka je gidan Alhaji Abdu suka banka musu wuta bayan sun É—auke duk wata kadara tashi, sai ga shi ba su mutu ba da ran su." Ya faÉ—a yana nuna Mai martaba.. Kallon in da yake nunawa Barrister ya yi suka haÉ—a ido da Mai martaba, dawo da kallon shi kan Jarmai ya yi ya ce "To saboda me ya masa wannan aika-aikar?"

"Saboda ya ga kasuwancinsa ya soma fin nasa bunƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci Alhaji Abdu ya buɗe katafaren shago a kantin kwari, wannan abin ne ya ƙona masa rai hassada ta mamaye masa zuciya, shi ne cikin dare ya sa aka sa musu wuta babu abin da ya haɗa su kawai dan ya fi shi samu ne. "

Barrister ya kalle shi irin kallon sannu mugu, nisawa ya yi ya ce "To dama shi Alhaji Mustapha a Kano yake? Ko kuwa yana daga nan Yola ne ya sa aka yo abin?"

Goge hawaye Jarmai ya yi ya ce "Da ya zauna a Kano, dawowar abokinsa Alhaji Ibrahim Yola ne ya sa ya shi ma ya baro Kano amma asalin shi É—an Fulanin Yola ne."

Kotu ta buƙaci Mai martaba ya zo ana neman shi, dogarai suka zagaye shi ya tashi ya zo ya tsaya Alƙali ya dube shi ya ce "Abin da ya faɗa gaskiya ne.?".

Jinjina kai ya yi tare da cewa "Da farko kirana ya yi yana barazana ya ce sai na saki matata ya aure ta in har ina son zaman lafiya, ni kuma na ce sam ba zan yi hakan ba shi ne sai yaji haushi ya kashe wayar, da dare suka sa mana wuta Allah ya sa na fitar da matata ita da aikin gidan Maigadi kuma suka kashe shi, amma sai da suka bi bayansu suka dawo da Matata. Nan ya ba su labarin yadda suka Kuɓuta suka yi jinya sannan suka koma ƙasarsu ya amshi mulkin gadon gidansu. Ya nisa tare da sakin murmushi ya ce "Shi Damisan da suke son kashewa ɗana ne ni na haife shi, shi ne jaririn da ana haihuwar shi suka ɗauko mahaifiyar suka dawo da ita suka sa mana wuta, ba su san cewa duk Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana buzuru ana shaho sai ya yi."

Jinjina kai Alƙali ya yi ya ce ya je ya zauna sannan ya koma mazauninsa, Alƙali ya yi Rubuce-rubuce ya sannan ya ce "Alhaji Mustapha da Alhaji Sadisu da Jarmai shin ko za ku iya sanar da mu dalilin da ya duk kuka aikata wannan ta'asar?"

Alhaji Mustapha da jikinsu ya ɗauki ɓari sai yanzu shi da Daddyn Aruf suka san da cewar lalle fa ruwa ya ƙare wa ɗankada, Daddyn ya fashe da kuka ya ce "Wallahi babu abin da suka mana kawai ni baƙin ciki da hassada ce ganin Ibrahim ya zama mai kuɗin da duk Nigeria da ma Africa ta san da shi ta fannin kasuwanci, ni kuma ba wanda ya sanni duk abin da na taɓa sai na ga ba ya min albarka irin na Ibrahim."

Suma sauran haka suka faɗa, Alƙali ya yi rubuce-rubuce ya ɗago tare da cewa "Sakamakon samun ƙwararan hujjoji masu laifi sun amsa laifin su kotu ta yanke wa Baraka hukuncin kisa ta hanyar jifa, ta aikata zina da auren a kanta, hakazalika kotu ta yanke wa su Alhaji Sadisu hukuncin kisa ta hanyar rataya, nan da sati ɗaya za ta aiwatar da hukuncin za su dawo da dukiyar marigayi Alhaji Ibrahim Abdullahi Maitama. " Ya buga guduma ya miƙe duk kowa ya mike.

Masu kuka na yi ma su Allah wadai na yi har kowa ya fito waje. Suna kallo aka nufi cikin mota da su Alhaji Mustapha Inna na jero musu Allah ya isa tana goge hawaye da gefen zaninta, har za a saka su sai ga 'yan jarida sun yo ca a kan su sai tambayar su ake amma suka ƙi cewa komai aka tura su cikin mota suka bar filin. Suma su Inna gida suka tafi kowa jiki a sanyaye Iman da Khairat sun yi kuka kamar ran su zai fita, sosai suke kokawa da halin mahaifiyarsu...

Bayan sun je gida aka zauna ana ta maida yanda aka yi ranar ba wanda ya iya cin abincin dare, washe gari Hajiyar su Umma ta zo tana kuka ta dinga ba wa su Abba haƙuri tana neman gafarar su ta ce ba ta san duk abin da suke shukawa ba, Abba ya ce sun yafe mata ba komai sai ta nemi a ba ta Khairat da Iman su tafi gidanta in za su koma sai ta dawo da Iman ita kuma Khairat ta zauna a wajan ta. Ai kuwa Iman ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta zuwa ita tana gidansu cikin yan'uwanta, itama Khairat ta ce ba in da za ta je tana wajan Inna, dole ta haƙura ta tafi tana kukan nadamar abubuwan da ɗiyanta suka aikata.

Bayan kwana biyar da gama shari'a aka ɗauki 'yan sanda aka tafi tare da su Alhaji Mustapha zuwa gidan da suke aje yara mata ƙanana, sun isa aka dinga bi lungu-lungu ana fito da su har da masu ciki, aka ɗura su a mota sannan 'yan sanda suka banka wa gidan wuta ya ƙone ƙurmus, sai da suka tabbatar komai na gidan ya ƙone sannan suka zagaye wajen da wata irin waya sannan suka tafi..

Sai da aka gama zartar da hukunci sannan su Mamma suka soma shirin tafiya Niger, a lokacin Hafsat ta ji labarin za su tafi a wajan Abir hankalinta ya tashi ta tafo gidan ta samu Mamma tana kuka ta ce ta ƙara ba wa Abdul haƙuri ya dawo da ita ɗakinta, Mamma ta ji Hafsat ta ba ta tausayi ta kwantar mata da hankali tukun ta tafi. Ta Kira Abdul ta mi shi nasiha mai ratsa jiki tukun ya ce ya dawo da ita su je su kawo ta. Da yamma ta je ita da Ammi da su Abir suka dawo da ita, ranar Hafsat ta sha kukan farin ciki da Abdul ya ce mata zai zauna da ita har karshen rayuwarsa yana son ta. Washe gari suka haɗa komai nasu na tafiya sai a lokacin Khairat ta fashe musu da kuka tana sambatu dama ana canja uwa da ta canja Umma ta zaɓi Mamma, sosai ta ba su tausayi Mamma ta sa Suhal da Abdul da Zaiyan har Salim suka ɗauke ta suka kai ta gidan mahaifinta Malamin Umma.

Ita da Abir suka tafi gidan Baba Malam daga can su isa gidan su Baba su musu sallama.

A zaune suka same shi duk ya rame ya ƙanjame suka nuna masa Khairat suka ce ita ce ƴar da suka haifa shi da Umma, ya sha kuka yana ruƙon ta gafara ta ce ta yafe mishi suka rungume juna suna kuka gwanin ban tausayi, da kyar suka rabu ta amshi number wayarsa suka dawo gida. Kafin su tafi Abba ya kira Baba Malam aka raba gado kowa aka ba shi nasa, Abir na kuka ta ce Abba ya gina mata makarantar Islamiya da gidan marayu, companyn motoci da ta ci gadonsa ta ce Abdul da Salim su kula da komai ita ba ta buƙatar komai yanzu. Bayan Sallar La'asar suka shirya aka fito da kayan su harabar gidan Khairat ta rikice ta ce sai ta bi Mamma Niger, Daddy ya ce su tafi ko ta rage damuwar da take ciki, hakan ya yi wa Mamama daɗi dan ba ƙaramin tausayi Khairat ke ba ta ba. Duk yan gidan suka musu Rakiya har Airport suna tsaye har jirgin su ya tashi tukun suka dawo gida..

Rayuwa ta yi wa su Abir daɗi matuƙa in da Mamma ke kula da su sosai.
Chapter 119 · 0% Book details