← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 120

Sashe 14

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace ya juyo zai masa magana takaici ya hana shi cewa komai, wani irin zafi yake ji na mamaye masa zuciya har bakinsa na masa É—aci, har zai juya ya ji dai ba zai iya ba sai ya maganta.

"Wallahi kar ka bari mu haɗu Salim." Ya faɗa yana hura hanci tare da zuƙo iska da sauri jin yadda numfahi ke ƙoƙarin barin gangar jikinsa. Juyawa ya yi a fusace ya kama hannunta suka shige part ɗin Mommy...

Salim kuwa dariya ya yi yana shafa sajansa ya ce "Mu zuba mu gani, ni da kai shege ka fasa É—an halak sai yanka."

Da guntun faÉ—ansa ya shiga palon har ya zauna bai daina faÉ—a ba a zafafe, abin ya ba wa Mommy mamaki ta ce "Babana lafiya dai na ga ka shigo kana faÉ—a?"

Hura hancin ya yi yana ƙara buɗe ƙofar hancin, da ƙyar ya sassaita numfashinsa ya ce "Wallahi Mom kar ki bari Salim ya ce zai ɗauki Baby su tafi zuwa wani waje, kin san halin Salim na shaye-shaye zai iya kai ta club in da suke shaye-shayen sigari da shisha."

Riƙe baki Mommy ta yi tana jimamin ɗabi'un da Salim ya ɗauka wa kanshi, dan dama ta jima tana zargin ko shaye-shaye yake su ba su sani ba ganin yadda zai zo ya yi ta zuba surutai marar kan gado ashe dai da gaske shaye-shayen yake. Numfasawa ta yi ta ce "To a ina ma ka ga shi Salim ɗin?"

Tsaki ya kuma ja kamar jikan tsaka ya ce "Yanzu ya tare mu wai ta raka shi su je É—auko Uncle Aruf a airport, daga nan ta raka shi wajan budurwarsa dan ya É—auki mutane marassa hankali."

Saƙare Grandma da ta fito ta yi a tsaye, sai ji suka yi ta ce "Amma ko Allah wadaran naka ya lalace! Yanzu shi Arufullah ɗin ne zai zo ƙasar ko ya kira ya ce ga shi nan? Tabbas shi ma ya zama ɗan iska irin ƴar'uwarsa."

Abdul ya yi kwafa gabaÉ—aya ce sun saka masa ciwon kai ya ce "Grandma rabu da shi kawai ki ba wa iska ajiyarsa, Mommy gani Baby ta ce kina nema."

Gyara zama ta yi cikin nutsuwa ta ce "Babana Wallahi akwai matsala babba." Ta faɗa idanuwanta na cika da hawaye. Da sauri ya matso kusa da ita cikin tashin hankalin ganin hawayen Mommy da tun da yake bai taɓa ganin hawayen Mommy ba, ko da aka ce an sace Abie da Abir ba ta yi kuka ba illa shuru kawai da ta yi.

"Subhanallahi! Mom wacce irin matsala ce haka wadda ta sa kike zubar da hawayenki?"

Girgiza kai ta yi ta mayar da hawayen da suke shirin zubowa tana sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Ban san waye yake yi wa rayuwarmu barazana ba, tun kafin su Mamana su ɓata ake min wannan barazanar, lokacin da suka ɓata na ɗauka ni da su sai a kiyama ba zan sake ganin su ba."

Kallon ta Abdul ya yi cikin rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa ya ce "Mommy ki warware min komai don Allah ko zan samu damar aiwatar da bincike na yadda ya kamata, yanzu haka maganar da nake miki muna bibiyar layin Baby da wayarta ke wajan su, ko sun gane ana bibiyar su ne sai suka kashe wayar gabaÉ—aya ba mu iya bibiya yanzu."

Ajiyar zuciya Grandma ta sauke ta ce "Abdullahi ni fa dan kar ku ce rikicin tsufa ne yasa nake surutai, amma tabbas akwai wanda yasan sirikan ahalin Maitama ciki da waje a cikin su."

Jinjina kai Abdul ya yi alamar gamsuwa da maganarta, "Wato Grandma kin faɗi gaskiya, tabbas akwai abin da ba daidai ba a cikin wannan family, kullum kaina ƙara daurewa yake akan lamarin gidan nan. Wani lokacin sai ka ga wasu sun zama salihai gobe kuma ka ji suna abin da ba daidai ba, Mom ki faɗa min abubuwa da ake miki na barazana ƙila na samu wata hanyar da zan samo bakin zaren a cikin labarin da za ki bani."

Ƙaran text ne ya shigo wayar Mom ta yi saurin ɗauka ta duba ai kuwa taga sakon da aka saba turo mata ne, a tsorace ta ce "Ka gani ko sun sake turo min sako."

Amsar wayar ya yi ya shiga karanta saƙon.

_"Idan har kika yi kuskuren faÉ—a wa Abdul ko da kalma É—aya ce daga cikin lamarin nan za ki sha mamaki."_

Ƙanƙace idanu Abdul ya yi masifa na cin masa rai, cikin ruwan masifa ya shiga musu reply..

_"In kun fasa ba ta mamaki ubanku ya daki hancin babarsa, ku ƙananan 'yan iska ne in kun isa ku faɗi inda kuke mana na zo ayi ta ta ƙare, banzaye kawai asarar haihuwa."_

Yana huci ya tura musu, har zai ƙara wani rubutun kuma ya daina ya aje wayar yana huci gabaɗaya fuskarsa ta ji jajur saboda ɓacin rai abin ka da farar tafa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Mom ki ba wa iska ajiyar 'yan iska ni zan ji da komai in sha Allah, amma dai ki faɗa min ko da kaɗan ne daga cikin al'amurin."

"Abdul!"

Jin ta kira sunan shi yasa ya gyara zama dan in har Mommy ta kira sunan shi na asali to tabbas maganar da za ta mi shi mai mahimmanci ce."

"Na'am Mom, ina jin ki."

"Ni dai a iya sanina ba ni da abokin faÉ—a a rayuwata, haka kawai wata rana aka turo min sako ana min barazana, sosai na shiga mamaki dan ni ba shiga harkar kowa nake ba. Abu kamar wasa ake ce min "Idan ba ki yi abin da muka ce ba za ki rasa kowa naki."

Abin ya taɓani sosai amma ba wanda na faɗa wa sai Abban Abir ya ce na share maganar kawai 'yan damfara ne ke haɗa number suna yi wa mutane barazana su ba su kuɗi, hakan yasa na watsar da komai ko sun turo sakon bana bi ta kai har lokacin da aka rasa su Abir. Ba su sake nema na ba sai cikin satin nan wai ina lalata musu aiki komai suka shirya sai na wargaza musu, abin nan ya ɗaure min kai suna tambayata na ba su ma'adanar bayanai alhalin ban san meye ma ma'adanar bayanan ba." Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye da mayafinta..

Shuru Abdul ya yi yana tunani kafin ya ɗago ya dubi Mommy da duk jikinta ya yi sanyi, shi kansa lamarin na ƙara kulle masa kai, ga shi kullum matsalar sai ƙara kawo kai take, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Mom to wai wani irin shiri ne haka har da suke iƙirarin kina rusa shi? Na ga ke ba wani aiki kike ba kullum kina gida, in bakya gida kina gidan Baba Malam." Ya faɗa cikin takaici.

Grandma ta ce "To gane min hanya dai Abdullahi ita ba likita ba, ba ƴar sanda ba, ba Soja ba amma ake maganar wani ana ɓata shiri? Shi shirim ya ci ƙundun ubansa." Ta faɗa cikin faɗa, ita kanta lamarin ya tsoratar da ita...

Shuru Abir ta yi tana tunani ita kanta ba ta gane shirin ba duk da ta ga wasu abubuwan, to amma ma'adanar bayanan à ina rltake? Kuma meye a cikin ta da har suka sace su a kan ta? Wani tunani ya faɗo mata ta yi saurin dafe ƙirji tana gyaɗa kai, ta ɗaga baki za ta yi magana sai kuma ta tuna da kashedin su a kanta ta yi saurin yin gum da bakinta hawaye na ta zirya ba tsayawa.

Abdul ya ƙura mata idanu ganin yadda bakinta ke motsi ya ce "Baby da alama kina da abin cewa amma kin yi shuru."

Girgiza masa kai ta yi hakan ya fusata Abdul ya ce" Idan na sake miki magana kika girgiza min kai sai na kakkarya ki a palon nan."

"Ka yi haƙuri babu komai."

Tsaki ya ja sannan ya shiga kwantar wa da Mom hankali sannan ya É—auki numberta ya haÉ—a da wayarsa ta yadda duk wani sako da zai shigo wayar, to shi ma zai shigo ta shi wayar hakan zai taimaka masa wajan gano abin da yake son ganowa.

Abinci Laraba ta kawo masa tare da durƙusawa ta aje ta ce "Ranka ya daɗe aradu har ka bani tsoro." Ta faɗa tana dafe ƙirji ta sha wankan riga doguwa ta atamfa wadda Abir ce ta ba ta. Tsaki ya ja ganin super da ya saya wa Abir a jikin Laraba, shi gabaɗaya yarinyar ba ta kwanta masa a rai ba ga shegen surutu marar kan gado. Ganin ba zai ce komai ba ta wuce abin ta tana waƙar

_"A zauna wattaran a saɓa tilas ne, ka sanya a ranka arashi sai ya faru."_

Wani tsakin ya kuma ja ya ce "Mom Wallahi yarinyar nan ta ci kai." Murmushi kawai Mom ta yi ta bar musu palon, Abir ma kaÉ—an ta ci abincin ta ce ta koshi ta wuce É—akinta da sauri.

Tana shiga ta zauna a bakin gado tana dafe kai cikin damuwa, wandonta da ta cire tun ranar da ta dawo gida ta lalibo shi a ƙasan gado. Aljihun ta laluma nan ta zaro wani farin kyanle ɗan karami a laulaye, murmushi ta yi tare da soma warware abin da yake ciki, har ta kusa warwarewa ta miƙe zumbur ta buɗe wata loka a ƙasan Drowerta ta daga jerun pant ɗinta ta sakala a cikin sannan ta rufe ruf..

Zarya ta shiga yi a ɗakin tana neman mafita, tuna sun yi da Dattijo za ta je Unguwarsu yasa ta fita da sauri palon. Wayam ta gani ba kowa, tana son ta je part ɗin Umma amma tana tsoron cin mutuncin da suke mata ita da Mom ɗinta ga mummunan kalamai, hakan yasa ta haƙura ta koma ɗaki. Dama ita ba ma'abociyar yawo ba ce kuma ba ƙawaye take da su ba sai Iman..

Bayan kwana biyu ta faÉ—a wa Mom ga abin da take son yi, Mom ba ta hana ta ba ta mata fatan nasara a cikin lamarin.
Chapter 14 · 0% Book details