← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 120

Sashe 79

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fashewa ta yi da kuka tana tashi daga inda take ta koma gefen Inna ta kwanta a kan cinyarta, hakan ya ƙara saka su a damuwa ta shiga bubbuga bayan ta tana rarrashin ta har ta tsagaita kukan, Inna ta sake tambayar ya aka yi ta ji wannan ciwon? Sai a lokacin ta ji za ta iya magana ta tashi zaune tana runtse idanu saboda ciwon da hannunta ke mata kamar ana sassoka mata allura haka take ji, a raunane ta ce "Inna babu wanda fa ya zo gidan nan, kawai faɗuwa ce na yi a toilet shi ne na faɗi akan hannun shi ya sa ya kumbura yana min zugi, na bari ne mu gama cin abinci sai na nuna muku a kira mai gyara ya gyara min." Ya faɗa tana hararar Zaiyan da ya saki baki yana kallon ta. Har Zaiyan ya ɗaga baki zai yi magana ta yi saurin tashi ta isa gareshi tana masa murmushi ta amshe cokalin da ke hannunsa ta dinga ɗibar abincin tana ba shi a baki duk dan kar ya kuma fadin wani abu game da yayan nata, tsam su Inna sun gane ba ta son Zaiyan ya sake magana ne ta yi haka sai suka ci gaba da cin abincin. Bayan sun gama Baba ya fita ya kira mai gyara, sai da Inna ta rirrike ta aka mata soma mata gyara tana ta kukan azabam Ganin hakan da Zaiyan ya yi ya fusata ya buge hannun mai gyaran ya ce "Ka daina dukan ta ashe kaima ba ka tsoron Allah? To zan maka duka in ka sake saka Anty kuka, in ma kayana kake so ai sai ka faɗa na dauko ma na ba ka ba sai ka daki Anty ba zan ba ka." Yana fadin haka ya wuce dakin su. Mai gyara da ya gama tsorata ganin tsarkacecen matashi yana zare masa idanu sai ya saki hannun Abir, Baba ya yi murmushi ya ce "Malam Salihu ka rabu da wannan yaron ka ƙarasa gyara mata kafin ya fito, shi indai an taɓa ta to zai ce dukan ta ake."

Gyaɗa kai Malam Salihu ya yi cike da mamaki, ci gaba ta yi mata gyara mata Inna ta rufe mata baki tana ce mata "Yi hakuri a ƙarasa kar ta yi ihu Zaiyan ya yi ya fito ya hana a gyara mata, dan dole ta yi gum da bakinta ta shiga juya kai sai zufa take haɗawa. Wani irin ja Malam Salihu ya yi wa hannun ai kuwa ba shiri ta kwace bakinta ta sa ƙara tana kiran sunan Mom, sakin hannun ya yi ta dinga fitar da numfashin wahala za ta tashi ya ce sai an shafa mata magani ai ƙashin gwiwar hannunta je ya goce shi ya sa aka jima ba a gyara mata ba. Lumshe idanu ta yi hawaye masu ɗumi suka silalo mata a daidai lokacin kuma Zaiyan ya fito hannunsa dauke da leda babba ɗayan leda ce babba hannun kuma takalma ne kala uku, da kallo suka bi shi har ya iso ya aje a gaban Malam Salihu ya yi raurau da idanu ya ce "Ga shi nan na kwaso ma kayan ka tafi da su duka amma karka sake dukan Anty ta yi kuka, ba ka ga yau da Baba ya zo gidan nan ba ya dake ta kawai ni kuma na rama mata. Yanzu kai za ki ji daɗi in aka daki Antynka?" Ya faɗa yana matso ƙwalla suka zubo kaɗan..

Sake da baki Malam Salihu ke kallon ikon Allah dan shi a iya sanin shi da Baba bai san akwai mai larura a gidansa ba, ganin bai ce komai ba Zaiyan ya matso kusa da shi yana hawaye ya ce " Baƙo ka dinga jin tsoron Allah ka daina dukan Anty, tun da kayan nan kake so ga shi nan na kawo ma ka dauka ka tafi ka bar mana gida." Ya yi maganar yana rushewa da kuka kamar wanda aka daka..

Mamaki da al'ajabi ne suka ƙara mamaye Malam Salihu, nisawa ya yi ya ce "To shi kenan na daina amma ka aje kayan ka yanzu zan tafi daga gidan naku."

Girgiza kai ya yi ya isa gaban ta ta zuba masa idanu so take ta yi dariya amma zugin da hannunta yake ya hana ta yin hakan, hannun mai ciwo ya ɗan taɓa yana tsayar da kukan ya ce. "Anty a nan ne ya dake ki ko?."

Kyale shi ta yi sai da ya sake maimaita maganar ta daure ta ce "Kwashe kayan wannan ka mayar da shi É—aki indai ba ka so na daina ma magana."

Da sauri ya kalli kayan sai kuma ya ce "Kayan baƙo ne kin ga ai ba zan daukar masa ba."

Sai da aka yi da gaske sannan ya kwashe kayan yana cewa Malam Salihu ya ba shi kayan ya kai dakinsu ya ce masa e tukun ya shige dakin. Sallama ya musu ya miƙa musu maganin da za take shafawa a hannun ya tafi, itama ta tashi ta nufi ɗakin inda ta samu ya yi ɗaiɗai da kayan sawar shi, ganin ta shigo ya janyo ledar ya dinga cusawa yana ce mata ga shi yana mayar da kayan ta girgiza kai ta hau gado ta kwanta. Sai da ya gama duk shiriritar shi sannan shi ma ya iso gadon ya kwanta yana mata surutu ta yi kamar ta yi bacci har ya gaji da yin maganar bacci ya kwashe shi....

Abdul da kyar ya iya barin Layin Unguwar sai kyarma jikinsa yake dole ta sa ya tsayar da motar y kira Ali ya zo ya dauke shi. Asibiti suka nufa Doctor Hashim ya duba shi yana tambayar shi me ya same shi haka amma ya yi banza ya kyalle shi har ya gama masa bai ce da shi komai ba, shi ma sanin halin abokin nasa sai kawai ya share shi bayan ya masa allura ya yi masa sallama ya nufo gida. Tunani yake wata kalar azaba zai gana wa Abir da ta sanadin ta aka masa haka? Sosai zuciyarsa ke tafasa sai kwafa yake da haka iso gida. Ko da ya zo gidan tambayar duniyar nan Hafsat ta yi amma ko ci kanki bai ce mata ba har da kuka ta yi dan ya faɗa mata dalilin jin ciwuka a jikinsa amma ya yi kunnen uwar shegu da ita, karshe ma tashi ya yi ya shige ɗaki ya bar ta a palon. Haka ya wuni a ɗaki har dare yana ta saka da warwara ya rasa wani hukunci zai yi mata dan ya wuce, yanke shawara ya yi kawai ya kashe ta bayan ta ba shi abin da ya buƙata kawai kowa ma ya huta, dan haka y ɗauki wayarwa wajan karfe goma na dare ya yi mata dogon rubutu ya tura mata....

Kamar daga sama tana zaune bayan ta yi ruwan ɗumi ta gasa hannunta ta ga sakon shi ya shigo wayarta, hannu na rawa ta dauka a zaton ta ko hakuri zai ba ta akan abin da ya mata amma sai ta ga saɓanin haka..

_"Baby tabbas zan iya kasheki akan wannan abin, idan har ba ki ba ni ta ruwan sanyi ba to za ki ga me zai biyo baya k.._

Saurin fita ta yi tana dafe kirji cikin tashin hankali, tashi ta yi tsaye ta dinga kaiwa da komowa tana tunanin abin da za ta yi. Can dai ta janyo akwatunanta ta zuzzuba kayanta da na Zaiyan da duk abin da tasan nasu ne, bayan ta gama ta zarge ta bubbuga Zaiyan ya tashi zaune ta janyo hannunsa ya sauko. Gabadaya jikinta rawa yake ta nuna masa ya riƙe wannan duka za su tafi wani waje, murna ya dinga yi ya soma mata surutu ta yi saurin ce masa in ya yi magana ba za ta tafi da shi ba sai ya yi shuru. Hijab ta saka ta cire wayarta a caji ta dauki cazar ta suka fito a hankali hannunta ɗaya sarƙafe a jikin wuyanta ɗayan kuma ta ruko akwati tana ja a hankali har suka fito harabar gidan, ta ce ya tsaya kar ya matsa ya ce mata to ta koma cikin sanɗa ta shiga dakinta buɗe loka ta janyo takarda da biro ta soma rubutu tana zubar da hawaye har ta gama, akwatin ta janyo ta fito palo ta aje da takardar tana share hawaye ta fita.. A hankali ta buɗe get ɗin ta fitar da Zaiyan ta ba shi kayan yana fito da su waje itama ta fito ta janyo kofar a hankali suka ja akwatunan suka hau hanya suna ta tafiya...

Sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka samu motar haya ta faÉ—a masa inda zai kaisu, suna tafiya tana sharar hawaye har suka iso wani hotel ya paka ta biya shi kudinsa ya fito musu da kayan ta ce zaiyan ya janyo su tafi ta janyo É—aya suka nufo ciki. ÆŠaki ta kama musu na kwana É—aya aka kai su ta yi musu godiya, alwala ta É—auro ta dinga sallar shi kuma Zaiyan ya zauna yana ta kallon ta karshe ma bacci ya kwashe shi. Yadda karen dawa bai runtsa ba haka Abir ba ta yi bacci ba tana zaune ta jingina da bakin gadon..

Washegari karfe tara ta yi wanka ta masa ta shirya su ta kira aka kawo musu pizza da tea suka yi breakfast, bayan sun gama suka fito da kayan su ta biya kuɗin suka tafi, sai da ta saka niƙaf. Mota ta tara suka shiga mai mota ya ce ina za a kaita, ta yi shuru ta rasa ma ina za ta faɗa masa can dai ta ce masa "Za ka iya kaimu Kano?"

Girgiza mata kai ya yi ya ce "Gaskiya Hajiya ba zan iya ba amma zan kaiki tasha sai na haÉ—a ki da wani abokina yana zuwa Kano."
Chapter 79 · 0% Book details