Sashe 96
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dukkan su sai gyaɗa kai suke kamar wasu ƙadangaru suna sauraron shi har ya gama jawabi, Jarmai ya buɗe baki zai yi magana ya ji ƙaran wayarsa da ke gefen shi, hannu ya sa ya ɗauka sai ya ga ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan jaridar da suka dauka ne ya kira shi. Karawa ya yi a kunne kafin ma ya yi magana na cikin wayar murya na rawa ya ce "Hello ranka ya daɗe idan kuna kusa da tv ku kunna tashar Albarka tv akwai abin da yake faruwa."
Hannu na rawa Jarmai ya sauke wayar ya janyo remote ya kunna tv da ke palon, kai tsaye ya kawo tashar da aka ce ya kawo, shuru suka yi dan lokacin a tashar sun tafi hutun taƙaitaccan lokaci, bayan sun dawo ne aka ɗaura daga inda aka tsaya inda mai gabatar da shirin ya soma faɗin, _"A yau ne aka gano wasu lefuka masu muni wanda su Alhaji Mustapha dan takarar gwamna shi da abokan shi suke aikatawa, suna safarar mata daga nan Nigeria zuwa ƙasashen Turai ana mayar da su karuwai, wanda wani matashi mai suna Damisa ne ya tabbatar mana da hakan ya kuma sanar da mu gidansu na shaƙatawa a can suke kai yaran su aje kafin a fita da su ƙasar waje."_
Saurin kashe TV Jarmai ya yi yana zaro idanu waje, dukkan su ba wanda bai girgiza ba da jin wannan labari, nan take Alhaji Mustapha ya kira wata number ana ɗauka ya soma faɗin "Duk inda wannan ɗan jaridar yake ku nemo min shi ku masa barazana ta yadda da kansa zai ƙaryata wannan labarin da ya yaɗa, sannan ku tabbatar kun gano min a wani hotel Damisa yake a faɗin garin nan." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar sai huci yake, sai da ya jima a haka sannan ya ce "Yau ba sai gobe ba za mu tafi gidan boka kuma yanzu nake so mu tafi ba sai kowa ya je gida ya shiryo ba. Idan har muka zauna a haka Damisa zai mamaye mu gabaɗaya."
Ba wanda ya yi muso da maganar tasa suka sa aka samar musu da tickets na zuwa Legos, ba su daÉ—e ba aka ce masu komai is ready suka yo Airport, ba jimawa jirgin yan kasuwa ya sauka suka hau sai Legos..
Laraba ta shirya tsaf cikin shirin ta na shigar abaya ƴar Dubai ta yi rolin da mayafin a kanta, baƙin glas ta saka ta fito palon tana riƙe handbag ɗinta a hannu cike da aji ta tsaya, kallon ta Damisa ya yi ya yi ƴar dariya ya ce "Wannan kyau haka sai ka ce matar Gwamna, wannan sai ki sa a dinga kallon ki duk inda kika nufa."
Dariya ta yi tana cire glas É—in ta ce "Haba dai Oga ni da zan fita aikin Allah ai sai na nuna wa waÉ—anda zan je wajan su ni ba kanwar lasa ba ce, dan haka kai dai ka haÉ—o ni da bodyguard É—inka mu wuce Kar mu shiga time É—in aiki na gaba."
Jinjina ya mata yana murmushi ya ciro bandir goma cif ɗaurin yan rafa ya miƙa mata, baki ta saki tana kallon shi cike da mamaki ta ce "Oga ya za ka miƙo min kuɗi har miliyan ɗaya na kai wa ƙaton banza ya ci? Ni fa da za ka bi shawarata da kawai mun yi yadda na tsara, idan har ya ga ba haza zai yi mana abin da muke so."
Murmushi ya sakar mata ya koma ya zauna yana faɗin "Nasan fa me nake yi Jk, ai da wannan aka ruɗe shi har ya yi abin da aka sa shi, to muma da shi za mu ruɗe shi ya mana abin da muke so, kin san fa ta hanyar da aka hau ta nan ake sauka! So wannan ba komai ba ne matuƙar buƙata za ta biya, idan har yaƙi bamu haɗin kai ne za mu fahimtar da shi a yaren da zai gane. "
Dariya Laraba ta yi tana gyara zaman Jakarta ta ce "Wani lokacin fa kai mugu ne Oga."
Shi ma murmushi ya yi ya ce "Ke dai je ki kawai."
Sallama ta masa ta kwashe kuÉ—in ta sa a jaka ta fita zuwa harabar gidan, direba ya buÉ—e mata mota ta shiga suka bar gidan..
Umma na zaune gaban malam tana koro masa bayanin sabon aikin da zai mata, sai da ta gama masa bayani tas ya É—ago ya kalle ta yana murmushi ya ce "An yi an gama dan yanzu haka na gama aikin, amma ba fa zai É—auki lokacin bai yawa ba asirin zai karye, saboda yana samun kariya daga wata aljana mai mugun haÉ—ari, abin da ya sa ma har na samu na cika aikin a yanzu ba ta a tare da shi ta yi tafiya, kuma tana gaf da dawowa."
Wani kalar shu'umin murmushi Umma ta saki tana jin daɗi ya mamaye ta, sake kaɗa baki ta yi ta ce "Ka tura masa masu ƙarfin gaske wanda zai mata faɗe ta yadda za ta kamu da yoyon fitsari ta ruɓe ta lalace, dan nasan yanzu dai ba ta kuɗin da za ta biya ayi mata magani in ya mata faɗen, sannan asa mijin da ya mata haka ya shiga duniya kar su sake haɗuwa ita kanta ina so ta dauwama a inda take rayuwa yanzu. Sannan ina so 'yata ta mallake mijinta sai abin da ta ce masa. "
Ƴar dariya ya yi yana kallon Umma ya girgiza kai ya ce" wato Hajiya ke a layin marasa imanin ma ke number one ce, ki yi komai ba komai Hajiya aljanna ta mai rabo ce. "
Dariya ta yi tana jin kanta ya ƙara girma ita ga ta ba mai ja da ita ya kwana lafiya, tashi ta yi ta ce masa ayi a gama mata komai kafin ita wannan aljana ta dawo, dan so take a farraƙa su ko a hanya kar su haɗu da juna. An ga Malam ya ce mata sannan ta tafi..
Tana fita kamar da minti goma ya ji ana neman izinin shigowa, izini ya bada ta shigo tana shan ƙamshi ta zauna tare da gaishe shi, ganin santaleliyar budurwa a gaban shi sai ya washe baki yana faɗin "Sannu da zuwa Hajiya."
Hararar shi ta yi ta cikin glas É—in ta gyara zama sannan ta amsa, yana washe baki ya ce "Hajiya me ke tafe da ke?"
Yatsina fuska ta yi ta ciro kuɗin da aka ba ta ta dire masa shi a gaban shi, Malam ganin tsallar madarar kuɗi maƙudai a gaban shi sai ya ruɗe yana shafa gemu ya ce "Ma sha Allah, to wani kalar aiki kike so ayi miki Hajjaju?"
Ji ta yi kamar ta kai masa naushi a baki jin ya ce ma sha Allah kamar wani mutumin arziƙi, Nisawa ta yi ta ce "Waccan matar da ta tafi nake son ka warware duk wani aiki da kasan ka yi mata, ni kuma zan kawo maka talumkar wannan kuɗin da kake gani a gaban ka."
Kwalalo idanu waje Malam ya yi yana kallon ta sai kuma ya kalli kuÉ—i, ga kuÉ—i amma kuma in ya tun irin amanar da ke tsakanin shi da Umma sai ya ji ba zai iya warware mata aiki ba, shi kansa bai san iya adadin aikin da ya mata ba wanda ta sa ya yi aikin a kan su wasu sun mutu wasu kuma bai san ma a wata duniya suke ba, ya girgiza kai ya ce "Hajiya gaskiya ni da matar nan akwai amana, shekara da shekaru ina mata aiki babu ta yadda za ayi rana tsaka na zo na warware mata aiki ba, wani aikin ma na manta yadda na yi shi bare na warware."
Ran Laraba ne yayi mugun ɓaci ta zare glas ɗin da manne a fuskarta tana masa kallon za ka yi bayani, gyara zama ta yi ta ce "Malam ko na ce Boka ka yi abin da na faɗa ko kuma ka ga abin da zan yi maka." Ta faɗa tana zaro bindiga daga cikin Jakarta ta saita satin goshinsa tana hura hanci ta ce "Za ka warware ko kuma ba za ka warware ba.?"
Jikin Malam ne ya dauki rawa karr karr karr ganin bindiga a zahiri, baki na rawa ya ce "Hajiya sauke bindigar mu yi magana kin ji."
Saukewa ta yi ya kalle ta a tsorace ya ce "Wanne da wanne kike so na warware miki?"
Ƙara daure fuska ta yi ta ce " Faɗa min irin aikin da ka yi mata ko na fasa kanka yanzu."
A ruÉ—e ya soma faÉ—in "Gaskiya in na ce zan faÉ—a miki adadin aikin da na yi wa Hajiya to na yi karya, saboda matar nan tun kafin ta yi aure take zuwa wajena na yi mata aiki, hasali ma nine na fara sanin ta a 'ya mace kafin ma ta kai ga yin aure, aikin da na mata wanda daga shi nake mata manyan aiki shi ne ta sa na sawa matar Yayan mijin da za ta aura sihirin kar ta ga jininta a duniya, duk cikin da za ta samu sai ya zube.." Ya É—ago ya kalli Laraba da ta nutsu tana jin bayanin shi, jin ya tsaya ta ce " Ci gaba mana ina jin ka. "