Sashe 94
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyara zama Damisa ya yi ya ce "In sha Allah wannan karon shi ne zuwana na karshe da sunan aiki, kuma har Kano zan je ina da wasu abokan aiki a can."
"To Allah ya taimaka Oga, Jk ke ma kin ɓata rabona da ganin ki tun zuwan ki na farko ƙasar nan."
Ƴar dariya ta yi ta ce "Muhammad kenan, yo ai ni ina ƙasar babu inda naje."
Sani halin Damisa baya son a dinga doguwar magana sai kawai ya ce ta ji daÉ—i.
Wani dan madaidaicin gida suka yi hon aka bude musu get suka kutsa ciki, suna gama packing suka fito Maigadi na musu barka da zuwa ya amsa sannan suka wuce ciki..
Wanka suka yi Laraba ta canja kaya ta sanyo abaya ta fito ta É—aura musu girki mai rai da lafiya, a cikin kalolin girkin da Mom ta koya mata ta musu haÉ—aÉ—É—an girki. Bayan sun gama cin abinci suka dawo palo kowa ya fito da computer shi suka hau aikin da yake gaban su..
Yau kawayen Ta Sakkwato suka zo kitso wajan Abir tun karfe 10:30am na safe, manyan mata ne irin 'yan kwalisar nan matan masu hannu da shuni, Abir ta yi ta mamakin inda ta Sakkwato ta samu irin wannan ƙawaye haka, jin ana kiran ta ta ɗago da kan Zaiyan da zazzabi mai ƙarfin ya rufe shi ta kwantar. Bude idanuwansa ya yi ya sauke su akan ta ta sakar masa murmushi ta ce "Ka kwanta ka ji in sha Allah zuwa gobe zan kaika asibiti in kuɗi suka taru, yanzu na yi baƙi kar ka fito waje an jima zan shigo na ba ka magani." Ta faɗa tana taɓa gefen wuyansa ta ji har yanzu zafi rau zazzabin na nan bai ragu ba, cike da damuwa ta janyo ɗan madaidicin bargonsu ta lulluɓa masa ta fita. Da kallo ya bi ta har ta rufe masa kofar ya tashi ya zauna, kansa da ke mugun sara masa ya riƙe yana jin yadda ake masa dakan tsakwara a cikin kan, wani kalar numfashi ya dinga fitarwa ya yi baya ya faɗa kan katifar, nan da nan jikinsa ya dauki rawa ya ƙanƙame jiki yana fitar da numfashi da sauri-sauri tamkar wanda ya zo gangarar mutuwa. Wani farin kumfa ya dinga fita daga bakinsa idanuwansa suka ƙaƙƙafe ya dinga fisgar numfashi da ƙarfi yana durje-durje irin na wanda rai ke ƙoƙarin fita daga gangar jikinsa, can kuma kamar an tsikara masa allura idanuwansa suka dawo daidai ya tashi zaune yana rarraba idanu, wani kalar murɗawa cikinsa ya yi ya cije lip ɗinsa na ƙasa yana juya kai, tamkar macen da ke kan nakuda ciwo ya tashi ba zama ba tsayuwa haka Zaiyan ya dinga birgima yana juyi. Ya daɗe a haka cikin ya sake murɗawa sai amai ya biyo baya kamar an bude famfo, sai da ya amayar da abin da ya ci tas amma bai daina kakarin aman ba sai nishi yake, ya dauki lokaci a haka tukun ya daina kakarin ya zube a gefen da ya yi aman sai bacci...
Abir kuwa na can a ƙofar Ta Sakkwato tana yi wa ƙawayenta kitso, amma gabaɗaya hankalinta sam ba ya ga hirar da suke yana kan mijinta, abubuwan da ya tsuro a cikin satin nan duk ya dame ta, ya daina magana ba ya iya cin abinci sosai da ya soma ci zai turo, wanda a in a baya ne zai ci abincin mutum uku ƙwarara ya kuma ce mata bai ƙoshi ba sai dai ta rabu da shi dan kar ya ƙwari cikinsa, ya dawo kamar kurma komai za ta yi masa sai dai ya kalle ta da ido kawai ba ya cewa e ko a'a. Nisawa ta yi jin ɗayar matar na cewa "Jiddo ni irin na ta Sakkwato za ki yi min."
Murmushin yaƙe ta yi tana ƙarasa wa wadda take wa ta ce "To Hajiya in sha Allah."
Kallon ta matar take sai kuma ta ce "Jiddo kamar fa na taɓa ganin fuskarki a Tiktok, ba ke ba ce aka ce za ki auri ɗan sarkin Niamey sai ranar ɗaurin aure ya ce ba ya son ki ƙanwarki zai aura?ko ba ke ba ce tabbas kuna kama gaskya, sai dai kamar ita wacce ɗiyar masu kuɗi ce a garin Yola ko ya ma sunan Familyn nasu?"Ta faɗa tana sake kallon Abir.
Tun da ta fara magana gaban Abir yake bugawa cikin tashin hankali, gyara zama ta yi ta kalli matar tana murmushi ta ce" Ayya Allah sarki Hajiya, ni ma wannan matashiyar Æ´ar tiktok É—in naji ana maganar ta sosai, an ce tana kama da ni amma ni ban ma san ta ba gaskiya, matso a kama miki mijina ba shi da lafiya yana É—aki a kwance. " Ta nisa ta dubi Ta Sakkwato ta ce "Mama don Allah ki yi wa Baba waya in zai dawo ya zo min da maganin maleria."
Ta Sakkwato da ta yi saƙare tana kallon ƙawata ta ɗauke kanta daga kallon ta ta dawo kan Abir, ganin yadda duk ta yi kicin-kicin da fuska sai ta ji ta ba ta tausayi, tasan rayuwarta ta baya ta tuna. Tashi ta yi ta shiga ɗaki ta dauko waya ta kira mijinta ta sanar da shi ya tafo wa da Abir maganin maleria ya amsa da to sannan ta kashe kiran, tana fitowa ta sanar ta ita ya ce zai kawo mata ta mata godiya..
Komai cikin sauri take yi dan ta ƙagara ta gama musu su tafi ko ta koma wajan mijinta, tana gaf da gamawa ta biyun sai ga wasu yara biyu, dayar ba ta fi 14 ba dayar kuma ba ta fi ƴar shekara 10 ba sun yo wajan su da sallama, amsa musu suka yi babbar ta kalli Ta Sakkwato ta ce "Ta Sakkwato Mamanmu ta ce mu zo wajan ki ki sa Jiddo ta mana kitso da lalle za mu tafi wajan biki Kaduna gobe."
Murmushi ta yi sai kuma ta ce "Ku zo na ga kuɗin hannunku in bai kai yadda ake yi sai ku koma ta ƙaro muku."
Kuɗin suka miƙa mata ɗari biyar ce, riƙe baki Ta Sakkwato ta yi ta ce "Wallahi Aisha muguwar ƴar rainin hankali ta, yo wannan ai kuɗin babbar ne ta bayar." Wayarta ta dauka ta kira Aisha ta rufe ta da masifa tana fadin wai babbar za ayi wa kitso da ƙunshi dayar kuma sai ta ƙara biya, da kyar da siɗin goshi Aisha ta shayo kan Ta Sakkwato ta ce za ta shigo ɗaukan su sai ta ƙaro ɗari uku ayi musu su duka, duk da haka sai da Ta Sakkwato ta mata tas sannan ta kashe wayar.
Duk da Abir na cikin damuwa sai da ta yi murmushi ganin yadda Ta Sakkwato take masifa har kumfan baki take, sake kallon ta ta yi ta ce "Allah Mama ki rage faÉ—a, kin ga su yan gida ne ana mutumci sai ake rage musu ai ba komai."
Hararar ta Ta Sakkwato ta yi ta ce "Wagga yarinya ba ki san rashin daraja irin ta matan Layin nan ba, indai kika nuna za ki musu Kyauta to fa sai sun kai ki maƙura, dan duk wacce ta kunce kitso za ta zo ki mata ta ba ki naira ɗari biyu ta yi gaba dan ba su san zafin sana'a ba, dan haka ki ma daina yi musu sako-sako kar su kashe ki daga tsaye. "
Ita dai murmushi take ƙawayen ta Sakkwato suka biya ta kuɗi mai tsoka tare da mata godiya suka tafi. Har ta yi wa babbar rabin kison ta ji ana kiran Sallah ta saki ta ce za ta yi Sallah, suma cewa suka yi za su yi Sallar Ta Sakkwato ta ja su ɗakinta...
Buɗe ɗakin ta yi ta shiga sai ta gan shi kwance kan tabarma, isowa ta yi sai ta ga amai felas a gaban shi ta waro idanu tana birkito shi, tashi ta yi ta dauko ɗan ƙaramin towel ɗinta na ka ta jiƙo da ruwa ta dawo kan shi, fuskar ta goge masa ta tare da ɗago da kansa ta tura shi da kyar ta ɗaura masa kan akan katifa, rigar jikinsa ta cire ta rufa masa bargo ta dawo tsakar ɗakin ta goge aman tana zubar da hawaye ciki da tausayawa, sai da ta goge tas ta gyara wajan ta dauko turare har za ta fesa sai ta tuna in fa ta fesa ta shaƙa akwai matsala, banɗaki ta koma ta tsiyayo chappo da suke wanka ta zuba ruwa ta dauko ta goge tsakar da shi. Sai a lokacin ta ji ƙarnin aman ya ragu sosai ta wuce toilet ta ɗauro alwala, tana fitowa ta gabatar da Sallah ta daga hannu sama tana ta kwararo musu addu'a ta samun sassauci na halin da suke ciki ta shafa.
Fitowa ta yi ta ƙarasa musu bai ma bushe ba yaran suna murna suka tafi gida ganin uwar tasu ba ta zo ba da ta ce za ta shigo, ita kuma ta ɗaura musu girkin taliya fara da man ja, ko da ta gama kasa ci ta yi saboda jikin nasa ya yi zafi sosai, ga shi duk ta haɗa kan kuɗin da ke wajan ta ta sayo musu kayan abinci iya kuɗin kitso da kunshin yau gare ta ballantana ta kai shi Asibiti, hakan ya sa duk ta damu ta kasa fitowa daga ɗaki ta tasa shi gaba kamar ta samu tv lokaci zuwa lokaci tana share hawaye...
Bayan mijin Ta Sakkwato ya dawo ya kawo mata maganin ta jika ta ba shi da kyar yana kaucewa rabi ya sha rabi ya zube, sai lokacin taji sanyi da ta ba shi maganin ta fito wajan matan gidan tare da fito da silitif ɗin ƙunshi ana hira tana yankawa dan kar azo nema babu. Can cikin dare suna bacci ta ji wani abu mai nauyi ya danne ta, da kyar ta buɗe idanu ta sauke su a kan shi ya kwanta a ruwan cikin ta, gyara masa kwanciya ta yi duk da nauyin da take ji ta koma bacci, kamar wasa ta ji yana taɓa ko'ina na jikinta ta zabura ta yunƙura za ta ture shi amma ta kasa.