← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 120

Sashe 114

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tun daga lokacin duk wani sihiri da ta yi ya dinga karyewa, ƙarshe fatar jikinta ta yi baƙi da ta yi wajan mutane sai ayi ta gudu, abin ya tayar mata da hankali ta shiga neman magani amma duk in da ta je sai a ce ba za a iya magani ba ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙiya, ganin rayuwa ta juya mata baya ta dawo ta tona wa kanta asiri ta sanar da su komai. Sarki ya fusata sosai ya ce ya sake ta babu shi babu ita, ganin haka ya sa Haris ya ce shi ba zai iya mulki ba dama Fulani ce ta cusa masa son yin mulki ya bar wa ɗan'uwansa zai koma England ya ci gaba da karatunsa tare da matan sa. Haka ya haɗa kayansa ranar da zai tafi Fulani ta dinga kurma ihu tana sururutai tana cirar gashin kanta, hankali a tashe aka rufo ta a ɗaki kafin a kawo malami ta rasu. A lokacin kuma Husna ta samu ciki shi kuma Haris bayan an yi wata da mutuwar Fulani ya yi tafiyar sa, dole Abdulwahid ya amshi mulki.. Auren Abdulwahid da ɗiyan abokan Mai martaba wata hudu Husna ta yi ɓari, ta sha kuka sosai dan ta ƙwallafa rai akan cikin dama tana kukan rabuwa da jaririnta, ɓarin nan sai ya fama mata wannan ciwon da ke danƙare cikin zuciyarta. Daga nan ba ta sake samun ciki ba sai da Kilishi ta haifi ɗanta namiji aka sa masa Sultan, har sai da ya kai shekara biyu sannan itama Allah ya ba ta ciki ta haifi ɗanta namiji wato ni kenan, sai da na yi shekara goma da haihuwa sannan aka haifi ƙanwata Ikilima yayin da Kilishi ta sake haifo ɗanta namiji mai suna Arma. Zaman Mamma da su Kilishi kamar zaman Kakarmu ne da kishiyarta Fulani Abida, dan duk wani rashin mutumci in suka kwaso ita suke zubawa, sukan ce mata ɗiyar matsiyata da ko danginta ba a sani ba, wannan kalma na ƙona zuciyar Mamma haka take kauda kai ba dan ba ta da abin faɗa ba sai dan kawai ta nuna biyayyarta ga mijinta da ya ce kar ta kula su ko me za su ce a kanta. Kwatsam wata rana Mamma ta tashi da ciwon wuya aka kira likita ya duba ta ya ce babu matsala ya rubuta magani aka sayo mata, abu kamar wasa sautin muryar Mamma ya dauke tun ina ɗan yaro dan lokacin shekaruna 13 ne a duniya, haka ta kasance ta dawo kurma tana jin komai amma ita ba za ta iya bude baki ta yi magana ba. A daidai wannan lokacin ne kuma Mai martaba ya amsa kiran mahaccinmu ya rasu. Allah buwayi gagara misali yanzu haka Mamma ta samu lafiya tana magana kamar kowa, sannan ta kan ce mana za ta dawo Nigeria ta yi cigiyar danginta, wanda tun kafin ta samu lafiya ni na gano dangin nata." Ya fesar da iska daga bakinsa.

Sauke tagumi Abir ta yi cike da al'ajabi ta ce "To Amma Ya Suhal taya aka yi ka gano dangin nata?"

Murmushi ya yi ya É—ago ya kalli Zaiyan ya ce "Ta dalilin É—an'uwana na gano su."

Abdul ya haÉ—e hannayensa waje É—aya ya ce. "Kamar yaya kenan?"

"Ni yanzu abin da nake son sani a wajan ka shi ne, ya aka yi kasan cewa nine Damisa? Wanda in ba abokan aikina ba babu wanda ya san wannan sunan."

Murmushi ya yi ya girgiza kai ya ce kun san ya aka yi na san kaine Damisa ?"

Girgiza kai suka yi a tare, hakan ya ba shi damar ci gaba da cewa "Wata rana na zo Nigeria cikin garin nan kwatsam zan shiga wata Asibiti sai na ci karo da Zaiyan lokacin yana tsakar yin hauka, na yi ta kallon shi ganin yadda muke kama har ya iso kusa da ni ban sani ba sai ji na yi ya warci gorar ruwan da ke hannuna ya wuce fuu, da kallo na bi shi har ya tsallaka bakin hanya ya wuce. Tun daga ranar na kasa sukoni na tuna da labarin da Waziri ya ba ni na cewar su Mamma sun yi zama a Nigeria kuma har sun haifi yaro yanzu ba su san yana raye ko ya mutu ba, hakan ya sa naƙi komawa England wajan karatu na kuma dawowa Nigeria. Da zarar na zo bakin asibitin nan zan gan shi, wata rana na juyo zan dawo sai na haɗu da wata mata ta tsare ni ta ce "Bawan Allah ka taimaki ɗan'uwanka." Da mamaki na ɗago kai sai na nemi matar nan na rasa, hakan ya sa da na dawo masaukina na dinga tunanin taya zan taimaki wannan mahaukaci da nake gani? Da yake ina da abokai wanda muka yi karatu da su a England na sa suka nemo min Zaiyan a lokacin dan na kai shi Asibiti, muna zuwa ko taɓa shi ba ayi ba ya gudu daga asibitin aka neme shi aka rasa, na damu sosai haka na dinga bin diddigi ko zan samu labarinsa har Allah ya sa na haɗu da wani abokin aikinsa, inda ya sanar da ni tarihin rayuwarsa har sunan da ake kiransa da shi Damisa, ya kuma ce min yanzu ba shi da kowa a wani kango yake kwana.. Na kaɗu da jin labarinsa hakan ya sa na tattara na nufi Kano naje har office ɗin da ya yi aiki, da farko sun ɗauka shi ne sai da na sanar da su ba shi ba ne ɗan'uwansa ne, sun sha mamaki dan su a iya sanin su da Zaiyan ba su taɓa ji ko gani ya ce ga ɗan'uwansa, su suka haɗa ni da abokinsa Bashow.. "

Waro idanu Zaiyan ya yi yana jinjina lamarin, Suhal ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ci gaba.

"A wajan Bashow na ƙara samun duk wani abu na Zaiyan, har aikin da ya fara akan su Alhaji Mustapha in da shi Bashow ya yi ta ƙoƙarin ya ɗauko Zaiyan daga Yola ya dawo da shi Kano amma abin ya gagara, saboda da an yi niyar zuwa ɗaukan shi sai a neme shi a rasa gabaɗaya. Bayan na koma Niger na samu wata friend ɗina wadda ta dalilin ta ne na gano Zaiyan ɗan'uwana ne, na aminta da ita na sanar da ita abin da nake son yi dan itama ma'aikaciya ce kamar Zaiyan. Ita ta binciko min har da photon Inna Asabe ta samo, bayan na iso Nigeria daret Kano ma sauka dan na tattauna da friend dina Jk, har masaukin da nake ta zo muka zauna nan take sanar da ni ai tasan matar nan ƙawar mahaifiyarta ce a da tana aiki a gidan wani attajiri mai suna Alhaji Abdu, jin haka ya sa na tambaye ta sunan matar in da ta sanar da ni sunan ta Husna. A take naji jikina ya ƙara yin sanyi, na ce mata shi mahaukacin ɗanta ne? Ta ce da ni "A'a, ai Inna Asabe ba ta taɓa haihuwa ba wata rana ta zo gidanmu Mamana ke tambayar ta ya aka yi ta rayu bayan an ce gidan gabaɗaya ya ƙone kurmus? Sai ta sanar da ita duk abin ya faru da ita da yaron da ke wajan ta a lokacin Zaiyan ya girma, haka suka sha kuka Mamana ta nemi da ta rufe wannan sirrin kar ta kuskura ta sanar da kowa ta riƙe shi a zaman ita ta haife shi. To ba su san ba ina jin abin da suka faɗa hakan ya sa na ce zan bi ta na wuni a gidanta, da murna ta ce mu tafi. Bayan naje na ga Zaiyan zuciyata ta cika da tausayin shi. Ban taɓa sanin ya samun ciwon hauka ba sai yau, tun da suka bar garin ba mu sake ganin Inna Asabe ba har itama Mamana ta rasu."
Chapter 114 · 0% Book details