← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 120

Sashe 95

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda take tunanin Zaiyan yau ya shallake tunanin ta, abin da ba ta taɓa tsammani ko zato daga gare shi ba yau shi take ji da gani, a iya rayuwarta in aka ce mata Zaiyan zai aika mata haka za ta musa, jin abin yana neman wuce gona da iri ta daddage ta ƙarfin tsiya ta hankaɗa shi can gefe ta fashe da kuka mai sauti sai kuma ta yi saurin toshe bakinta tana tashi zaune,

Kallon shi take duk da ɗakin da duhu amma ɗan hasken fitilar da ta kunna ya sa ta hango shi yana ta juyi. Ta jima tana kallon shi tun yana juyi har ya daina bacci ya dauke shi, gabaɗaya wani mugun tsoron shi ta ji ya mata dirar mikiya, wai yau Zaiyan ne ke ƙoƙarin raba ta da tufafin jikinta abin da ko a mafarki ba ta yi tsammani ba, dan ita a tunaninta ba zai taɓa neman ya yi wani abu na auratayya da ita ba, tashi ta yi da sauri ta shige toilet tana goge kawaye, ganin jinin al'ada ne ya zo mata duk da haka ta ɗaura alwala ta zo ta zauna ta dinga lazumi tana kallon shi, karshe bacci ya kwashe ta a kan abin Sallar cike da mafarkai kala-kala....

_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na (47)

Kiran Sallah Asuba ne ya tayar da ita daga nannauyan baccin wahalar da ya dauke ta, a hankali soma ta buɗe idaunwanta da suka yi mata nauyi saboda kukan da ta ci ga baccin da ya rufe idanu, da kyar ta iya tashi zaune tana yarfa hannu ba shiri ta koma ta kwanta, wani azababben zafi mai fitar mutum daga haiyaci ya ziyarce ta, a gabaice ta sake yunƙurawa tana cije lip ɗinta na ƙasa cikin wani kalar yanayi marar musaltu, da kyar ta zauna tana runtse idanu mararta ta mugun ɗaure mata ga zafi sosai da take ji, kallon ƙafafuwanta ta yi ta ga har sun fara kumbura kamar na mace mai tsohon ciki ta ja numfashi da kyar tana juya kai, jin tana neman sheƙawa ba shiri ta sunkuya ta rarrafa ta isa bakin katifar tana haki kamar wacce ta yi gasar tsare.

Juyowa ta yi ta ga ta ɓata daddumar, waro idanu ta yi ta rasa ya ma za ta yi kawai ta fashe da kuka, sautin kukan ta ne ya tayar da shi daga bacci ya buɗe idanuwansa ya sauke su a kan ya, da sauri ya tashi zaune ya matso kusa da ita ya ce "Me ya faru."

Sororo ta yi ta saki baki da hanci tana kallon shi jin yadda ya mata magana, amma da yake tana cikin yanayin da ba za ta iya wani dogon tunani ba sai ta nisa ta ce "Don Allah ka kaini banÉ—aki please."

Tashi ya yi ya ɗauke ta cak ya nufi banɗaki da ita sai kuka yake tana faɗin bayanta zai karya, aje ta ya yi har zai fita ya ga kamar wani abu a hannunsa ya yi sauran kai duban shi gare ta, fahimtar hakan ya sa ta kuma ɓarkewa da sabon kuka tana jin kamar ƙasa ta tsaye ta shige, ruwa ya sa ya wanke tas ita kuma duk ta yi zuru-zuru kamar ɓarawon da dubansa ta cika, yana gamawa ya fito ya bar ta a ciki ya rufe mata kofar.

Daddumar da ta ɓata ya ɗauke ya aje a gefe har zai juyo ya ga wata babbar kula irin ta gidan bikin nan, isa ya yi gaban kular ya buɗe ya ga ruwan zafi ne a ciki sai tururi yake , dube-dube ya soma yi can ya gano roba irin ta wanka sabuwa dal ya ɗauko ya zuba ruwan zafin rabin roba ya nufi banɗaki. A inda ya barta a nan ya dawo ya same ta sai ganin shi ta yi da ruwa yana tashin tururi ya aje mata bai ce da ita komai ba ya fita, ganin haka ya sa ta tashi a daddafe ta cire kayan jikinta da suka ɓaci ta shiga ruwan, da kyar ta daure ta zauna taba yarfa hannu har taji ruwan ya mata daidai ta jingina kanta da jikin bangon banɗakin tare da lumshe idanu, sai da ta ji ana kabbara Sallah ta tashi ta ƙarasa yin wanka sai lokacin ta tuna babu abin da za ta sa ta fita, ta tsaya tana karanta wasiƙar jaki. Ji ta yi an buɗe ƙofar an shigo ta yi saurin kallon ƙofar ta ga shi ne. Saurin kare jikinta ta yi tana rawar sanyi kamar mai jin zazzabi, shi kuma bai kalle ta ba ya iso inda take ya sa towel ɗin da ya shigo da shi ya naɗo ta ya ɗauke cak suka yo waje, idanu ta rufe ƙirjinta na mugun bugawa da sauri-sauri har ya aje ta akan katifar, komawa ya yi ciki ita kuma ganin haka ta yi saurin dauko duk abin da za ta yi amfani ta shiga sawa da sauri tana kallon ƙofar , har ta gama bai fito ba ta sulale ta kwanta tare lulluɓe jikinta da bargo ta yi mataƙau tana baza na Zomo kamar ɓarawon da ke shirin yin sata. Fitowa ya yi ya janyo dayar daddumar ya tada kabbara, a hankali ta ɗan buɗe ta ƙyalla idanu tana kallon shi cike da tarin tambayoyi a cikin zuciyarta, gabaɗaya lamarin Zaiyan yana son girman ƴar karamar masarrafarta, shin Zaiyan ɗin ne dai take gani a gaban ta yana Sallah kamar kowanni mai hankali da nutsuwa ko kuwa dai aljannun jikinsa ne suka sa shi yin hakan? Lumshe idanu ta yi ta sake buɗe su ta rasa wa za ta tara ta amayar wa da abin da yake cikinta ko za ta samu solution a zuciyarta, abin da ya mata jiya da dare shi yafi tsaya mata a rai ta ƙara jin tsoron shi ya kuma mamaye kowacce kafa ta jikinta, indai har kintacanta da daidai yake kintato mata samun lafiya ta bayyana a tattare da rijalun nata, yana yi mata wasu abubuwan irin na masu hankali ga shi yau har ruwan zafi ya kai mata banɗaki ya kuma dauko ta da ta gama, lalle in ba ƙarya idanuwanta suke gano mata ba Sallah cikakkiya take ganin Zaiyan yana gabatarwa kamar kowa..

Nisawa ta yi tunanukan da take gabaɗaya sun haddasa mata wani ciwon kai mai tsanani, tana jin shi ya gama ya zame a wajan ya kwanta ta yaye bargon ta tsura wa bayan sa idanu, yadda ya kwanta a takure sai ta ji ba daɗi ganin ita tana kan katifa shi kuma a ƙasa, a hankali ta tashi ta buɗe ledar da ta yo musu cefane ta ɗauko madarar ruwa ta buɗe hannu na rawa saboda yunwar da take ji ta kafa kai, sai da ta kwankwaɗe tas sannan ta isa wajan tukunyar abincin da ta dafa da dare ta sa cokali za ta ci a haka, tuna ba kyau yin hakan kar ta ɓata abincin sai ta miƙa hannu ta ɗauko wani plate ɗan madaidaici ta zuba taliyar da ta sandare ta yi sanyi ƙarara kamar ta kwana a freezer. Haka ta dinga turawa tana ci tana hawaye har taji ta ɗan rage yunwar ta janye ta tashi daga wajan, banɗaki ta shiga ta wanko bakinta ta ta dawo ta tsaya a kan shi tana ƙare wa kyakyawar surar jikinsa kallo. Yadda yake fitar da numfashi abin sai ya birge ta har ba ta san san da ta saki murmushi ba, bargon ta ɗauko ta rufa masa ita kuma ta yaye zanin gadon ta rufe jiki da shi da haka bacci ya dauke ta...

Sai wuraren karfe 11:00am ta farka duk jikinta a mace, banɗaki ta shiga ta gyara jikinta ta fito jin matan gidan suna ta hira, kallon inda ya kwanta ta yi ta ga ba kowa, da sauri ta kalli katifar sai ta gan shi a can karshen bango yana ta bacci, doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta saka hijabi ta fito waje. Maman Amal ta riƙe baki ta ce "Ke Jiddo wai lafiya kike kuwa? Kin san karfe nawa yanzu?"

Janyo kujare ta yi ta zauna a gefen Aisha maƙociyarsu tana murmushi ta ce "Wallahi bacci yau na sha sosai, kun tashi lafiya? Ina Mama take ne ban gan ta a nan ba?"

Maman Samira ta ce "Ai Ta Sakkwato É—azu ta gama wanke mu tas ta fita daga gidan, yau ko inda za ta je ba ta sanar da mu ba ta fita tana sababi."

Yar dariya ta yi ta ce "Mamana ba dai faÉ—a ba."

Hira suka ci gaba da yi ana ta shewa sai ga wata mata ta zo a mata lalle, nan Abir ta shiga ta ɗauko kayan ƙunshi ta shiga yi mata.

Yau gabaɗaya sun hallara ana ta tattaunawa kamar dai kullum su uku, Alhaji ya gyara zama ya ce "Yanzu dai abin da ya fi mu koma gidan boka, kun ga yanzu ana gaf da fara zaɓe kar mu bari Damisa ya ɓata mana shiri, sannan na ga kwana biyu Abdul ba ya kawo mana labarin komai game da wajan aikinsu shi ma mu sa a ƙara kama mana shi a hannu kar ya kuɓuce. "

Alhaji Mustapha ya yi kwafa dan shi gani yake ma ya fi kowa tsanar Damisa, a kufule ya juyo cikin faɗa-faɗa ya ce "Ni fa da za ku bi shawarata kawai daga can ma mu sa a kashe shi cikin ruwan sanyi, yanzu kuna ga mun bari an yi auren wannan sheɗaniyar yarinyar dan mu cika burinmu amma mun ƙasa cikawa, mun sa a bincika mana ita a kowacce Jaha amma shuru ba wanda ya ce mana ya gan ta, sanin kanku ne duk wani sirri namu Ibrahim ya tattara ya miƙa mata, idan har ta ga wannan sirrin me kuke tunani zai faru? Duk da shi wanda zai mata ja gabar mun shanye shi sai abin da muka ce zai yi, ya kamata mu tashi daga baccin asarar da muke mu nemo ta duk inda ta shiga a faɗin Nigeria. Ba na so wani abu ya kawo mana cikas a harkar siyasar nan tamu. "
Chapter 95 · 0% Book details