Sashe 53
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Iyayenmu 'yan ƙasar Niger ne amma ba nan suke da zama ba a nan Nigeria suke rayuwar su, mahafinmu ya kasance Jakadan yan Niger ne a nan Nigeria. Tun da aka yi wa Babanmu aure ya kwaso matarsa mai suna Aisha wadda a garin su ake kiran ta da Shatu suka dawo Kano da zama, auren su da shekara biyu ta haifi 'yan biyu mata wato ni da 'yar'uwata, ni ce Hassana ita ce Usaina. Shakara biyu da haihuwar mu ta sake haifo mace wadda ita ce mahifiyarka,. Mun taso cikin so da ƙaunar juna kanmu a haɗe yake. Haka muka yi ta girma muna karatu har muka kai mun gama secondary school, mu na shirin shiga jami'a ne wata ranar Juma'a Baba ya je Sallar Juma'a bai dawo da ƙafarsa ba sai gawar shi aka kawo gida, mun yi kuka kamar za mu shiɗe musamman Mama har suma ta yi, haka muna ji muna gani aka masa wanda aka kai shi gidansa na gaskiya, bayan an dawo aka ci gaba da karɓar gaisuwa har na tsayin kwana bakwai sannan aka bar mu daga mu sai Mama, sai wasu 'yan' uwanta mace da namiji su biyu da suka zo daga garin su Mama Maradi, sai kuma dangin Baba Kawu Sule da Ladidi,, .. Bayan kwana biyu suma suka shirya suka ce Mama ta haɗa komai nata mu tafi, amma sai Baba Malam da yake maƙocin mu ya ce sam kar su tafi da mu su bar mu mu gama karatu zai kula da rayuwar mu in sha Allah.
Ai kuwa Kawu Sule ya ce da mu zai tafi mu Maradi tun da zama ba wani zuwa muke ba sai ana wata sabgar kasancewar 'yan'uwan Baba ba son Mama suke ba, Yayan Mama ya fusata ya ce babu wanda ya isa ya raba mu da mahaifiyarmu tun da ba son mu suke ba ba za mu bi su ba su dinga azabtar da mu, da kyar Baba Malam ya raba su suna shirin yin dambe. Haka Kawu Sule ya zazzagi Mama tatas ya ce dama ita ce ta yi sanadin mutuwar shi, ba ta kula shi ba ya ce sai an raba gadon su an ba su tun da gidan nan mallakin Baba ne, haka Yayan Mama ya zuciya ya ce Baba Malam y raba gadon su ya ba su.. Haka aka raba gado dama Baba gida biyu gare shi wanda ake haya a ciki, da aka raba mu muka ci gidan da muke ciki, suma aka ba su na su inda suka ci gida daya. Sai da suka sayar da gidan aka ba su kudin su sannan suka bar Kano.
Washegari Yayan Mama suka shirya da ƙyar suka yarda suka bar mu a nan Mama na kuka ta rabu da 'yan'uwanta suka tafi gida, haka muka shiga Jami'a muna ta karatu ba ma kula kowa saboda kashedin da Mama ta yi mana, mun shiga aji na biyu a nan ne na haɗu da wani mai suna Ibrahim in da kai tsaye ya ce yana sona, amma na ce masa ya yi hakuri an hanani kula samari, amma yaƙi ji yake ta bibiya ta har sai da Hajara ta ce na haƙura na kula shi, ba dan na so ba nake kula shi...
Muna gama jami'a ya zo gidanmu inda Mama ta haÉ—a shi da Baba Malam ya ce aurena yake son yi, a lokacin shekarun mu 18 Hajara 16.
Baba Malam ya sanar da shi mu marayu ne Babanmu ya rasu in ya san yaudara ta ya zo yi kamar yadda wasu É—iyan masu ke yi wa É—iyan talakawa ya tafi, sai da ya rantse ya ce shi ba haka yake ba sona yake tsakani da Allah Baba Malam ya tambayi sunan iyayen shi, inda yake sanar masa sunan mahaifinsa Abdullahi Maitama. Jin sunan babban mutum Baba Malam ya cika da mamaki amma ya kawar ya ce ya turo magabatan sa ayi maganar gemu da gemu, cikin jin daÉ—i ya tafi gida ya sanar da mahaifinsa komai. Baban Ibrahim mutum ne mai karamci da sanin darajar talaka haka ma matarsa wato mahaifiyar Ibrahim, bayan sati da maganar suka zo gidanmu inda suka yi maganar komai Baba Malam da ya zame mana uba ya yi bacike akan Ibrahim, inda bai samu wata matsala daga É—abi'u ko halayensa ba hakan ya sa ya amince ya ba shi aurena aka sa bikin wata É—aya tak..
Mama ta tura wa dangin baba da danginta maganar an sa ranar bikina, ai kuwa takanas Kawu Sule ya zo har Kano ya ci mutumcin Mama ya ce bai aminci da auren nan ba ɗansa shi ne mijin da zan aura ba wani bare ba, na yi ta kuka saboda za a rabani da Ibrahim wanda nake tsananin so, Haka ya yi ta masifa ya ce kuma da mu zai tafi dama ai ya kyale mu ne mu gama jami'a aure zai mana a can garin su Baba da ɗiyan 'yan'uwan shi, muna ta kuka ya ce sai mun haɗa kayan mu mun bi sa ai kuwa Mama ta shaƙa ta nuna masa matsayin ta na uwa, ta ce masa bai isa ba ya tafi da mu tun da ba shi da mutumci, tun da Baban mu ya rasu ba su taba cewa bari su zo su ganmu ko su taimaka mana ba, ko mun shirya za mu sai ya ce kar mu zo sai ya ce mu zo, sai da ta masa tas sannan ta mayar da mu ɗaki ta ce ba inda za mu je. Sosai Kawu Sule ya ji zafin maganar da Mama ta faɗa masa haka ya tafi ya ce ranar biki sai sun zo, Mama ta ce in sun ga dama kar Allah ya sa su zo haka dai ranar muka wuni ba daɗi..
Lokacin biki na yi Kawu Sule da tawagar su suka zo har dangin Mama, an sha biki aka kai ni J. R. A inda dangin Baba ke zuzuta kyan gidan da Ibrahim ya gina min, bayan biki da kwana biyu Ƙanen mijina mai suna Kabir ya ga Hajara ya ce shi fa lalle a aura masa Hajara cikin satin nan, lokacin su Kawu Sule ba su tafi ba Daddyn su ya zo ya nemi auren Hajara a wajan Kawu Sule, ganin kuɗin da aka kawo na na gani ina so da sadaki Kawu Sule ya ruɗe ya ce ya bai wa Kabir Hajara yana son nan da kwana biyu a ɗaura aure sai su wuce maradi. Sosai Kabir ya yi murna bayan kwana biyu aka ɗaura auren su, washegari aka yi walima aka kai Hajara gidan Kabir, sosai Usaina ke kuka ganin sai ita kaɗai haka muka dinga rarrashin ta muna faɗa mata itama nata mijin na hanya..
Zaman auren mu a gidajenmu ba wata matsala, sai dai matsalar dangin miji yan uwan Daddyn su Ibrahim. Family Maitama ahali ne masu yawa suna da matasa da samari ba lefi, Grandma yaran ta biyar Ibrahim, Kabir, Sulaiman, Nabila, Yasira. Nabila da Yasira duk an musu aure da yaran su, Yasira na Madina da mijinta, Nabila na Gemerny da mijinta. So asalin Fulanin Yola ne, kasuwanci ya dawo da mahaifin Ibrahim Kano inda duk ya daura su kan kasuwancin, duk cikin su Ibrahim ya fi kwazo dan haka ya tara duniya sosai yana da kamfanin motoci a nan Kano, yana da shaguna a kwari na sayar ta atamfofi da duk wani nau'in kayan sakawa a jiki, yana hulɗa da manyan 'yan kasuwa na ƙasashen Africa.
Sulaiman shi ke kula da shagunan da ke kantin kwari, shi kuma Kabir ma'aikacin banki ne..
Ƙannen mazajenmu basa nuna mana tsangwama ko kaɗan hasali ma so da kauna suke nuna mana kamar yan uwansu na jini haka muke wasa da dariya, a ɓangaren dangin Daddy kuwa ba mai son mu yan'uwansa mata biyu da namiji ɗaya, matan su ke nuna basa son mu saboda sun so su haɗa yaransu aure da su Ibrahim su kuma sun ce basa so, namiji ne mai suna Alhaji Ishaq bai taba nuna mana rashin so ba sai matar shi da ɗiyan ta ke nuna mana tsani da kyara..
Shekarar mu ɗaya da aure na samu ciki, zo ku ga murna wajan Kabir har walima ya haɗa mana a gidan, haka na dinga samun kulawa ta ko'ina daga wajan mijina har Inna har cikina ya kai mawar haihuwa na ce zan tafi zaman haihuwa, ai kuwa Inna ta ce ba inda zan je ita za ta kula da ni. Ganin wannan karamci na Inna sai Mama ta haƙura ta bar ni a gidana, cikina na isa haihuwa na haifo yaro na namiji kyakkyawa fari tas mai kama da baban shi, ranar an sha murna da yamma aka taso ni muka dawo gida aka ci gaba da kulawa da ni, ranar suna yaro ya ci sunan Daddy aka sha hidima. Bayan suna Mama ta ce za ta ɗauke ni na yi wanka a gida amma Inna ta ce a bar ni a gidanta ita za kula da ni, sosai Mama ta ji daɗi ganin yadda surukar mu ke matukar son mu. Yarona na cika wata da haihuwa wata ranar Lahadi jikin shi ya ɗau zafi muka nufi Asibiti, ko da muka je ana ɗaura shi a gado ya rasu, na sha kuka kamar ba gobe saboda na kwallafa rai a kan yaron. Sai da na cika arba'in sannan aka dawo da ni gidana muka ci gaba da rayuwa..