← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 120

Sashe 54

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata biyu na samu wani cikin muna ta murna har ya kai wata biyar aka yi taro a familyn Maitama muka tafi wajan taron Ibrahim na lallaba ni. Ƙanwar Daddy na gani na ta dinga sababi wai an zo musu taron family da bare, ni kuma na yi shuru ina kawar da kaina gefe saboda bana son na mata rashin kunya a gaban mijina ya ji ba daɗi, Inna ce ta mata tatas ta ce kuma ko da wasa ta sake zagina sai ta rama min tun da abin nata ya wuce gona da iri. Bayan an gama taro na na ɗan zaga harabar gidan ina shan iska sai ji na yi an bangaje ni na yi saurin direwa Allah ya taimake ni ban fadi ba, juyowar da zan yi na ga Hajiya tana jijjiga jiki ta ce "Maiya mai farar ƙafa Wallahi mu dai Hauwa'u ta cuce mu da ta bari jinin mu ya auri dangin tsiya, kuma Wallahi ba ki isa ba ki haihu a wannan gidan kin yi kaɗan matuƙar ina raye, ba za mu haɗa jini da masu farar ƙafa ba dangin matsiyata."

Shuru na yi ina kallon ta har ta gama sannan na ce mata "Hajiya kenan, ai ke ba ki isa ki hanani haihuwa ba tun da ba ke kike ba da haihuwar ba Allah ke badawa, kuma ina ganin girman ki sosai saboda kina kanwar mahifin mijina, amma ba dan haka ba tsaf zan cire miki É—ankwali Wallahi ki kama girman ki na suruka ta."

Zagina ta dinga yi tana faɗa min baƙaƙen maganganu, ni kuma da na gaji da ji na koma ciki tare da ɓoye damuwata dan kar Inna ta gani ta tambaye ni dalili. Bayan mun koma gida cikin dare ciwon ciki mai tsanani ya mamaye ni, haka muka nufi Asibiti aka shigar da ni dakin taimakon gaggawa, gari na wayewa cikin jikina ya ɓare.. Bayan wata biyu da hakan labari mai daɗi ya zo mana, Usaina ta samu mijin aure itama a nan Kano yake, amma ba ɗan garin ba ne amma a nan aka haife shi kamar mu, sai da Baba Malam ya kira Kawu Sale ya sanar da shi Usaina an zo neman auren ta ko ya tura su can Maradin?

Kawu Sale ya ce kawai Baba Malam ya sa rana in dai ya yi bincike akan yaron, haka kuwa aka yi suna zuwa bayan kwana biyu aka sa biki nan da wata biyu Usaina murna take sosai, a lokacin kuma Mama na fama da ciwon zuciya yanayin kuzarin ta ya ragu amma dan kar ta tayar mana da hankali ta daure. Lokacin biki na yi aka yi shagali su Kawu Sule sun zo wannan karon sai nan-nan yake da mu har aka gama biki suka koma maradi.

Usaina shekarar ta daya da aure ta samu ciki muka shiga murna da farin ciki marar musaltuwa, kwatsam cikin Usaina na cika wata tara wata ranar Asabar wadda ta zame mana baƙar rana, gidan su Usaina ya kama da wuta ƙurmus komai ya ƙone na gidan har su gabadaya babu wanda aka iya ceto kasancewar gobarar dare ce, ranar kamar na yi hauka saboda wannan tashin hankali sai da muka kwana a asibiti daga ni har Hajara da Mama,. Bayan mun farfado aka musu zaman makoki na kwana bakwai aka musu addu'a, sosai na shiga damuwa na rashin Usainata mun shaƙu fiye da Hajara hakan ya sa na fi Hajara shi ga damuwa. Watan su biyu da mutuwa na kuma samun ciki wannan karon tare muka samu da Hajara, ban yi wata murna ba na dinga addu'a cikin na yin wata uku shi ma ya zube, Hajara kuwa lokacin haihuwa na yi ta haifo ɗanta namiji fari tas mai kama da ita wato kai. "

Ta É—an nisa ta ci gaba,

"Ranar suna aka mayar da sunan yarona na farko, haka na dinga kula da kai sai bacci yake rabani da kai, kana yin wata biyu na samu wani cikin ina ta tunani ban kuma kwallafa rai ba akan cikin ganin duk wanda na samu zubewa yake, har cikin ya kai watan haihuwa kullum fargaba nake, ranar Litinin ina jin naƙuda kaɗan-kaɗan cikin dare na yi wani mugun mafarki ina farkawa jini ya ɓalle min, kafin ma muje Asibiti na haifi yaro namiji bai zo da rai ba. Haka aka gyara ni Hajara take kula da ni dan yanzu Mama na fama da rashin lafiya sosai, ana tsaka da haka cikin dare Mama ta ce ga garin ku nan ta mutu ta bar mu. Mun sha kuka kamar ba gobe da kyar muka dawo kaiyacin mu ni da Hajara, Kawu Sule na kira amma bai dauka ba bai zo ba wajan mutuwar, har su dangin Mama babu wanda ya zo muka yi ta mamaki. Su Hajiya da suka zo gaisuwa suka dinga faɗa mana baƙaƙen maganganu Surukar mu ta musu cin mutumci ta kore su, bayan mutuwar Mama komai ya mana zafi duk da ba ci ko sha ko sutura muka rasa ba, kawai in muka tuna mu marayu ne gaba da baya babu wanda za mu yi shawara da shi duk da akwai surukar mu da take iya bakin ƙoƙarin ta wajan ɗebe mana kewar iyayenmu.. Watan ka uku da haihuwa Hajara ta kamu da cancer nono sai madara ake ba ka, ganin ban daɗe da haihuwa ba sai na yi wa mijina magana akan a kawo min kai na soma shayar da kai ganin yadda ka soma ramewa, bai musa ba ya nemi Daddyn ka a waya ya faɗa masa ganin ba ya gida amma bai same shi ba, sai kawai ya je a ɗauko min kai kana ta tsala kuka kaƙi ka sha madara, haka na wanke nonona na yi kunun alkama da duk abin da zai kawo ruwan nono dan ka samu ka sha. kwana uku da kawo ka ruwan nono ya zo na dinga shayar da kai, shi kuma mahaifin ka da ya neme ka sai Hajara ta ce ai kana wajena na dauke ka dan itama ban ce mata shayar da kai zan yi ba iya mijina da Inna na faɗawa.. Haka ka yi ta girma har na yaye ka, zuwa lokacin Hajara ta warke tas sai tafiya ta sami Kabir suka bar min kai suka yi tafiyar su Dubai, sai da suka cika shekara hudu ciwon ƙafa ya kama Hajara dole suka dawo Nigeria, ganin ta a wannan halin hankalina ya tashi na shiga nema mata magani ni da Kabir duk inda muka ji mai magani sai mun je. Sai da ta kusa shekara a cikin wannan yanayin da yamma daga shiga toilet sai fiddo gawar ta aka yi, na yi kuka na rasa yadda zan yi na dawo ni kaɗai ina ji ina gani aka yi mata wanka aka kai ta makwancinta, na ci gaba da kulawa da kai Kabir kuma ya shiga damuwa na rashin matarsa, Hajara na cika wata biyar da mutuwa Hajiya ta zo gidan ta ce lalle sai Kabir ya yi aure ba zai zauna ba mata ba tun da ƙanen shi Sulaiman zai auri ƴar ɗan'uwansu shi za ta aura masa Baraka yar wajan ta, Sam ya nuna ba ya son Bakara saboda ta mugun raina shi dan a lokacin ma tana ƙasar waje tana karatu, amma Hajiya ta je ta ƙulla makircin ta har da kukan wai na asirce Kabir so nake na je Maradi na kawo wata a dangina na aura masa. Haka ta dage sai da ta shayo kan baban su Kabir ya ce ya auri Baraka aka sa bikin lokaci ɗaya da na Sulaiman, haka aka yi ta hidima ranar biki aka gama ni dai ina cikin jima min rashin ƙanwata ban wani yi walwala ba, hakan ya sa dangin su Daddy ke zagina wai kishi nake taya gawa, raina ya ɓaci zuciyata ta sosu na yi ta kuka na dawo gida..

Bayan bikin su gabaɗaya muka tashi daga Kano muka koma babban gidan Maitama Family wanda Daddy ya gina amma ya ce ba zai bar Kano ba tun da part uku ne mu mu zauna kawai, haka muka haɗa komai namu muka dawo Yola da zama na sha kuka da nake gidan Baba Malam zan masa Sallama. Bayan mun koma na zama saniyar ware su Farida ba sa ganina da mutumci kullum rashin kunya suke min, amma haka nake dannewa na rabu da su na ci gaba da kula da kai dan a lokacin na fidda rai da haihuwa. Sai da Farida ta haifi yara biyu Salim da Yasmin, Baraka ta haifi Khairat sannan na samu wani cikin, a lokacin kana da shekara tara ka dinga murna kaima za ka samu kanwa. Cikina na kai wa watan haihuwa na haifi yata mace wato ta ci sunan Inna *Hauwa'u Maijidda* wa ke Abir, wadda na cire rai za ta taka ƙasa, tun da aka haife ta ta tashi da farin jini Kabir har Office yake zuwa da ita, shi kuma Sulaiman sai ya ga ta yi bacci ko tana kuka yake kawo min ita, komai suka samu mai sunan Innar su za su kai wa. Wannan abu na kona wa Farida da Baraka rai suka ɗauki karan tsana suka ɗaura mata, ko wajan su Salim ta je yin wasa koro ta suke su mata duka ta sha kukan ta ta more, in kuma kana nan za ka goya ta ku yi ta wasa. Shekarar ta shida wata rana tana fita zuwa wajan su Salim ta faɗi a ƙasa sai kawai ta dinga yin abu kamar mai farfaɗiya, hankali a tashe muka nufi Asibiti aka soma ba ta taimakon gaggawa.....

_Taku har kullum Maman Nusaiba._
[6/20, 7:55 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~

Littafin A HAKA NAKE SON SHI na kuɗi ne, idan har kin gan shi a waje to na sata ne kika karanta. Ga du mai buƙatar shi sai ya neme ni ta whatsapp number na 👇🏻

+966577675904

Shafi na (27)
Chapter 54 · 0% Book details