Sashe 76
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya Alhaji Mustapha ya yi ya ce "Ƴar jakar uba har wani umarni take ba ka dan ta samu waje? Ka rabu da ita ni zan mata bayani ko da ka wuce awa ɗaya ballantana ma minti talatin ya wadatar mu gama maganar. " Ya faɗa yana kallon Jarmai da yake wani hawa kamar fulawa shi ga suriki. Gyada kai ya yi hakan ya sa Alhaji Mustapha ya ce "Dama mu abin da muke so ba wani dogon turanci za mu tsaya yi ba, ina son ka amso mana ma'adanar bayanai a hannun ƙanwarka Abir, sannan da wata takarda wanda sun jima a tare da ita, so muke duk ka amso mana su saboda namu ne ba na mahaifinta ba." Ya faɗa yana daure fuska irin ba wasa din nan..
Sauke ƙafa Abdul ya yi da ɗaura ɗaya kan ɗaya ya nisa ya ce "Lalle sai na kakkaya Baby kat, me ya kai ta ɗaukar muku kaya? Ko dai sata ta fara ne ban sani ba?" Ya faɗa yana ƙara jin tsanar ta na ƙara ruruwa a zuciyarsa, ji yake zai iya ɗaura bindiga a kanta ya ɗana mata kunama ya harbe ta.. Alamar jinjina Jarmai ya yi wa Alhaji Mustapha a ɓoye, ɗan jim ya yi sannan ya ce "Ka bari kawai Abdul karambanin yarinyar nan ne ya sa ta buɗe kayan mahaifinta ta ɗauka duk da ta san ba na babanta ba ne amma ta dauke shi."
Kwafa Abdul ya yi ya miƙe tsaye ya ce. "Ka yi haƙuri Dad zan dawo maka da kayanka gobe ko jibi zan je gidan nata ta ba ni na kawo ma." Ya faɗa yana wucewa bai ma tsaya ya saurari mai zai faɗa masa ba..
Dariya suka sa suna tafawa shi da Jarmai, sai da ya jima da fita sannan Jarmai ya ce "Amma ai ba mu tambaye shi takardun ba."
"kwantar da hankali Jarmai ai a hankali za muke amso komai har mu gama mu aika shegu lahira." Dariya suka kuma sawa suna tafawa...
_NIGER_
zaune suke a harabar gidan daga can gefen part ɗin Mamma, Ikilima ce da Iman sai masu Hidima suna ta musu fifita su kuma suna hira. Ikilima ta miƙe ta ce tana zuwa za ta dauko wani abu ta wuce.
Kamar daga sama ta ga an tsaya a gaban su, ɗago kai Iman ta yi ta kalle ta tun daga kan ƙafafu har zuwa fuskarta da take a daure, sosai ta ji gaban ta ya faɗi amma ta dake ta ce "Malama ba ki iya Sallama ba ne?"
Wani irin Abu Fauziya ta ji ya zo mata wuya, ita wannan Æ´ar ficikar yarinyar za take ce mata ba ta iya sallama ba? A fusace ta ce "Ai na ga nan É—in gidan Ubanki ne."
Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarci zuciyar Iman jin an zagar mata uba, kallon banza ta watsa mata ba ta ce mata komai ta kawar da kai, hakan da ta yi ba ƙaramin fusata Fauziya ya yi ba ta ƙunduma mata ashar ta kori hadiman duk suka bar wajan daga ita sai ita. Miƙewa tsam Iman ta yi ta sa takalmi tana ƙoƙarin wucewa ta ji an damƙo ta, da sauri ta kalle ta ta sa hannu ta kwace tana huci gaban ta sai dukan uku-uku yake na tsoron Fauziya amma a fili ta dake ta nuna babu wannan tsoron. Ɗagowa ta yi da nufin yin magana ta ji saukar mari tas! Tas! Tas! A kumatunta, a firgice ta ɗago ta kuma ƙara mata wani, ƙara Iman ta kwalla ƙara jin zafin marin ya gama mata jiki..
Suhal da ke ƙoƙarin isowa wajan ya ji ƙaran Iman hakan ya sa ya tako da hanzari dan ya ga meke faruwa da ita, a kan idanuwansa Fauziya ta yi wa Iman mari na hudu kamar wani zaki sai ga shi a gaban su yana huci.
Da sauri Fauziya ta saki Iman tana zaro idanu tuni jikinta ya hau rawa tun kafin ma ya ce mata komai, Iman da ta gigice ta yi baya za ta faɗi ya yi saurin taro ta ta faɗo kan shi. Jin ƙamshin turaren sa ya sa ta saki kuka tana ƙanƙame shi ya ƙara shigar da ita yana cewa "Yi shuru gani na zo yau sai na ga wanda ya daure mata gindi har ta sa hannu ta dakar min ke.."
Da sauri Fauziya ta juya za ta gudu ya daka tsawa tare da sa ƙafa ya taɗe ta faɗi tim, Ikilima da ta dawo ta ga abin da yake faruwa sai ta amshe Iman daga hannunsa tana cewa "Wallahi Yaya in ba ka rama wa Iman abin da ta mata ba ba ka cika mijin kwarai ba." Tana faɗin haka ta ja Iman suka koma gefe. Kan ta ya yi gadan-gadan yana zare bal ɗin jikinsa cikin tsananin ɓacin rai....
😂Iyar Haidar, Mom Islam ku zo ku raba faɗa 🙃
_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~
Shafi na (37)
Yana isa bai tsaya yin komai ba ya dinga zabga mata bal ɗin ba ji ba gani, ihu take tana faɗin "Waiyo don Allah ka yi haƙuri Yaya Suhal ba zan sake shiga harkar ta ba." A mugun fusace ya yi bol da ita ta saki wani irin ƙara na azaba saboda da yadda ya daki kadon bayanta da ƙafa, damkar ta ya yi yana daka mata tsawa sai ga ta ta tsaya ƙyam akan ƙafafunta sai rawar jiki take. Wani irin kallo yake bin ta da shi mai cike da tsantsar tsana yana huci kamar namijin zaki, jefar da bal ɗin ya yi ya nuna ta hannu ya ce "Wallahi ko da wasa na sake ji ko gani kin harari matata sai na canja miki suffar jiki, ke yanzu ko cewa aka yi ki ɗaga wannan banzan hannun naki ki mari matata sai ki yi?" Kwafa ya yi ya juyo ya kalli su Iman da har yanzu kuka take tana rakuɓe a jikin Ikilima, tsaki ya ja ya ce "Yadda kika daga hannu kika dake ta sai ta rama." Ya faɗa yana nufar Ikilima ya kamo ta ya tsayar da ita a gaban Fauziya. Idanu Iman ta daga ganin Fauziya ya sa ta kwalla ƙara ta yi saurin faɗawa jikin Suhal tana ci gaba da kuka ta ce. "Yaya ni ka ɗaukeni mu tafi wajan Mamma wannan muguwa ce." Ta faɗa tana ƙanƙame shi.
ÆŠago da fuskarta ya yi ya sa É—ayan hannun ya raba ta da jikinsa, cikin ba da umarni ya ce "My Iman É—ago ki kalle ni da kyau, yadda ta mareki kema ki rama yanzun nan."
Saurin komawa jikinsa ta yi tana girgiza kai ta ce "A'a ni dai mu tafi tun da ka rama min." Ta faɗa tana dira ƙafa. Kallon banza ya watsa mata ta sunkuyar da kai tana rawar jiki, wutar tsanar Iman na ƙara ruruwa a zuciyarta ta kuma ci alwashin rama duk abin da Suhal ya mata a kan ta..
"Maza ki wuce an jima ki saurari abin zai biyo baya shashasha jaka aladiya wadda kanta babu komai sai tarin iskaci da wulaƙanci."
Sim-sim ta wuce tana dafe bayanta da yake mata azabar ciwo, ganin ta tafi ya ɗauke ta cak ya nufi ciki da ita yana jin haushin abin da aka mata.. Duk abin da ya faru akan idanun Jakadiya har sai da ta ga sun tafi sannan itama ta tafi da sauri har tana haɗawa da tuntuɓe.
Ko da suka shiga daret É—akinsu ya nufa da ita yana jera mata sannu har suka isa ciki, aje ta ya yi ya shiga toilet ya haÉ—a mata ruwan zafi sannan ya fito ya same ta kwance kan capet, da sauri ya iso ya tsugunna ya kai hannu ya shafo fuskarta da satin yatsun Fauziya suka kwanta a kan kyakkyawar kumatunta..
Lumshe idanu ta yi tana jin yana kiran sunan ta amma ta yi shuru kamar mai bacci. Ganin haka Suhal ya tankwashe ƙafafu ya ɗago da ita ya kwantar da ita a kan cinyarsa tare da sunkuyo da kansa ya soma hura mata iskar bakinsa. Turo baki ta yi tana buɗe idanuwanta akan kyakywar fuskarsa da take a dame duk ya shiga yanayi, shagala ta yi da kallon shi tana yin raurau da idanu ya riƙe hannunta cikin sanyin murya ya ce "Am so sorry my Beauty in sha Allah ta yi na farko ta yi na karshe kin ji." Ya faɗa yana murza hannunta cikin tausayawa. Kwaɓe fuska ta yi ta kai hannu ta zagaye bayansa jin wani sanyi na shigar ta, dankwalin kanta ya saɓule ya shiga shafa lallausan gashinta baƙi siɗik, lumshe idanu ta yi tana ƙara yin luf jin wani ɗumi mai daɗi na shigarta.. Hannu ya kai ya taɓa wuyanta ya ji shi rau ya yi saurin ɗaukewa yana ɗago da ita ya ce. "My Iman ba ki da lafiya ne? " Ya faɗa yana tallafo fuskarta ya tsare ta da kallo. Hawaye ne suka silalo mata ta buɗe idanu cikin rawar sanyi ta ce "Ya.. Yaya ka rufeni sanyi nake ji har kaina ciwo yake." Ta faɗa tana kwantar da kanta a ƙirjinsa ganin yaƙi sakar mata fuska ballantana ta koma ta kwanta. Nisawa ya yi yana bubbuga bayanta ganin ta soma mutsu-mutsu, juyin da take ne ya ƙaru hakan ya sa ya ce "My Iman bayan zazzaɓi da ciwon kan ina yake miki ciwo? Sannan tun yaushe kike jin zazzaɓi ba ki sanar da ni ba?" Ya faɗa a ruɗe.
Kuka ta sa masa tana yarfa hannu jin ciwon na ƙaruwa ta tashi zaune ba shiri ta dafe cikinta, juyar da kai ta yi suka haɗa idanu ta ce "Yayaaa." Ta ja sunan tana mayar da numfashi. Amsawa ya yi yana riƙe ta sai tambayar ta yake ina ne ke mata ciwo, sai da ta yunƙura za ta tashi ta ji cikinta ya murɗa ta kwashi salati tana yarfa hannu cikin azabar ciwo ta ce "Yaya cikina ciwo, waiyo zan mutu Yaya ka kaini wajan Umma na ni dai." Ta faɗa a gigice.