← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 120

Sashe 42

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jan motar ya yi suka nufi Asibitin da aka kai Zaiyan, suna isa suka fito suka nufi ɓangaren da yake. A kwance suka same shi yana bacci, Suhal da yake danna waya ya ɗago ya kalli Zaiyan, a razane ya ja da baya yana nuna shi ya yi saurin isowa gaban gadon y shafa fuskar Zaiyan, wani irin faɗuwa gaban shi ke yi ya ƙura masa idanu. Abir ta yi murmushi ta ce "Ka gani ko Ya Suhal? Ai na ce ma dama abu kaɗan ne ya bambanta ku."

Gyaɗa kai ya yi yana janye idanuwansa daga kan fuskar Zaiyan ya ce "Tabbas na gani Princess, Allah mai halitta sai ya yo mai kamar ka sak sai dai hali ko wani abu ya ɗan bambanta ku." Ya faɗa yana komawa bakin ƙofa y ci gaba da kallon shi.

Zai sake yin magana suka ji an buɗe ƙofar an shigo, da sauri Suhal ya juya dan ya ga waye ya shigo.

A daddafe ta rufo ƙofar tana haki, Suhal y dube ta ya ce " Baiwar Allah lafiya kika shigo nan? Ko dai kin manta ɗakin jinyar ki ne?"

Jin surutu a bakin ƙofar ta ƙaraso kusa da Suhal ta soma magana tana rarrabewa, "D.. Dan Al.. Allah.. K.. Kar ku ce ina nan, za su kashe ni." Tana ƙarasa maganar ta yi baya luu ta zuba a ƙasa. A ruɗe suka yo kan ta, Abir ta janye gashin gashin da ya rufe mata fuska, a razane Suhal ya kalle ta cikin kiɗima ya ce "Sajida...

Taku har kullum Maman Nusy.

[10/23, 10:20 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~

+966577675904.

Shafi na (22)

Kallon shi Abir ta yi jin abin da ya faɗa, ɗago da ita ta yi ta dubi Suhal da ya ƙame a tsaye kamar soja ta ce "Ya Suhal ka san ta ne?" Girgiza kai ya yi ya ƙaraso kusa da ita ya sa hannu ya amshe ta daga hannun Abir, hawaye masu ɗumi ne suka silalo daga kwarmin idanuwansa ya ɗiga kan fuskarta, huci yake yana ƙara rungume ta kamar wani zai kwace ta daga gare shi ya ɗago ya kalli Abir da Abdul da suka yi ƙiƙam suka kallon ikon Allah ya ce "Princess na san ta ita ɗin matata ce tun shekaru biyar da suka wuce." Ya faɗa yana shafa bayan ta, jin ya taɓo danshi a gefen cikinta ya yi saurin kallon hannun, jini ya gani ya waro idanu ya sake kallon gefen cikin sai lokacin ya ga jini duk ya jiƙa mata doguwar rigar Asibitin da ke jikinta, a ruɗe ya ce "Sajida waye ya miki haka." Dogon numfashi ta ja tana juya kan ta cikin tsananin ciwo ta soma buɗe idanu, ganin fuskar wanda yake riƙe ta ita ya sa ta ƙara buɗe idanun tana yatsina fuska, ɗago da ita ya yi dan ta kalle shi da kyau yana goge hawaye ya jingina ta da gefen kafaɗarsa. A sanyaye ta ce "Suhal." Gyaɗa mata kai ya yi ya ce "E nine, Sajida ashe kina raye ?" Fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikinshi ya yi saurin ɗago ta yana girgiza mata kai ya ce "Tell me Sajida duk tsayin shakarun nan a ina kike? Kuma waye ya kawo ki Asibiti?" Su dai su Abir sun zama 'yan kallo dan haka ta ƙaraso gadon da Zaiyan yake kwance ta zauna a gefe ta rafka tagumi tana kallon Sajida da jini ya ɓata mata riga, gabaɗaya ji ta yi ta ba ta tausayi ta goge hawayen da suka zubo mata tana sauke ajiyar zuciya.

Ganin taƙi yin magana Abdul ya zaro wayarsa daga aljihu ya kira Likita, bayan ya ɗaga ya sheda masa ya zo ɗakin da Zaiyan ke ciki sun zo ya amsa da to sannan ya kashe kiran.. Bai fi minti ɗaya ba sai ga shi ya buɗe ƙofar ya shigo bakinshi ɗauke da sallama suka amsa, zabura Sajida ta yi Suhal ya shigar da ita jikinsa ganin yadda ta firgice ya ce "Likita ne fa."

Kallon ta Likita yake yi cike da mamaki har ya kasa ɓoyewa ya ce "Wannan ba majinyaciyar mu ba ce mai matsalar ƙwaƙwalwa? Me ya kawo ta nan ɗakin?"

Ƙara riƙe Suhal ta yi tana gunjin kuka ta ce "Wallahi ni ba bahaukaciya ba ce da hankali na aka mayar da ni mai taɓin hankali."

Wani irin kallo Suhal yake yi wa likitan wanda ya sa 'yan hanjin Likita kaɗawa, shafa kanta ya yi ya ce "Ai ko ma waye ya mayar da ke mahaukaciya sai na gano shi na ɗauki mummunan mataki a kan shi, ashe duk tsayin lokacin nan kina raye muke neman ki har mun gaji mun miki sadaka mun ɗauka kin mutu ashe kina nan a raye? Kai kuma na dawo kanka." Ya nuna likita cikin zallar ɓacin rai ya ci gaba "Yau sai ka faɗa min wanda ya kawo muku ita a zaman mahaukaciya." Ya faɗa a zafafe yana nuna shi da yatsa..

Ganin abin zai tada cecekuce Abdul ya ce "Ka kwantar da hankalin ka mana Suhal, ka bari yanzu tukun ya duba lafiyarta in yaso sai ayi maganar."

"Ba dai a Asibitin nan ba za a duba ta? Ni zan duba ta da kaina."

Da mamaki Abdul ya kalle shi ya ce "To kai likita ne dama?"

"Yes I'm doctor." Ya faɗa yana huci ya sake cewa "Zan iya tafiya da ita masauki na akwai kayan aikina a cikin kayana zan mata komai." Ya faɗa yana tashi tsaye ya miƙar da ita ta ƙwalla ƙara tana dafe mararta tana juya kai cikin azaba. Da sauri Abir ta sauko ta iso wajan su ta kamo hannun Sajida ta dubi Suhal da ya riƙe ta ta ce " Ya Suhal ka bari please a duba ta a nan, ka ga fa jini a jikinta bai fasa zuba ba in ka ce sai ka je masaukin ka to za ka iya rasa ta gabaɗaya."

Ajiyar zuciya ya sauke ya raba ta da jikinsa Abir ta kama ta ta dubi Likita ta ce "Likita muje ka kaimu inda za a duba ta." Jiki a sanyaye Likita ya ce "Ok muje to."

Har zai bi bayan su Abdul ya hana shi ya bi bayan su, shi kan shi so yake ya san wace ce Sajidar nan da Suhal ya ƙidime da ganin ta kuma ya ce wai matarsa ce da haka dai ya iso bakin ƙofar ɗakin da aka saka ta Abir ma na tsaye a wajan tana safa da marwa, kusan minti 30 ba su fito ba Abdul ya ce ta koma ta kawo Suhal su za su tsaya da shi ita kuma ta zauna a wajan Zaiyan, to ta ce ta koma ɗakin ta same shi yana kaiwa da komowa ganin ta ya sa ya soma tambayar ta.

"Princess ya jikin nata."

Sauke hannayenta ta yi daga ƙirji ta ce "Tukunna dai, Yaya ya ce na kaika ku tsaya a can ni na zauna a nan.".

Da sauri ya ce "To.. TO mu je ki kaini."

Jagora ta masa har bakin ƙofar ta nufo ɗakin za ta koma suka yi kiciɓus da Hafsat, riƙe baki Hafsat ta yi tana ƴar dariya ta ce "Su Baby manyan gari, wa kika kawo Asibiti?" Murmushi ta yi tana ɗan yarfa hannu ta ce "Babu kowa kawai dai mun zo duba wani friend ɗin Yaya ne."

Jin abin da ta faɗa ya sa Hafsat kallon bayan Abir, ganin ba ta ga Abdul ɗin ba sai ta harare ta ta ce "Kai ƙawata ban san ki da ƙarya ba, ina Yaya Abdul ɗin yake?"

Ganin tana ɓata mata lokaci ya sa ta ce "Ya tafi wajan mara lafiyar ni kin ga sai an jima tafi abin ki zan neme ki a waya in na koma gida." Tana faɗin haka ta wuce ta bar Hafsat tsaye a wajan cikin son ganin Abdul, amma ba yadda ta iya dole ta tafi..

Tana isa ta samu ya soma buɗe idanunsa, da sauri ta matso jikin gadon tana murmushi. Yana buɗe idanu da ita ya fara yin arba ya mayar ya lumshe ya sake buɗe su a kan ta, ƙoƙarin tashi ya soma yi ta taimaka masa ya tashi ta kara masa pilo a bayan shi ya jingina da gadon, a hankali ya ɗago ya kalle ta ya sakar mata da kyakkyawa murmushi yana miƙa mata hannunsa. Kama hannun ta yi tana mayar masa da martanin murmushin ta ce "Sannu Zaiyan ya jikin naka? "

Murmushi mai sauti ya sake yi a karo na biyu, sai da ya haɗiyi yawu sannan ya soma magana da muryarsa mai mata daɗi in tana sauraron shi a duk lokacin da yake magana. "Anty a gidana kike?" Ya faɗa yana tattaɓa fuskarta. Ƴar dariya ta yi cike da jin daɗin ya tashi ta sauke hannunsa daga kan fuskarta ta kai hannu za ta gyara masa rigarshi da ta dan saɓule daga wuya farar fatarshi ta bayyana, tana ɗaura hannunta a kan shi ta ji wani chok ya kama ta ta yi saurin ɗauke hannun tana sauke numfashi, a hankali ta dube shi ta ga ita yake kallo ta sakar masa murmushi ta ce "Ka yi kewa ta ko?"

Gyaɗa mata kai ya yi yana yin dariya, za ta sake magana ta ga ya zare allurar ƙarin da ake masa ya zauna a tsakiyar gadon ya ci gaba da kallon ta. Cike da mamaki take kallon shi, ta ce "Me ya sa ka cire ƙarin ruwan?"

"Ba ya buƙatar hakan dan cutar da shi ake ba wai ruwan ba ne ake sa masa guba ce."

A ruɗe Abir ta ɗago jin wata murya a gefen Zaiyan, matar da ta gani ranar nan ta gani ta bayyana cikin shigar ta ta fararen kaya. Wannan karon Abir ba ta ji tsoro ba ganin an ɗauke wutar ɗakin, ajiyar zuciya ta sauke ta lalibo Zaiyan ta kama hannunsa ta riƙe gam, hasken jikin matar shi ne ya haske ɗakin kamar an haska fitila. A ɗarare Abir ta ce "Baiwar Allah wai ke ɗin wace ce?"
Chapter 42 · 0% Book details