← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 120

Sashe 89

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Sannu kin ji Jiddo Ubangiji ya ba wa mijinki lafiya, ki daina kuka kin ji yata na miki alƙawarin zan zame miki uwa duk abin da kike so ki tambayeni zan miki shi ko min tsadar shi, sannan ki adana duk abin da kika san yana da mahimmanci karki yi sake da shi. " Sosai zuciyar Abir ta sanyaya ta rungume Ta Sakkwato tana mata godiya, haka suka ci gaba da hira tana ƙara kwantar mata da hankali..

Zaiyan ganin Abir ba ta É—akin sai ya tashi ya fito waje, bai ga kowa ba sai Maman Samira da take wanki, juyawa ya yi zai koma É—aki sai kuma ya nufi kofar fita daga gidan. Maman Samira na ganin shi amma tsoron shi ya sa ta kasa cewa komai ha ya fice a gidan, ganin haka ta yi saurin komawa dakinta dan kar ma ya dawo ya same ta a waje..

Abir ta fito daga dakin Ta Sakkwato ta shige dakinta ta ga wayam, bandaki ta leka ta ga nan ma baya nan, hankali a tashe ta fito tsakar gidan ta kwadawa Ta Sakkwato kira ta fito da sauri har tana tuntuɓe.

"Minana ya hwaru kike kira hakan ga?"

Fashewa ta yi da kuka ta ce. "Zaiyan ba ya É—aki kila da bai ganni ba ya fita waje, bari na leka kofar gida ko zan gan shi."

Kafin Ta Sakkwato ta ba ta amsa ta janyo Hijabinta da ke kan igiyar shanya ta nufi waje da gudu, Ta Sakkwato ta ce "Bari mu gani kila ta samu shi a kofar gida."

Tana fita ta leka ba ta gan shi ta ƙara shiga tashin hankali, Layin nasu ta dinga bi tana tambayar duk wanda ta gani bai ga Zaiyan ba? Wasu su ce ba su ma san waye wani Zaiyan ba, ta kusa shan kwana hannunta a ka tana rusa kuka ta ji ƙaran mota a bayan ta, saurin matsawa ta yi ta ji an yi sama da ita cak a tsilla ta cikin motar. Ihu take tana bige-bige karshe ma suka shaƙa mata fauda ta yi shuru suka ja motar a guje suka bar Layin.....

_Maman Nusaiba ce_

[11/26, 12:55 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na (44)

Kusan minti ashirin da fitar Abir Ta Sakkwato ta ga ba ta dawo ba, saurin janyo mayafinta ta yi ta nufi waje ta gani ko lafiya ba ta dawo ba. Wayam ta gani babu ita babu alamar ta, hankali a tashi ta nufi ƙofar gidan maƙotan su tana tafa hannu sai sallallami take. Da sallama ta shiga gidan inda ta samu matar gidan na shirin fita, kallon ta matar ta yi cike da mamaki ganin yadda ta shigo, matsowa kusa da ita ta yi ta ce "Ta Sakkwato lafiya?"

A ruɗe ta ce. "Ina fa lafiya Aisha, yarinyar ga da take haya a gidanmu ce ta fito neman mijin ƙofar gida, to ganin shuru ba ta dawo ba shi ne na bi bayan ta na ga ba kowa, na shigo nan ne ko ta zo neman mijinta."

Riƙe baki Aisha ta yi sai kuma ta dafe ƙirji tana salati, "Subhanallahi! To ina ta shiga haka? Amma kin san dai ai magidanci ba zai shigo min gida ba ina matar aure ko? Ina tunanin dai ko ya fita kasuwa ne."

Dafe kai Ta Sakkwato ta yi, a sanyaye ta ce "Ai mijin nata yana da taɓin hankali kaɗan, bari na tafi tun da ba wanda ya shigo a cikin su." Tana faɗin haka ta yi saurin wucewa tana surutai..

Sake da baki Aisha ke bin bayan Ta Sakkwato da kallo, sai nanata kalamar ba shi da hankali take cike da al'ajabi, dan ita a yanda ta ji kawai dai an ce mata wata matashiyar mace ta kama haya a gidan da mijinta kamar Balarabe. Jinjina kai ta yi ta fito ta yi inda za ta je..

Ta Sakkwato na fitowa ta hango Zaiyan tsaye da shi da ɗayan maƙocin su ya ruƙo hannunsa yana jan shi, da hanzari ta iso garesu tana huci ta kalli Zaiyan ta ce "Ina Jiddo ɗin?" Ta faɗa tana kama hannunsa za ta wuce da shi ta ma manta ta tambayi maƙocin nasu.

"Ta Sakkwato wannan É—in daga ina yake? Ko kin san shi ne?"

Juyowa ta yi ta dawo ta ce " Malam Iro ba ka gan shi tare da wata yar baƙar yarinya ba?"

Girgiza kai Malam Iro ya yi cike da son ƙarin bayani dan shi bai san su a Unguwar ba, nisawa ya yi ya ce "Baƙi ne kika yi daga garinku? Ni ban gan shi da kowa ba, hasali ba yarona Umar ne ya tare yana ce masa wai ina Anty? To sai ya kirani lokacin na shigo gida ko zama ban yi ba naji kiran shi yana daga ƙofar gida, to da na zo na gansu nake tambayar shi ina yake nema? Sai ya ce min shi Anty yake nema. Umar ya ce min ai yana zaune a ƙofar gida ya gan shi ya fito daga gidanku shi ne na zo na kawo shi, dan na lura kamar ba shi lafiya." Ya faɗa yana kallon Zaiyan da yaje ta murza idanu.

"E ba shi da lafiya, matarsa ta fito nemansa yanzu ni ban san ina take ba." Tana gama faÉ—in haka ta ja hannunsa ganin ya fara kuka suka wuce gida..

Su Maman Amal sun yi cirko-cirko suna jiran dawowar su sai ganin su suka yi su biyu sun shigo, Gamboliya ya ce "Ta Sakkwato yo ina Æ´ar shawalwalar take.?"

Zaunar da Zaiyan ta yi tana rarrashinsa har ya daina kukan amma bai daina faɗin "Ina Anty take? Baba ne ya zo ya sace ta ko?" Haka yake ta faɗa duk suka zuba masa ido, ganin ba zai kyale ba Ta Sakkwato ta dauko masa abinci ta sa masa a gaban shi, ƙin kallon abincin ya yi ya lafe a jikin bango ya yi shuru yana kallon gefe ɗaya. Ganin ya kyale Ta Sakkwato ta shiga ɗaki ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki, shi ma salati ya dinga yi ya ce ta kai maganar wajan yan sanda ko an dace su samo ta, ba ta musa ba ta ce Ladidi su tsare Zaiyan kar su kuskura su bari ya fita suka amsa da to sannan ta fita...

Tun da suka ɗauke ta suke ta sharara gudu ba ji ba gani, sai da suka yi tafiyar awa ɗaya da rabi suka yi hon a wani babban get ruwan gold, wangale musu ƙofa aka yi suka sa kai ciki da sauri. Suna gama packing daidai lokacin ta buɗe idanuwanta ta gan ta a cikin mota, firgita ta yi za ta fito ta ji ƙafarta a ɗaure, kallon ƙafar ta yi sai ta ga an buɗe ƙofar, wani rikakken namiji ne ya kunce mata ɗaurin ya mata alama da hannu ta fito daga ciki. Ba muso ta fito tana rarraba ido ganin ta a wani tanfatsetsan gida, murya ta ji daga gefen ta, "Madam muje."

Duk inda suka nuna mata nan take bi hankali a tashe ita ba kanta take tausayawa ba mijinta wanda ba kowa zai iya zama da shi ba sai ita da ta zame masa dolen sa shi abin da ya fi damun ta.

Wata ƙofa suka bi kamar za su zaga bayan gidan sai ga su a bakin wata kofar ƴar madaidaiciya, dam! Gaban ta ya faɗi nan da nan jikinta ya dauki rawa tuno da abin da ya faru da ita a baya, sai da aka ce ta shiga sannan ta ɗaga ƙafa da kyar ta sa kai ciki. Ganin su ta yi a wani babban palo wanda yake Kusan cike da 'yan mata da samari, gabadaya sun shagala da jin kiɗan wata waƙar turanci wadda in ba shigowa palon ka yi ba ba za ka taɓa cewa an kunna music ba, kallon su take cike da tsoro tana ƙara ƙanƙame jikinta..

Wani matashi ne fari yake nufo inda take tsaye, sanye yake da T-shirt da wandonta iya gwiwa black color, fuskar nan a daure amma duk da haka in ka kalle shi za ka gane ba lefi yana da kyau daidai misali, gefen wuyansa zanen tatu ne an rubuta *Big boy*, haka ma hannuwansa duk an yi rubutu da zanen tatu ɗin, abin ka da farar fata sai zanen ya fito raɗau a jikinsa. Tafiya yake cike da kasaita har ya iso gaban Abir ba ta sani ba tana can ta lula duniyar tunani, yatsunsa biyu ya ɓala mata a kusan fuska ta yi saurin kallon shi, ja da baya ta yi tana nuna shi da hannu baki na rawa ta ce "K.. Kaine?" Saboda ta gane fuskarsa tana ganin shi a Tiktok.

Wani ƙayataccan murmushi ya yi bai ce da ita komai ba, sai da ya ga za ta sake masa magana ya nuna mata hanya. Nunawa ta yi ba ta ma san me yake nufi ba, tsare ta ya yi da ido yana kada kai, da wata ce ta masa haka babu abin da zai hana ya kifa mata mari, amma saboda da yadda yake matuƙar so da kaunar ta ya sa bai ji komai ba sai ma birge shi da ta yi.

"Idan ba ki tafi da ƙafarki ba ni zan dauke ki na kaiki."

Da sauri ta kalle shi ta ga da gaske É—aukan na ta zai ganin yadda yake janye hannun rigarsa, da sauri ta bi hanyar da ya nuna mata, 'yan matan wajan suka bi ta da kallo cike da mamakin Big boy ganin ta masa gardama bai mata hukunci ba.

Wani É—aki ya nuna mata yana É—aure fuska, jiki na rawa ta shiga ta tsaye a tsakiyar É—akin cike da tsoro take kallon É—akin.
Chapter 89 · 0% Book details