← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 120

Sashe 43

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban ta ta dawo ta kalli Zaiyan ta ce "Ki daina gaggawa Hauwa'u Maijidda zan sanar da ke komai, har ma abin da ya shige miki duhu duk zan sanar da ke game da wannan bawan Allah." Ta nuna Zaiyan ta ci gaba "Tabbas na san zuciyarki tana raya miki abubuwa da dama a kaina, za ki É—auka ko dan na cutar da ku nake tare da ku, ni kuma ina tare da ku ne dan na taimaka muku."

"Ta yaya za ki taimaka mana bayan ban san ke wace ce ba? Kuma kin ga wannan ba shi da lafiya yana cikin halin taɓin hankali don Allah kar ki cutar min da shi."

Murmushi ta yi ta harɗe hannunta a kan ƙirji ta ce "Maijidda, ina da tarin maganganun da zan sanar da ke, amma hakan ba zai yiyuba kasancewar ba ni da lokaci zan bari sai wani lokacin na sanar da ke komai, amma zan dinga bibiyar rayuwarki dan na taimaka miki ke da shi. Idan Yayan ki ya zo ki ce masa ya sa a sallame ku ku tafi gida maganin Asibiti ba zai taɓa warkar da shi ba, ku koma gida ba yanzu zai samu lafiya ba sai nan da wani lokacin hakan kuma ba zai yiyuba har sai kuna tare a waje ɗaya, idan har kika bar shi kika tafi wani wajan da zama to tabbas samun lafiyarsa ba lalle ya samu ba ballantana ki san shi ɗin ɗan waye? Daga ina ya fito? A wani gari yake? Ki yi nazari Hauwa'u Maijidda. " Tana gama faɗin haka ta ɓace ɓat a wajan sai ga wutar ɗakin ta kawo..

Dafe ƙirji ta yi tana juya maganar a cikin zuciyarlrta, gwauron numfashi ta sauke tana ɓata fuskar kamar za ta saki kuka ta ce "Babu wanda yake ba wa wani lafiya in ba Allah ba, idan har da sharri kike bibiyar rayuwarmu Allah ya yi mana tsakani da ke, in sha Allahu kuma zai warke ras ya yi rayuwa irin na kowa na kaishi gun ahalinsa ni da Yayana da yarda Allah." Ta ƙarashe maganar tana hura hanci, gabaɗaya ma ji ta yi matar nan ta ba ta haushi, ta zauna shi kuma ya matso kusa da ita ya ɗaura kan shi a kan kafaɗarta, ganin haka ya sa ta ɗago shi tana shagwaɓewa ta ce "Kai indai ina kusa da kai ba ka da wajan zama sai jikina kamar wata mamanka?" Ta ƙarashe maganar tana cuno baki.

Hannu ya kai ya taɓo bakin nata ya yi dariya ya ce "Mamata ce ke Anty?"

Dariya ta saki ba shiri, bayan Antyn da yake ce mata yau kuma ta koma Mama? Taɓe baki ta yi ta ce "Tab ƙato da kai zan haife ka? Ni ai Anty nake ba mama ba ka ji ko!" Ta faɗa tana zaro masa idanu irin ga Uwarsa tana masa kashedi..

Gira ya ɗage mata ya ce "Tab ƙato da kai zan haife ka? Ni ai Anty nake ba mama ba ka ji ko!"

Dafe kai ta yi jin ya maimaita abin da ta faɗa ta kafe shi da idanu tare da yin tagumi, shi ma kamar yadda take kallon shi ta yi tagumi haka ya yi, sauke hannun ta yi tana ɓata rai ta ce "Idan na yi magana kar ka sake kwaikwayo na, idan ka sake zan dai kula ka."

Kamar jira yake ta dasa aya ya maimaita yana wasa da zoben hannunsa fara sol wadda aka rubuta sunan *Abir* a jiki, da mamaki ta kalli hannun nasa ganin wata zoben bayan wadda ta sa masa mai sunan ta, ita wannan ruwan gold ce sai sheƙi take yi, kamo hannun ta yi tana duba zoben ta ce "Zaiyan waye ya saka maka wannan zoben?"

Kallon hannunsa ya yi yana ɓata fuska ya ce "Zaiyan waye ya saka maka wannan zoben."

Dafe kai ta yi tana rufe idanu, gabaɗaya ita ba ta so in ta yi magana a kwaiwaye ta sai ga shi shi kuma Zaiyan da Allah ya jarabce shi da hakan sai ya kwaikwaye ta, ta ɗago za ta masa magana ta ji an turo ƙofar ta juyo ta ga su Suhal ne..

Kallon shi Suhal ya yi ganin yadda yake shige wa Abir sai abin ya tsaya masa a wuya, tunawa da shi ɗin ba mai hankali ba ne sai ya sauke ajiyar zuciya ya ƙaraso kusa da su ya tsaya yana kallon Zaiyan, so yake ya ɗago fuskar shi su haɗa idanu hakan ya sa ya yi gyaran murya ya soma magana.

"My Princess an jima zan koma Niger tare da Sajida."

Da sauri ta kalle shi sai yanzu ta tuna da kalmar da ya faɗa na matarsa ce Sajida, wani iri ta ji ta kalle shi cike da kunyar maganar da za ta fito daga bakinta, ƙasa ta yi da kai ta ce "Sorry to say Ya Suhal."

"OK tell me." Ya faÉ—a yana kafe ta da na mujiya.

"Ya Suhal na ji ka ce wannan baiwar Allah matarka ce."

GyaÉ—a mata kai ya yi duk da ba kallon shi take ba, sai ta ci gaba.

"Kenan in kuka tafi ka janye maganar auren nawa?".Wani irin ƙayataccan murmushi ya yi ya shafa sajansa, kenan Princess ɗin tasa tana son shi take ɓoye masa? Wani irin daɗi ya ji ya gyara tsayuwar shi cikin nutsuwa kamar ba shi ba ne yanzu ya ruɗe da ganin Sajida ya ce "Princess kenan, to dan kawai na ga matata sai na janye maganar auren ki? Ai ni da ke miji da mata ne in sha Allah zan kuma tabbatar miki da hakan idan na koma Niger nan da sati ɗaya Maimartaba zai turo a nema min auren ki, kuma bana son a sa lokaci mai tsayi. Sannan maganar Sajida ki aje a gefe Allah ya ba ni damar auren mata ɗai-ɗai har guda huɗu, kin ga kuwa dan ina da Sajida ba zan ƙi auren ki ba my Princess ɗina.." Ya ƙarashe maganar yana murmushi, ya ji daɗi da ta nuna masa hakan ko ba komai yanzu zai daina kokwanto akan soyayyar shi da ita..

Ajiyar zuciya ta sauke, ita fa ba wai dan kishi ta masa hakan ba, so take ta san taya suka haÉ—u har aka musu aure? sannan kuma taya aka neme ta aka rasa tsayin shekaru 5 cif? Kallon shi ta yi ta ce "Ina son naji shin taya aka sace Sajida?"

Murmushi ya yi ya ce "Zan faɗa miki yanzu dai an sa mata ruwa da allurori ya ma kusa ƙarewa, minti kaɗan za a sallame mu sai mu zauna mu ji komai daga bakin ta ni ma na faɗa miki yadda muka yi soyayyar mu da ita."

Ɓata fuska ta yi ta harare shi ya yi dariya, Zaiyan ya kalli Suhal bai ce komai ba yana zaune a gefen ta kamar ba ya ɗakin, sai da Suhal ya ce "Zaiyan ya kake?"

Saurin ɗagowa ya yi ya kalle shi ya maimaita abin da ya faɗa masa yana dariya. Idanu ya zuba masa ganin yadda komai nasa irin nashi ne, ji ya yi kamar an zare masa kuzari ya ja ƙafar shi ya isa gare su ya kamo hannun shi ya sauko da shi daga kan gadon, tsayar da shi ya yi a gefen shi ya kalli Abir wadda ita ma su take kallo ya ce "Ya kika gani Princess?" Yatsarta manuniya da ta gefe ta haɗe ta miƙe uku tare da yin murmushi ta ce "Kamar 'yan biyu ma sha Allah."

Ganin yadda ta yi sai Zaiyan shi ma ya yi yana dariya maimaita abin da ta faɗa, sai kuma ya matsa daga jikin Suhal yana nuna shi da hannu ya matso kusa da Abir ya ce "Anty kin ga wannan babban yana taɓa min hannu." Ya faɗa yana daddaga hannunsa akan goshin Suhal ya dawo inda take ya tsaya tare da saka yatsu biyu a baki ya ci gaba da kallon Abir..

Ƴar dariya Suhal ya yi ya ce "Allah ƙadiran wa muridan! Wai har shan yatsu yake kamar wani ɗan goye?" Dariya ta yi ta ce "Wallahi fa wani lokacin yana yin haka idan wani ya taɓa shi."

GyaÉ—a kai Suhal ya yi ya ce mata zai koma ya dauko Sajida sai su tafi ta amsa da to ya fita...

Ba su jima sosai ba sai ga su sun shigo Sajida na haƙaƙarin Suhal yana jera mata sannu, ganin haka ya sa Abir ta wurga masa harara ta ce "To kawo ta nan sarkin marassa kunya."

Sosa kai ya yi ya janye jikinshi daga nata Abir ta tallafo ta ta kai ta bakin gadon ta zaunar, kallon Abdul ta yi da ya gama waya akan shigar da kes É—in Sajida ya kalle ta, haÉ—e rai ta yi ta ce "Yaya ka sa a sallami Zaiyan mu tafi gidan su Inna.".

Da mamaki ya kalle ta ya ce "Baby me ya kawo kuma maganar a sallame shi bayan bai gama shan magani ba?" Ƙara murtuke fuska ta yi irin ba wasa ɗin nan ta ce "Ni dai na faɗa ma ba na son zaman shi a Asibitin nan kwata-kwata mu koma gida."

"To idan naƙi fa?"

"Ba ma za ka ƙin ba ai, ka ce a ba shi sallama ko kawai mu tafi ba sai an ba shi sallamar ba, ni fa gabaɗaya ma Asibitin nan bana ƙaunar ta ko kaɗan mu tafi gidan su Baba. In kuma ba za ka iya faɗa wa Doctor ɗin ba ni sai na je na masa bayani da kaina."

Sake da baki suke kallon ta, ganin ta ci gaba da faɗa ya sa Abdul cewa su tafi kawai, hannun Sajida ta riƙe shi kuma Suhal ya kama Zaiyan da nufi ya riƙe shi ya ce sam ba zai yarda wani ya riƙe shi ba bayan Antynsa, dole ta haƙura da riƙe Sajida ta kama hannunsa Suhal tuni dama ya yo gaba ya bar su, Abdul ya ce shi su isa motar ita kuma ta zo su suje ya sanar da likita ya ba su takardar sallama..
Chapter 43 · 0% Book details